New Post

Sunday, 16 October 2016

ABDUL WAHAB 29

ABDUL WAHAB 29

©Rabiatu sk msh
          ®NWA

Sai da taci ta ƙoshi ta gyara wurin, ta miƙe ta maida kitchen sannan ta dawo ta zauna taa rasa ma me zatai?

Har ƙarfe 12 tana zaune ita kaɗai tana tunani, Abdul bai shigo ba ko meya hana? Wayarta taji taayi 'kara, ita tama manta da ita ta d'auko da sauri, fatyma ce ke kiranta kamar karta d'aga saboda itama haushinta takeji.

Wata zuciyar tace 'dauka mana kiji me zatace, shru tayi bayan ta d'auka, fatyma tace "Amaryar yayanmu kinsha 'kamshi, sadeey tajaa tsaki tace wai bazaki daina sunannan ba ko? Tayi dariya tace "ay yanzu ma zan fara fad'arshi matar yayanmu, ya jikin naki ina angon? Tace "ke ohon miki, ta kashe wayar kawai gaba d'aya ta maida jikka sannan ta jinginar da kanta bakin gado.

Da azahar hajia ce ta aiko musu da abincin rana lokacin Abdul ya fita masallaci, 'yan bikin da suka kwana sunata zuwa, wasu ma bata sansu ba, da yawa dai zuwa suke ganin kayataccen gidan da akai kaita, ba 'karamin tsaruwah yayi ba ga dukiya da aka zuba mata. Ita kanta gidan yaa mata kyau sosae.

Duk wanda yazo daga gida ji take kamar ta bishi, ko kad'an zaman gidan bai mata dad'i, gata dai tare da masoyinta, anma ji take kamar don dole yake zaune da ita.

Har dare bata 'kara sanyashi a idonta ba, tsoro ta faraji don sai yanzu ta kula da girman gidan, kallo ma kasa kunnawa tayi, ta shige d'akinta can 'karshen gado ta 'kudundune, a haka barci ya d'auketa cike da tsoro.

Daya shigo baiji motsinta ba ya shige d'akinshi yayi shrin kwanciya sannan ya dawo d'akinta, can ya hangota yanda ta nannad'e wuri d'aya duk ta bashi tausayi, 'karasawa yayi ya tsaya yana kallonta, kasa ha'kuri yayi sai da yakai hannunshi ya ta'bata da sauri ta farka a tsorace.

Mi'kewa yayi da sauri yaja da baya, itama saukar da ajiyar zuciya ta dingayi gabanta na bugawa da sauri.

Yace "naga bakici abincin dare ba kin kwantane," tace "daman ina cin abinci da dare ne? Da inajin yunwa da naci, Yace "tohm shknan" ya juya zai tafi, kamar tace mishi ya dawo takeji, anma bazata iya ba, ko magana take mishi haushin kanta takeji.

Sai da ya fita sannan ta tashi ta rufo 'kofar ta dawo ta kwanta, lokacin taa fara ragejin tsoran tunda ba ita kad'aice a gidan ba.

❤❤Rabiatu sk msh❤❤

Related Posts:

  • MAKASHINKA 41-42```MAKASHINKA...```          41-42 ©Rabiatu sk msh Tun daga ranar soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, koda yaushe suna tare, wani bai iya ɗaukar lokaci bai ga wani ba.… Read More
  • MAKASHINKA 43-44```MAKASHINKA...```           43-44 ©Rabiatu sk msh Tun daren ranar take saka ran kiran daddy bai kirata ba, har barci ya ɗauketa suna cikin waya da Shamsuddeen daddy bai… Read More
  • MAKASHINKA 45-46```MAKASHINKA...```          45-46 ©Rabiatu sk msh Daren ranar har ƙarfe sha ɗaya na dare shamsuddeen da sadeey suna tare, saboda yanda suke jinsu cikin farin ciki sun ka… Read More
  • MAKASHINKA 39-40```MAKASHINKA...```           39-40 ©Rabiatu sk msh Taaji daɗin furar tasha ta sosae suna ci gaba da firarsu. Sai da maraice yayi sosae sannan Shamsuddeen yazo yafiya da … Read More
  • MAKASHINKA 43-44```MAKASHINKA...```           43-44 ©Rabiatu sk msh Tun daren ranar take saka ran kiran daddy bai kirata ba, har barci ya ɗauketa suna cikin waya da Shamsuddeen daddy bai… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts

 
seo