New Post

Sunday, 16 October 2016

ABDUL WAHAB 8

ABDUL WAHAB 8

©Rabiatu SK msh
          ®NWA

Kauda fuskarshi yayi gefe, nan take yanayin khadija ya canja ba tare da taace mishi komi ba ta juya tabar wurin, da sauri yabi bayanta

Sadeey nacan tana kallon kawayenta tana ta zuba surutun ta ,ganin su duka inda Abdul yake suke kallo sai wani dadi takeji taa wuce raini a wurin qawayenta don duk cikinsu babu mai hadadd'en saurayi kamar Abdul

Wannan ta kalli wannan, su kwashe da dariya, Sannan Daya daga cikin su tace "gaskiya kinyi dace" nan suka kara kwashewa da dariya, wadda tafi kowah dariyarnan tace "kuma da alama ji yake dake sosae," tace "eeh mana ay kinsan yana sonah sosae, d'ayar tace "tabbas yayannan naku son kowah ne, cikin jin dad'i ta dafa kafad'arta tace "harmaa da wanda bai samu ba, su kayi dariya gaba d'aya sannan sukace mata zasu koma wurin birthday d'in, tace "tohm nima inanan tahowa tare da masoyinah! Har suka tafi suna mata dariya

Juyawa tayi tana cewa, "yayanmu bakuyi ban kwana ba ko sai zamu tafi gida? Wayam ta gani babu kowa, ta zare ido tana waige-waige a fili tace "tohm ina yayanmu kuma ya tafi?

Khadija na tafiya taji alamar kamar anabinta a baya, ta juyo da sauri ya 'boye bayanta, duk inda ta juya saiya qara 'boyewa, tsayawa tayi taqi ko motsawa, sannan ya zagayo inda take yana murmushinda na kasa gano muku ma'anarshi.

Tsareta yayi da lumsassun idanunshi yana murmushi yace "meyasa kika gudu? Kina kishi ne? Da sauri ta girgiza kai duk taa rasa ma me zatace tace "kishi kuma? Da sauri ya tari numfashinta yace "eeh mana, kodai abnda raheem ya fad'amin gaske ne kina....? Da sauri tace "kaaga ni a'ah babu wani abu a raina, yace "kedai ki fadamin! Duk ya rikitata kawai ta ra'bashi zata wuce.

Yana niyyar tare ta, ya hango sadeey tana tahowa dafe kanshi yayi kamar ya d'aura hannu saman kai yakeji, har khadija ta wuce.

Ta qaraso tana fad'in "yayan mu baku Koh gaisa da kawayena ba Fah ka wuce
, ya kwantar da murya kamar dole yana murmushin yaqe yace "am sorry qanwanah, ki basu Ha'kuri kinsan bana son yawan yin Mgn shiyasa.

Tace "haba yayanmu, miye don kawai gaisawa da qawayenah?duk pa bakaga yanda suka damu dasu ganka ba.

Yace "tohm mun gaisa wani lokacin yanzu, ku taho mu tafi hajia harta kira waya, tace "haba yayanmu ya za'ay mu tafi ko farawa ba'ayi ba? 'bata rai yayi yace "shikenan saikun taho," ya juya ba don taaso ba tabi bayanshi tana kumbura fuska

*dedicated*to Mr. Smiles😃

❤❤Rabiatu sk msh❤❤

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts