```MAKASHINKA...```
65-66
©Rabiatu sk msh
ƘARSHE
Sadeey Sai zagaye ɗakin take cikin fargaba, a zuciyarta kuma addu'ar samun nasara kawai take, kasa haƙura tayi ta ɗauko wayarta ta kunna zata kira Anwar.
Batasan sanda ta kunno recording ɗin da tayi b, sai dai ta jiyo muryar Abba da momie suna magana a tsakaninsu.
"lallai hajia kin iya acting fa sosae, babu wanda zai ganki yace lafiyarki ƙalau" tace "ba dole ba Alhaji, ina zamu bari zargin yarinyarnan yayi ƙarfi a kanmu, kasan dai bazata haƙura ba haɗa kai zasuyi da shegen yaronnan a kaimu kotu a kashemu, ko kuma su ɗauki fansa da kansu"
Yace "Sosae ma, shiyasa kikaga naa dage akan sai an hukunta yaronnan da laifin kashe iyayen sadeey, don idan har yana raye zai iya tona mana asiri ya faɗi gaskiyar mune muka kashesu" tace "ay itama sadeeyn ba ƙyaleta zamuyi ba don zata iya zamar mana matsala"
Yace "hakane itama inanan ina tunanin Yanda zanyi da ita mu gama da wannan ɗin dai" jikin Sadeey ne ya kama kyarma, ta kusan sakin wayar a ƙasa, bata koma ɗakin da momie take ba ta juya kawai cikin hanzari ta tare mai napep ya kaita kotun.
Kotu taayi shiru kawai ana sauraren Alƙali ya yanke hukunci kawai sai gata ta shigo da gudu kamar wacce aka jefo duk kallo ya koma kanta, Tace "ina da magana"
Alƙali Yace "ke kuma wacece da zaki shigo ana cikin shari'a?" Tace "mai girma mai shari'ah nice sadeeyn da aka kashe ma iyaye, kuma naazo nan in bada shaidar da zata tabbatar ma da kotu cewa ba shamsuddeen bane ya kashemin iyaye ba"
Br ishaq Ya miƙe tsaye yace "Mai shari'ah bai kamata ace sai bayan an gama ƙara bane zasu kawo hujjojinsu na ƙarya"
Lawyern dake kare shamsuddeen Yace "A gani nah Ya mai shari'ah, bai kamata mu yanke ma shamsuddeen hukunci a bisa laifin da bai aikata ba, ka daure ka saurari wannan hujjar tunda ba'a riga da an yanke hukunci ba" Alƙali ya amince da zawabinshi, Sadeey ta miƙa ma lawyern Shamsuddeen wayar ya bada aka miƙama Alƙali.
Tun kafin a gama sauraren recordn ɗin Abba ya fara hawayen nadama, cikin sauƙi ya yarda da laifinshi yana kuka yana roƙon yafiyar Sadeey, Momie ma akaje har asibiti aka taho da ita tayi wuri wuri.
Hukuncin ɗaurin rai da rai aka yankema momie, Abba kuma kisa ta hanyar rataya, su duka kuka suke sunyi nadamar da bata da amfani, kuma Abba ya maido mata duk dukiyarta dake hannunshi.
Zuwa tayi ta rungume Shamsuddeen cikin farin ciki, su duka hawayen murna suke.
Muryar kaka zainabu suka jiyo tana cewa "lokaci na gaba dai ku kula kar kuyi a gabanmu, kaaji yaran zamani" su duka suka ƙyalƙyale da daria, sadeey ta rufe idanunta saboda kunya.
Shamsuddeen Yace "kin cika masoyiyah ta haƙiƙa sadeey bansan da bakin da zan miki godia ba..." tace "don haka kayi shiru kawai ba saika godemin ba"
Ya Anwar ya ƙaraso inda suke shima yana murmushi duk da bai ɓoye damuwar da yake ciki ba Yace "Yanzu kuma buri guda ne ya ragemin a matsayinah na babban yaya" sadeey tace "wanne kenan?" Yace "inga auren ƙanwata da wanda takeso mana"
Murmushi tayi ta rufe fuskarta.
***
Ba daɗewa akayi auren Shamsuddeen da Sadeey, Yaya Anwar dasu kaka ne suka shige musu gaba, ta miƙa mishi gaba ɗaya dukiyarta, suna zamansu lafiya da ƙaunar juna.
Sadeey (Kishiya) da Shamsuddeen(soulmate ɗinmu) Allah ya bada zaman lafiya.
Alhamdulillah
Godia ta tabbata ga Allah, ubangijina, mai kowah da komai daya bani ikon Kammala wannan littafi, tsira da Amincin Allah su ƙara tabbata Ga Annabinmu muhammad (S.A.W).
Iyayenah Abin Alfahrina.
Addu'ahta kullum tana tare da kai Abbana, Allah yakai haske a kabarinka, ya gafarta maka dukkan zunubanka, Ya saka maka da Aljannah firdausi.
Momie banda bakin da zan miki godia kin gamamin komai A rayuwah, Allah ya saka miki da Alkhairi ya ƙara miki Yawancin kwana.
Sadauwarwa
Wannan littafin sadaukarwa ne gareki Sadeey S Adam (splexy) Ina miki fatan Alkhairi a koda yaushe, haƙiƙa ke ƙawace ta haƙiƙa, Allah ya ƙara miki basira, ya tabbatar miki farin ciki a rayuwarki.
YABAWA
Na yaba da irin ƙwarin gwiwar da kake bani Abdul jega, MR SMILES, da taimakonka da shawarwarinka na kammala wannan littafi nawa, Allah ya ƙara basira.
Ban manta daku ba..
Muhd Abba gana
Saeed bebeji
Raheem jega😏
Abdul azeez.
Kuna raina.
My princess Amrah (ƴar uwah, kuma ƙawa ta ƙwarai)
Zahra bb tamu😘
Sistona beely badaru
Mr umar
Maman adnan
Pherty
Zahra bukar
Billy sarki
Ummu Abrar
Ummeeterh
Fulani cerdiya
Anush didi
Aneelurv
Ankerh
Kdeey
Asea bashir
Deejah Abdul
Shafa'atu
Basma er lele
Rash kardam
Sahaf
Safah
Stylish
Waliyyah
Da dukkan ONLINE HAUSA WRITER'S ina jinjina muku Allah ya ƙara basira
Jinjina ga ƙungiyar NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION, Allah ya ƙara ɗaukaka
Dole na ambaceku.
Aunty ma'u
Hasma
Aunty mermah
Aunty haneesa
Aunty bilky maman shaheed (sarki)😉
Ina miƙa godiyatah ga dukkan masoyana, makaranta littafinnan wanda na sani da wanda ban sani ba, Allah yabar ƙauna, idan da mai gyara ko comment akan wannan littafin
08032133670... Anma karkuce ban kawo muku rayuwar Shamsuddeen da sadeey ba, kishine ya hana😉 sai kunjini a sabon littafina
Shafcy
Mrs Zango
Maman munauwara na gaisheku kyauta👌🏻
Ga masu neman littafaina sai su shiga blog ɗina kamar haka
www.babymsh.blogspot.com
Ko a facebook: Rabiatu sk novels
Daga marubuciyar
Ƴar Autah
Princess Amrah
Miye sanadi?
Mai farin jini
Maryam ko maryama
Hafsatul kiram
Wasu mazan wasu matan
Mata biyu
Amanar aure
Abdul wahab
```Rabiatu sk msh```
0 comments:
Post a Comment