```MAKASHINKA...```
59-60
©Rabiatu sk msh
Tana shiga ta tada mota ta tafi, shamsuddeen ya duƙar da kanshi yana hawaye, shin wai meke faruwa dashi ne?meyasa soyayyar sadeey tazo mishi ta ƙaddara kala-kala? Meya faru da momie har ta kwanta asibiti? Shi dai a iyakar tunaninshi baiyi mata komi ba.
Yana ɗago kanshi sai dai yaga ƴan sanda zagaye dashi kowanne riƙe da bindiga, ga wani tashin hankalin fa sabo, ya yunƙura zai gudu suka ƙara zagayeshi, ya duba gabas da yamma babu hanyar guduwa.
Ya fara laluben abin ɓacewarshi, cikin tsawa sukace ya sake ya motsa halbeshi zasuyi, yana gani babu mafita suka tafi police station dashi.
Sadeey tana hawan titi ta fara sharara gudu, batasanma ta bama zuciyarta damar da zata tsayayin wani tunani, komi yaa gama rikice mata.
Tana isa gida masu aiki sun gama haɗa break fast ɗin, ta shiga ta tsinto musu kayan da zasuna canjawa ita da momie, ta ɗauka break din ta koma asibiti.
Har lokacin momie kwance take bata motsa ba kamar yanda ta barta, duk da tsanar momie da takeji tana matuƙar tausaya mata, ta nemi wuri ta zauna kawai sannan ta samu damar fara kuka, tama manta rabon data zauna taci wani abincin kirki.
Sai bayan magrib Abba ya dawo, cikin fara'a daga ganin yanayinshi yana cikin farin ciki, ya zauna bakin gado ta gaisheshi kawai ba wanda ya ƙara cewa komi, sai dai kallon zargin da take mishi.
Waya aka kirashi ya miƙe har zai fita kuma ya dawo ya zauna, ya ansa wayar Yace "wace irin maganace wannan? Na faɗa maka komai kuke ku gaggauta kaishi kotu gobe a yanke mishi hukuncin daya dace dashi, kar abin ya ɗauki lokaci"
Yayi shiru yana sauraren ɗayan ɓangaren, Yace "lawyer ba matsala bane, kudai kawai kuyi abinda nace zanyi magana da lawyern, Yauwah tohh ngde"
Tunda ya fara magana sadeey ta gagara zama, ta miƙe tsaye tana kallonshi kamar jira take ya gama wayan tace "Abbah waye za'a kai kotu?" yace "Akwai wani banda shamsuddeen?" ɗaura hannunta tayi saman kai kamar wadda aka jefa ta koma ta zauna "Na shiga uku" Abba yace "meye na shiga uku kuma? Kamata yayi kiyi farin ciki Allah ya bamu ikon kamashi, wanda ya kashe miki iyayene fa"
Tace "Abba bashi bane, wlhy ba shi bane don Allah kar a hukuntashi akan laifin da bai aikata ba" Abba ya ɗanyi murmushi "idan ke kince bashi bane, ay dunia taa gama sanin shine ya aikata sadeey," kuka ne ya ƙwace mata.
Ya duƙo dai dai fuskarta "kiyi a hankali karki tada marar lafia, ko laifin ƙoƙarin kasheta ay yaa isheshi zaman prison" hannu ta saka ta toshe bakinta tana ci gaba da rairo kukanta.
Bazan iya kwatanta halin da sadeey ta shiga ba a daren ranar, sai dai ta miƙa duk lamurranta ga ubangiji, kwana tayi tana roƙon Allah ya sauƙaƙa mata lamurranta, ya fidda shamsuddeen daga halin daya shiga, laifinshi kawai da take gani yanzu idan taa tuna takejin haushinshi shine ƙoƙarin kashe momie, kuma shine babban matsalan da yake fuskanta yanzu.
Sadaukarwa Ga Sadeey S Adam
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment