New Post

Sunday, 16 October 2016

ABDUL WAHAB 9

ABDUL WAHAB 9

©Rabiatu sk msh
          ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

Tun daga ranar kullum Abdul neman hanyar da zai 'kara ganin khadija yake, gashi cikin rashin sa'a Yaa mnta bai amshi numberta ba, dafe kanshi yayi yaa rasa yanayin da yakeji, shidai a nashi tunanin ba sonta yakeyi ba, anma tana matuqar burgeshi, yanayinta na rashin hayaniya, murmushinta, gata da nutsuwa da dad'ad'an lafazi.

Murmushi yayi cikin jin dadi, baiyi zato ba sai dai yaji wata irin 'kara a kunnanshi, da sauri ya fara waiwaye, sadeey ce ya gani tsaye tana 'kyal'kyala dariya, dafe kanshi yayi lallai yarinyarnan.

Murmushi tayi ta zauna saman hannun kujerar da yake, tace "yayana miye zaka zauna kayita tunaninah? Kawai ka 'kwalamin kira sadeey, da sauri zan taho in tayaka fira, d'aga mata kai kawai yayi, tace "mama taace in rage yi maka yawan surutu, naa daina ko? 'daka mata kai ya 'karayi, tace "kuma taace in dinga baka amsa dakai koda hannu kawai ay dai bani zaqewa ko? Murmushi yayi har saida kyawawan haqoranshi suka fito, ya d'aga mata kai.

Fatyma ce ta fito cikin fara'a tace "yayi masoyan asali, firar me ake? Sadeey tace "Soyayyah mana, ke ya kika gani? Fatima tace "hakan, sai a tsaida hakanan hajiya tace in kiraki.

Da sauri ta mi'ke tsaye tace "anma ki tsaya ki taya yayana firaa! Falon hajia ta tafi saida ta shige sannan Abdul ya kalli fatima yace "Qanwatah ya akai naga 'kawayenku basu kawo muku ziyara? Tace "kamarya yayanmu? Duk wannan 'kawayen namu dake yawan zarya? Kuma ayni ba wasu qawaye ne dani ba wannan sai sadeey kowah nata ne!

Yace "tohm ita khadija 'kawar waye a cikinku naaga bata ta'ba zuwa ba, fatyma daria tayi tace "kacemun dai khadija kake nema, ni ba 'kawatah bace kawai dai munyi class d'ayane a sec, shiyasa ma kaga bamu zumunci sosae!

Yace "aikam dai yaa kamata ku dinga zumunci, ki shirya anjima in kaiki! Tace "kai dai kawai kace zan raka ne, banmapa san gidansu ba, anma zanyima shafa'atu waya ta turamun address dinta.

Yace "yauwah er qanwatah anma pa karki fad'ama sadeey, miqewa tayi tana dariya tace "aikam yanzu zan fad'a mata ta tafi d'akin hajiya da gudu yana kiranta bata tsaya ba.

Dedicated to Mr. Smiles😃

❤❤Rabiatu sk msh❤❤

Related Posts:

  • MARYAM KO MARYAMA 61-80[14:07, 3/12/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣soyayyar whatsapp❣ @OHW 61-70 Maryama ce kwance tana chat da abn qaunarta wani irin farin ciki takeji dk sanda suke tare, murmushi tayi tace Ma… Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 81-100[14:07, 3/14/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣soyayyar whatsapp❣ @OHW📚 81-90 A rude Maryam ta duqa tana tattara wayar, Maryama tayi tsaye kamar ana hura mata wuta a qirji don sosae … Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 41-60Rabiatu sk novels [11:59, 3/11/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣soyayyar whatsapp❣ @OHW 41-50 Washe gari yaa kama ranar monday, suka shrya maryam da maryama suka fito zasu tafi school, Mary… Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 100-110[14:17, 3/15/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣soyayyar whatsapp❣ @OHW 100-105 Ta miqa hannu zata yaye labulen falon kenan wayarta tayi qara har sai data tsorata, ta duba taga sunan Aboki A … Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 21-40[10:39, 3/10/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣Soyayyar whatsapp❣ @OHW 21-30 Tana bude datar messages da yawa suka shgo mata, anma naashi ta fara dubawa, da wayarta glaxy s5 wadda Abokinta A… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts