```MAKASHINKA...```
9-10
©Rabiatu sk msh
Tananan zaune har 10pm, saiga momie ta fito, har zata wuce ɗakin Abba ta hangota ta taho inda take tana mata kallon mamaki
Momie tace "Yau kuma da wuri kika tashi sadeey? Tace "Wlhy kuwa momie, duk na damu da abinda ya faru jiyane, don Allah kuyi haƙuri momie," tace "ba komi sadeey, ni bakimin laifi ba, kawai dai da alama yayanki ne baiji daɗi ba, shima bai fushi dake ki kwantar da hankalinki.
Tace "tohm momie ngde sosae," ta shafa kanta tace "ba komi sadeey, mu tamkar iyayene a wurinki, sai dai kawai kiyi ƙoƙarin kiyayewa duk inda ya gayyaceki kije, yayanki dai ne jini ɗaya bazaiyi abinda zai cutar dake ba," tace "insha Allah momie jiyanma bawai naƙi zuwa bane,"
Anwar ya fito da shirin fita, ko kallonsu baiyi ba zai wuce momie ta mishi magana ya dawo, yana ciccijewa ganin wani irin kallo da momie ta mishi ya basar ba don yaso ba yace "lovly ƙanwa an tashi lafia? Ganin ya saki fuskarshi itama cikin fara'a tace "lafia lau yayanmu yajin haushina? Yace "wane ni inji haushin ƙanwata? Kawai dai anyi shagali babu ke, daria tayi ganin yaa maida abun wasa.
Momie ta tafi ta barsu sadeey tace "ina zakaje haka yayanmu? Yace "wani wuri yanzu zan dawo, tace "tohm nima muje ka ajiyeni wani wuri, suka fito suka jera a tare har inda motarshi take.
Suna cikin tafiya yace "wai ina zakijene ƙanwata? Tace "kai dai duk inda kaga dama ka ajiyeni, wani wuri zanje" yace "aikam ƙarama ki faɗamin" ganin ya takura mata tace "police station zaka kaini"
Wurin kallonta ya kusa sauka daga hanya da sauri ya sai saita yace "kodai kunnena ne baiji dakyau ba? Tace "wlhy police station zanje" yace "me zakiyo? Tace "idan kanaso kaji ka biyoni mu shiga kaji" sunata gardama bata faɗa mishi ba har suka shiga.
Har ƙofar police station ya kaita ya ajiye ya tsaya yana kallonta koda gaske shigar zatayi, tayi murmushi tace "ngde" sannan ta buɗe motar ta fita yana ta kallonta harta shige.
Wurin da ake rubuta ƙorafi ta nufa, ta gaishesu cikin girmamawa sannan tace "na kawo ƙara ne" ya jawo biro zai fara rubuta statement"
"ƙararwa kika kawo? Ya sunanshi wnda kika kawo ƙararshi? Saida ta ɗanyi tunani sannan tace "sunanshi ~masoyi~" wani irin kallo yayi mata yace "cikakken sunanshi zaki faɗa mana" ta marairaice fuska tace "nidai bansan sunanshi ba, da haka na sanshi"
"wane dalili ya sanyakike kawo ƙararsa? Tace "yana takura ma rayuwatah ne, kullum yana turomin saƙonni a wayata komai nake yana tare dani, ko nawa ne zan iya biya aymin tsakani dashi,"
Yace "tohm keda bakisan sunanshi ba a ina zamu ganshi muyi miki tsakani dashi? Tace "nima fa ban sani, anma nasan yanzu haka yananan wurin" bai kulata ba yace "kawo muga saƙonnin da yake turo miki" ta ciro wayarta da sauri ta miƙa mishi,"
Yana kallon wayar ya watsa mata kallon ta raina mishi wayau yace "ina saƙonnin da kike cewa anyo miki? Ta amsa wayar tana dubawa da sauri tace "sunanan rututu, bari ka gani" cikin mamaki take kallon akwatin ajiye saƙon dake cikin wayar wayam babu komi ciki, kuma ita dai iyakar saninta bata goge ko ɗaya ba, tana cikin kallon waya saƙo ya ƙara shigowa.
```karda ki wahalar da kanki wurin tunani, bai kamata kiman lakani da mai takura miki ba, don banma fara nuna miki kulawa da soyayya ba, kuma zanci gaba da kasancewa tare dake har saikin gane ni masoyinki ne, ban cancanci ki kaini ƙara wurin hukuma ba sadeey```
~masoyi~
Da sauri take nuna mishi wayar da yayi tsaye yana kallonta tana karantawa tana haɗa zufa tace "ka ganshi ko? Ka wani saƙonnan ma ya turo min? Ya kalleta sheƙeƙe yana kallon wayar yace "ni har yanzu banga wani saƙo ba" ta ƙara dubawa shima yaa goge.
Ta kwantar da kanta tace "wlhy gaskia nake faɗa muku, don Allah ku taimakamin ni tsoro yake bani, yanzu haka ma cewa yake zaici gaba da kasancewa dani" ganin yanda take ta roƙonshi yace "naji, faɗa mana ya kamanninsa yake? Tace "ni ban taɓa ganinshi ba bansan kamanninshi ba? Yace "kuma ko yaushe yana tare dake ba? Ta ɗaga mishi kai da sauri.
Sanyawa yayi aka fitar da ita tana ta roƙonsu tana faɗa musu itafa da gaske take, anma kallon mahaukaciya ma suke mata, a dai dai ƙofar police station ɗin suka barta, Anwar nanan har lokacin yana jiranta, ta duba mutane duk sun tsura mata ido.
Ta ɗaga murya tace "inanan dawowa da hujja, saina nuna muku kamanninshi, wannan Alƙawari ne, saina tabbatar muku da ina cikin hankali na, taja tsoki ganin ita kaɗai ke surutanta, ta buɗe motar ta shiga, Anwar naa kallonta sai daria yake mata.
Sadaukarwa ga Sadeey S Adam (kishiya)
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment