New Post

Sunday, 16 October 2016

ABDUL WAHAB 30

ABDUL WAHAB 30

©Rabiatu sk msh
          ®NWA

Hakan zaman sadeey da Abdul yaci gaba da kasancewa, ko kad'an bata sakar mishi fuska idan yazo inda take, anma ta fara da yi mishi girki da duk abnda tasan zai bu'kata, anma da taa jishi zata shige d'akinta, shima yaa daina neman takura mata anma dai yana 'ko'kori wurin kyautata mata da son nuna mata shi masoyinta ne na ha'ki'ka.

Yau watanta biyu kenan babu abnda ya canja tsakaninta da Abdul, tana zaune falon d'akinta ya shigo,bata sanma ya shigo ba tana can duniyar tunani, a fili ta furta, Hmm NAMIJI KENAN (littafin ummieluff) da sauri yace "me namiji ya miki kuma? 'dago da fuskarta tayi cikin mamaki batasanma maganar zuci taa fito fili ba.

Kamar bazatace komi ba, sannan tace "mefa namiji yake? Babu abnda yayi, ba ruwanshi da yaudara, satar farin ciki, da kuma 'kwatar soyayya da fin 'karfi.

Yace "duk namijin keda wannan? Shruta mishi ba tace komi ba, zama yayi bakin gadon ta mi'ke da sauri, tace "wlhy bazaka zaunamin a d'aki ba, Yace "haba sadeey, kina tunanin zamanmu zaiyi a haka kuwa? Ina mijinki anma bazamu zauna wuri d'aya ba?

Tsugunnawa tayi ta fashe mishi da kuka, "tohh ni wlhy sai dai ka sauwa'kemun, bazan iya zaunawa dakai ba, kana shiga ha'kkina da yawa, don Allah ka rabu dani ka aura wadda kakeso yayanmu.

Kallon mamaki ya tsaya yi mata, kasa jurar jin kukanta yayi mai tsuma zuciya, duk ya rikice, yake cewa "waya fad'a miki ina da wadda nakeso bayanke? Wlhy ke kad'ai nakeso sadeey, ban ta'bason wata d'iya mace ba kamr yanda nake sonki, ki bani dama in bayyana miki irin son da nake miki.

Da 'karfi tace "baka so na yayanmu, saboda rashin khadija ne kawai yasa ka aureni, ay naji labarin zatayi aure shine ka 'bulloma su hajia da wannan salon yaudarar, ko sonka zai kasheni bazan iya zama dakai ba, 'kara in auri wanda yakeso na, ni bazanyi zaman 'kunci a gidan aurena ba.

Yace "wlhy banda burin 'bata miki rai qanwata, don Allah ki fahimceni, wlhy ina sonki, naayi miki alqawarin faranta miki har iyakar rayuwatah.

Hannu biyu ta sanya ta rufe kunnenta tace "bani sonji yayanmu, don Allah ka 'kyale zuciyatah ta huta hakanan, duk abinda zakamin don kasan ina sonka ne.....kifa kanta tayi taci gaba da shesshe'kar kuka.

Sosae yake jin kukanta a jikinshi, ya rasa yanda zai rarrasheta, hannu ya saka ya d'agota a jikinshi, da sauri ta fara 'ko'korin zamewa, anma tsam ya rumgumeta a 'kirjinshi sosae, har saida tayi 'kara saboda ba ri'kon wasa ya mata ba, maida numfashi ya farayi a hankali, ko motsi taa kasayi.

Bata da wani 'karfin daya wuce kuka, shikam idonshi rufe ko rarrashinta ya kasayi, duk jikinta ya saki ta fara rage kukan, sun dad'e a haka, kafin ya sassauta mata ri'kon ta zame ta kwanta a hankali ta rufe idonta, shima mi'kewa yayi ya fita ya barta da wani haushin nashi fal cikin ranta.

Dedicated to Mr. Smiles😃

❤❤Rabiatu sk msh❤❤

Related Posts:

  • MATATAH CE 75♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              75 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More
  • MATATAH CE 72♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡             72 ©Rabiatu sk msh       ®NWA   … Read More
  • MATATAH CE 73♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              73 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More
  • MATATAH CE 73♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              73 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More
  • MATATAH CE 74♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              74 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts