ABDUL WAHAB 13
©Rabiatu sk msh
®NWA
Daga fatima har Abdul babu wanda ya iya magana, duk jikinsu yayi sanyi da kalaman sadeey, maganar da hajiya ta mishi ce ta fad'o mishi a rai d'azu bayan dawowarsu daga gidansu khadija.
Tace mishi "Kadai'ki maganar aure ko Abdul, tun ina maka magana harna fara gajiya, ga qanwarka nan fatima tana shirin tafiya d'akinta anma kai ko maganar bakayi, kai dai ba yaro bane, Yace "hajia nipa ba na'ki aure bane, kawai inason in samu macen da zata soni ne, kuma wacce ta kwantamin a rai, kuma insha Allah na kusan samu kumah zakiyi mamakin za'bin dazan kawo miki.
Tace "hmm, anma sanin kanka ne sadeey na matu'kar 'kaunarka ko? Taa'ki yarda da soyayyar kowa sai dai kai, ba nace dole zanyi muku auren had'i ba, A'ah da tunda ran mahaifinku zanyi maka,! Anma kayi tunani akan soyayyar da take maka, idanma baka amince ba ni bazan takura ba.
Jikinshi a sanyaye har suka gama magana da hajia, saukar da ajiyar zuciya yayi yana kallon sadeey tana murmushi tace "da wannan kallon ay saika sanya tunaninka ya hanani barci yayanmu, duk da kullum na rufe idona kyakkyawar surarka nake gani, ina sonka da yawa yayanmu.
Kallonshi fatima tayi ya saukar da kanshi 'kasa, duk farin cikin da yake ciki ya nemeshi ya rasa, mi'kewa kawai yayi yana 'ko'korin yin murmushi yace "saida safenku 'kanwata, sadeey tace "saida safe yayanmu, kayi barci mai dadi.
Fatima tace "Allah ya kaimu," yana tafiya sadeey ta dawo kujerar da fatima take ta zauna tana murmushi tace "yadai? Naaga duk yanayinki yaa canja, kodan hajia taa fad'a miki iyayen kabir sunzo akan maganar aurenki? Karki damu naasan sha'kuwar da kukayi da yayanmu, ko bayan aurenki nizan kula miki dashi.
Tace "kekam dai daga maganar aure sai damuwa, ko biki ba'a saka ba? Sadeey tace "shine nima na gani, kinga kizo mu tafi mu kwanta mun 'karasa maganar a can.
Dedicated to Mr. Smiles😃
❤❤Rabiatu sk msh❤❤
0 comments:
Post a Comment