```MAKASHINKA...```
55-56
©Rabiatu sk msh
www.babymsh.blogspot.com
Kwana biyu duk taayi su ne da tunanin yanda zasu tona asirin Abbanta, duk zaman gidan a takure take saboda ko ganinsu bata ƙaunar yi, gashi momie sai ƙara shige mata ko yaushe tana tare da ita bata da wata hanyar da zatayi magana da Shamsuddeen.
Ranar da kwana biyun zai cika tana kwance kusa da momie, ta miƙe zaune kawai tana kallanta cike da jin haushinta sai shaƙar barcinta take, ta koma tunanin halin da shamsuddeen yake ciki kuma.
Miƙewa tayi ta nufi toilet ɗin ɗakin, tsayawa tayi gaban mirrow taja tsoki, "haka kawai an hana mutum ganawa da masoyinshi, Mugaye kawai" daga bayanta taji Yace "nima haushin da nakeji kenan, sai dai in hangeki daga nesa kin barni da kewarki" washe baki tayi cikin fara'arta ta juyo tana daria tace "Ya deen! Yaushe kazo cikin darennan? Sai kuma ta ɗaure fuska.
"har a toilet zaka biyoni?" Yace "tuba nake masoyiyatah, babu hanya dazan magana dake ne, kinsan ina buƙatar kulawa da soyayyarki" tace "naji wani lokacin saika kiyaye" yana dariyar tsokana yace "an gama ranki shi daɗe" su duka sukayi daria.
Yace "yanzu dai bamu da lokaci, ki faɗamin me kika gama yankewa?" tace "kaina ya ɗaure Yaa deen, na rasa gano mafita, duk tunani nah ya tsaya akan mu faɗama hukuma kawai"
Yace "kima daina wannan maganar, tunda dai kin kasa samo mana mafita" tace "tohh me zakayi kenan?" wani ɗan murmushi yayi yace "maiyi bai faɗa sadeey" tace "kada ka ɗauki doka a hannunka Ya deen" ƙofa ya nuna mata da ido, yana juyawa sai dai ta juyo taga bainan, kamar motsi ta jiyo a bakin ƙofar ta buɗe.
Momie ce tsaye da sauri taja da baya tana kame-kame, itama sadeey ta tsorata da ganinta a ƙofar toilet din tace "momie yaushe kika tashi? Tace "yanzu mana wani abu? Sadeey tace "A'ah" ta wuce ta sumi-sumi.
Momie ta tsaya tana jinjina kai, lallai zarginmu akan yarinyarnan ya zama gaskia, daman kallan tsanar da take mana dole yaronnan ya fayyace mata komi, dole musan matakin da zamu ɗauka da Alhaji.
Washe garin Ranar 5:00pm
Duk ranar momie ɗakin Abba ta yini, sadeey na ɗakinta tana tunanin Abinda shamsuddeen zaiyi zuciyarta cike da fargaba.
Dai dai lokacin momie ta fito daga ɗakin Abba ta ƙwalla ƙara, sai ihu take a rikice sadeey ta fito shima Abba har yazo inda take yana rirriƙeta, ta riƙe wuyanta sai burgima take idanunta sun firfito numfashinta na ɗaukewa, ta saka hannunta sai ƙoƙarin ƙwacewa take da alama dai wani ne ke shaƙe mata wuya, Abba dake ƙoƙarin taimaka mata shima sai jefar dashi ake yana dawowa.
Sadeey ta ruga wurinta tana rirriƙeta tace "momie, momie meke faruwa? Ta kasa magana sai kakari take ta fara janye hannunta tana kuka tace "Ya deen ka bari, don Allah ka daina," anma ko gezau sai magiya take.
Ganin haka ta ruga da gudu kitchen ta ɗauko wuƙa tace "ka daina ko in kashe kaina," yaƙi ya saketa tace "dgsk nake Ya deen" gani tayi numfashin momie ya fara ɗaukewa ba shiri ta yanki hannunta jini naa zuba, sannan ya saki momie ta faɗi.
Ta ƙarasa duk da yanda jini ke zuba a jikinta tana jijjiga momie, a ruɗe Abba ya kira Anwar suka sakata mota sai asibiti, suna zuwa aka wuce da ita emergency, sadeey kuma aka tafi yi mata dressing.
Abba duk yaa fita hayyacinshi sai zagaye zagaye yake shi kaɗai yana faɗa, sadeey na zaune ta ɗaura hannuwanta duk biyun taayi tagumi.
Abba zama yayi kusa da sadeey da alama da magana a bakinshi, haushi kamar ta haɗiye zuciyarta ta huta, gata dai tare da MAKASHIN iyayenta anma bata da wani yanda zatayi.
Daga inda suke tana iya hango momie kwance da robar oxygen a hancinta, ana mata ƙarin ruwa, kamar babu rai a jikinta.
Sadaukarwa ga Sadeey S Adam, ina miki fatan Alkhairi a koda yaushe
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment