```MAKASHINKA...```
35-36
©Rabiatu sk msh
Sun ɗanyi tafiya mai nisa daga unguwarsu duk a cikin garin jigawan, gani tayi yaa ɗauke hanya sun nufi wata unguwa da bata taɓa sanin akwaita bama a garin jigawa, kwatoci sunyi yawa sosae da kwazazzabai, unguwar talakawa dai sosae.
Mashin ɗinma daƙyar yake samun wurin wucewa sai kwazazzabai suke takawa, ji take yana girgiɗi kamar zai faɗi mashin ɗin, taa rufe idonta hannunta maƙalƙale jikin shamsuddeen sai ƙara take.
Tsayawa taji yayi da mashin ɗin, tun kafin ya mata umarni da diro, tana goge zufa, ya harɗe hannuwanshi biyu yana kallonta "Ki huta saimu ƙarasa tafiya"
Ta fiddo idanunta tana kallonshi "ina kuma zamu ƙara zuwa? Allah nidai na gaji daga nan bazan iya ƙara gaba ba, kaaji yanda kaina ke juyawa kuwa da muna wuce wurinnan?"
Dariya yayi sannan ya Yace "gashi ma munzo, nan ne wurinda nake kwana sadeey, nan ne mahaifata, kuma a wurinnan na tashi na ganni" juyawa tayi ta fara ƙare ma wurin kallo, bata taɓa tunanin wani mahaluƙi zai iya rayuwa a wurin ba, wani gida yafi kowanne muni a unguwar, bata ɗauka ma gida bane, Yace "ga gidanmu nan, mu shiga ki gaisa da ƴan gidanmu"
Kallo kawai ta bishi dashi ya shiga gaba, tabi bayanshi duk jikinta a sanyaye, ya yaye tsumman da aka rufe ƙofar shiga gidan da hannu, yace "Shigo" ta shiga, gidan ginin jar ƙasa ne anma duk yaa zaizaye, tana shiga filin tsakar gida ta hango, sai wani ɗaki ƙwara ɗaya can daga ƙarshen filin ɗan ƙarami, sai kewaye da aka zagaye itace aka ɗaura tsummuna, duk caɓali ne a ƙasa inda take taka ƙafarta da yake damuna ne.
Kasa ɓoye damuwarta tayi tace "anma bakayi kama da mai rayuwa anan ba Ya deen" yace "ƙwaraima kuwa, duk da nayi karatun boko sosae, bai saka na guji kakanni na ba masu sona sosae sadeey, Mahaifina Yaa rasu tun kafin nazo duniya, mahaifiyata kuma wurin haihuwa Allah ya anshi rayuwarta da ita da abinda yake cikinta, banda wanda sukafi mutanennan guda biyu sadeey da kuma mutanen unguwar nan, kullum burina in samu aiki, in tara kuɗi domin in faranta musu" tunda ya fara magana take hawaye, ta kasa furta mishi ko kalma ɗaya.
Murmushi yayi bayan ya goge ƙwallarda tazo mishi "kinga na ɓalle da surutu ko? Maganar ma da bata da wani amfani, kawai naji kamar yaa kamata in sanar dake komi game dani, muje ko"
Magana ta jiyo daga ɗakin da alama tsoho ne "kedai har kullum saikin ga zan fita abu mai amfani zaki tsaidani, tun yaushe ya tafi ɗaukota har yanzu basu dawo ba" tace "haba! Kaima kaasan bazaiji daɗi ba idan sukazo basu iskeka ba, kuma bazan aika kiranka ba" yace "yauwah Matar kirki Abinda nafiso kenan" kama gemunshi tayi tana ja kamar yanda ta saba kullum ya ɓata mata rai, rirriƙe bango yayi yana faɗin "A hankali dai, karki ciremin gemun da nake miki kwalliya, kodan kinga babu furfura kamar gashin kanki?" ci gaba tayi da jan gemun tana "zaka sani tunda ma nice mai furfura," shikam daria kawai yake mata dai dai lokacin shigowarsu sadeey.
Ba ƙaramin burge sadeey sukayi ba, kallonsu take gasu tsofaffi dai anma da alama akwai fahimta da mutumta juna a tsakaninsu wanda shine jigon soyayyar, tabbas soyayya bata tsufa koda masoya sun tsufa, kamar irin farkon aurensu ɗinnan.
Sai kuma taci gaba da bin ɗakin da kallo, gadon ƙarfene kawai da aka tila ma tsummokara, sai kwanonin wanke wanke daga gefe ɗaya, da tilin tsummokara an tilasu gefe ɗaya, tsakar ɗakin ko sumunti babu, anma duk da haka babu ƙazanta.
Muryar Shamsuddeen ta tsinkayo "ga kakanni na sadeey" duk suka jiyo tare don basu jiyo shigowarsu ba, nan da nan sadeey ta saki fuskarta tana kallonsu, su duka fuskokinsu farin ciki ne, sai sannu da zuwa suke mata.
Kaka tace "taho ki zauna nan kishiyatah tana nuna mata bakin gado," tace "A'ah kaka a nanma sai in zauna" tana nuna ƙasa" tabarma ta ɗauko cikin jin daɗin hakan, sabuwa ce bata gama shan jiki ba ta shimfiɗa mata, suka zauna ita da Shamsuddeen, sannan ta gaishe dasu kaka.
Kaka zainabu sai haba haba take taa rasa inda zata saka sadeey, jan hannun mijinta tayi suka fita, saiga abinci ana ta shigoma su sadeey dashi da fura, duk maƙota ne ke aikoma baƙuwa dashi.
Sai gashi ta dawo da roba mai marfi a hannunta, da pure water guda biyo ta ajiye gabanta shamsuddeen yace "kaka duk wannan fa?" tace "maƙota ne da suka ji zuwanta suka aiko dashi, wannan kuma malam ne ya saka a dafa mata"
Yace "hohh! Kaka duk fa na faɗa miki bazataci wannan ba, na riga da naa tanadar mata abinda zata ci, bata saba da wannan ba" nan take fuskar kaka ta nuna rashin jin daɗi, itama sadeey sai taji ba daɗi tace "nikam bazanci naka ba, girkin kaka zanci" ta miƙa hannu ta anshi robar da alama sabuwa ce, kaka tace "da gaske zakici? Tace "Yanzu ma kuwa kaka" tana buɗa robar.
Kallon abincin ta tsaya yi tana ɓata fuska, ganinka kaka da shamsuddeen na kallon ta da sauri ta wayance da washe baki tace "daman ko inason fate sosae, hakanan idan nayi marmari sai in saka aymin" kaka zainabu da shamsuddeen tsayawa sukai suna kallon kallo, sai maigidanta ne dake shigowa yace "ba fate bane, dafa dukan shinkafa ne" buɗe ido tayi tana kallon damammiyar shinkafar da ba'a ganin ko ƙwaya ɗaya, kaka yace "kin ganta nan duk da taa tsufa, har yanzu taa iya girki sosai," shamsuddeen yace "sosaima kuwa, shiyasa banijin daɗin girkin kowa kamar na kakata" ita dai sai murmushin jin daɗin an yabi girkinta take.
Ɗebo lomar farko sadeey tayi tana ɓata rai takai baki, wani irin ɗanɗano taji a harshenta data kasa koda motsa bakin ballanta na ta tauna, ta ɗago ido tana kallonsu duk ita suke kallo, babu yanda ta iya daƙyar ta iya haɗiye abincin tana kallonsu da murmushin dole.
Tun kafin ya ƙarasa shiga cikinta, cikinta ya fara juyawa zuciyarta na tashi, duk yanda taso ta riƙe aman daya taso mata kasa daurewa tayi, da gudu ta fita ta fara kwarara shi kamar ƴan cikinta zasu zazzalo.
Tana gamawa ta miƙe sai ga zugar ƴan unguwar sunzo ganin baƙuwar Shamsuddeen.
Sadaukarwa Ga Sadeey S Adam
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment