New Post

Sunday, 5 March 2017

MATATAH CE 6-10

♡MATATAH CE♡
   ♡♡♡♡♡♡
           6-10

©Rabiatu sk msh
      ®NWA
                   
            Labari....Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

  Saman mutum taji ta faɗo, ya tafi zai rik'ota, anma saida suka faɗi tare, k'afarta ta dama ta bugi wani k'aton dutsi, ta saki wata irin k'ara,
   Ya tafi inda take da sauri zai rik'ota sai kuma ya fasa,
   "Sannu kinji, kema in banda halinku na en k'auye meya kaiki hawan bishiya kina mace?" sai sannan ta ɗago fuskarta wacce tayi kaca-kaca da hawaye, ta tsagaita da kukan da take jin daddaɗar muryarshi a kunnenta, yana magana cikin natsuwa, da zazzak'ar muryarshi mai daɗin sauraro,
   Wannan kyakkyawan ɗan gayunne da ake labari duk k'auyen, Ɗan bautar k'asar da yazo musu, sunanshi ma na en gayu ko rik'e sunan batayi,

   Ya hure mata manyan idanuwanta data tsura mishi tana kallonshi, tayi saurin sadda kai cikin jin kunya,
   "Halan kin daina jin zafinne kika tsuramun ido haka kina kallo?" ba tace mishi komi ba, ta rumtse idonta kawai tanajin yanda k'afarta keta mata raɗaɗin ciwo, dai-dai lokacin su kabiruwa suka dawo, suna hangota tsugune suka nufi inda take a guje, wurin gudu suka yarda tulun nan a hanya ya fashe gaba ɗaya ruwan ya tsiyaye,

   Ta k'ara ɗaura hannu akai, "na shiga Ukuna! Kabiruwa kun kasheni"
   "sannu Saude, bamusan zaki faɗo ba da bamu rok'ek'i ki ciro mana ba" ya faɗa yana matse k'walla ganin yanda k'afarta ta fara kumbura, anma ita ta tuluntama take, taasan yau Allah ne kawai mai rabata da azabar gwaggo bilki,
    "nima bansan zaku fasa tulunnan ba da ban baku ba, shikenan yau kasheni kawai zatayi, in tafi can inda babana da mamana suke" cikin tausayawa yace "wacece zata kasheki?"
    "Matar k'anen mahaifina mana, kullum sai tamun kashedi akan tulunnan, ko gurjewa yayi saita dokeni" ba k'aramin tausayi ta bashi ba, ganin yanda take kuka, ga kuma ciwon da k'afarta ke mata,
   "ina ake siyarwa? Basai kije mata da wani ba"
  "Ba'a siyarwa a k'yauyennan fa, sai cikin gari (birni), nidai na shiga uku na"
  "Ki daina ihunnan, kije gidan sai kice mata faɗuwa kikayi, tunda ga shaida nan a k'afarki" shiru tayi kawai tana mishi kallon bazaka gane bane, ita kaɗai tasan bala'in da take ciki,

   Ta fara k'ok'arin tashi, anma har k'afarta tayi tsami, ta kusan faɗuwa da sauri taje zata rik'oshi, ta kuma fasa gaba ɗaya ta kasa taka k'afar, sai dai ta tsaya da k'afa ɗaya,
   "Sannu" yace mata ganin yanda taketa cijar leɓe, su kabiru na can gefe suna kuka, yaje zai kamata ganin ta kasa taka k'afar ta matsa da sauri, bai saurareta ba, ganin ɓata mishi lokaci take bazata iya tafiya da ita ba, ya sungumeta kawai ya nufi cikin k'auyen da ita, su kabiru suka bi bayansu suna nuna mishi hanya har k'ofar gidansu,
   Tun kafin isarsu labari ya kaima gwaggo bilki da kawu Ado, ga Saude can ta faɗi tulunta ya fashe, ɗan bautar k'asarnan ya ɗaukota zai kawota gida, tun kafin su iso taketa kumfar baki tana masifa, kamar ta haɗiye kawu Ado ɗanye, gajiyar da yayi da saurarenta ya sakashi mik'ewa ya nufi hanyar fita, sai gashi sun haɗu da Saude Yasseer na niyyar shiga da ita gidan kamar ya ɗauka en tsana,
   Cikin zafin rai kawu Ado ya mik'a hannu zai cakumota, Yasseer ya matsa da ita da sauri, ta fara k'ok'arin sauka, ya duk'a ya ajiyeta,
   "Yanzu Saude wulak'ancin naki har yakai haka? Ki faɗi da gangan ki kashema bilki tulu, yauko zakici ubanki a gidannan, Gobe ko mutuwa ce tazo muki kinyi k'ok'arin kare tulun bawai faɗuwa ba, in banda tsabar bak'in ciki ma inji da Ci dake mana, anma saikin janyo mana asara? Wallahi baki isa ba" baba Ado ne keta faman banko mata masifarnan, tunita takure wuri ɗaya, ji take inama mutuwa tazo ta ɗauketa ta huta da bala'in da zata shiga yau, shi bama ta ciwon da taji yake ba, duk da ganin saida aka ɗaukota aka kawota gida, ya saka hannu ya jawota, ta fasa wani uban ihun azaba,
   Yasseer bazai iya kallon wannan rashin tausayin ba, cikin muryar tausayawa yace "Haba baba, yanzu ko baka tausayama halin da take ciki ba, ay kaa saurara mata saboda ciwon dake k'afarta, marainiya? Baka gudun hak'k'inta a kanka, saboda abin duniya saika jikkata ta? Wannan fa k'addara ne, don Allah kayi hak'uri ka tausayama halin da take ciki,"
   Shiru kawu Ado yayi yana saurarenshi, duk jikinshi ya fara sanyi, ya kalli k'afar tata da tayi wani suntum, ga wani ciwon da taji, sai ga Gwaggo Bilki,
   "Malam tsayawa kayi kana saurarenshi? Kama manta da asarar da tamun kenan, tunda ba uban wani zai biyani ba wlhy yau sai jikinta ya gaya mata"
   "nawane kuɗin?" Yasser ya tambayeta,
   "jikka biyu da rabi (500)"
  Ya zaro mik'ak'k'ar dubu ɗaya a aljihu ya mik'a mata, cikin zalama ta saka hannu ta warce, sannan ta ɗaureta a zani, saida ta tabbatar ta ɓoye sannan ta jawo Saude, k'ii tana ihu duk ta fita hayyacinta saboda azaba,
   "tahonan, ko an biyani kuɗin ay baza'a maido min tuluna ba, kema sai kinji a jikinki asarar da nayi," ta shiga da ita cikin gidan, tana janta a k'asa sai ihu take, ga ciwon k'afa, ta dinga dukanta da wani iccen girki har k'afar take bugowa duk inda ta samu,
   Kasa jurewa Yasseer yayi, ya fita yabar gidan yanajin k'unci a zuciyarshi, hakanan Allah ya ɗaura mishi tausayin yarinyarnan. Shima kawu ado sai fitar yayi

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • HAFSATUL KIRAM 31-32[6:39PM, 4/21/2016] Rerbee'art: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                        &nbs… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 28-30[11:20AM, 4/20/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &n… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 23-25[2:03PM, 4/18/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &nb… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 26-27[12:44PM, 4/19/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &n… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 23-25[2:03PM, 4/18/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &nb… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts