New Post

Thursday, 9 March 2017

MATATAH CE 52

♡MATATAH CE♡
   ♡♡♡♡♡♡
             52

©Rabiatu sk msh
      ®NWA
                   
            Labari....Ilileee

  Ina matuk'ar baku haqurin rashin jina kwana biyu, wasu na faɗa musu uzuri na rashin charge, anma komai yaa dai daita zakuna jina insha Allah, Nogode sosae da soyayyarku ga wannan littafin.❤
    Masu tambayana daga farko, na samu naa sakashi a blog, zaku iya samunshi a can harma da wanda aka wuce👇🏻😊

www.babymsh.blogspot.com

  Da marece sosae suka isa garin, sai da aka gama kai kowa sannan ta tafi kai Saude gidan da zatayi aiki, sai kalle-kalle take ta dai daure tace, "Baba haja wai duk nan garine?"
     "eeh mana, babban birnin tarayya kenan da kikeji"
   "Aini ban ɗauka yakai girman haka ba, wannan ai sai dai a kirashi k'asa guda"
   "A'ah shima garine, ai bakiga komi ba a girman garin Abuja,"
   "Taɓ! Gaskiya ne Baba haja, kowah da garinsu"
  Baba haja na mata daria tace "hakane kam"
  Suna tafiya ta k'ara ganin wani ginin bene, shima dai kasa shiru tayi tace "Yanzu baba wannan ma mutanene suka ginashi?"
   "tohh saude kin taɓa ganin Aljanu sunyi gini?"
   "A'ah baba, anma dai yana faɗowa ko?"
     "A'ah ko zaki hau ne?" Baba Haja ta tambayeta cikin tsokana, da sauri ta girgiza kai, "A'ah ni bazan hau ba ya zurma dani ciki"
   Baba Haja na mata daria tace "ai bazaki zurma bafa"
    "A'ah nidai Baaba"

    Ana kiran Sallahr Magrib suka isa gidan da Saude zatayi aiki, Babban gidane sosae anan ma saida Saude ta cika Baba Haja da tambaya, ta ware ido sosae tana kallo, sai tayi tuntuɓe take ɗan kallon hanya sannan taci gaba.
   Saman carpet suka zauna bayan an tafi musu iso, sai faman shafawa take tanajin laushi har mai gidan ta fito da fara'arta da yake tasan baba Haja, suka gaisa cikin mutuntawa, Saude ma ta gaisheta, sannan Baba haja ta gabatar mata Saude a matsayin er aikin data nema, saida ta gama k'are ma Saude kallo sannan,
    tace, "Baba haja mantawa nayi ban faɗa miki ba, banda en matah indai an samu dattijuwa dai ita nakeso"
   "Ai duk ɗayane uwargidanah, duk aikin da dattijuwa zata miki itama zata iya"
   "Ba aikin ba ai Baba haja, ina tsoran budurwa da aiki ne"
   "tohh ai ita ba budurwa bace, gashi dai harda Goyonta"
  Dariya tayi "Haba Baba, wannan ai sai dai ko k'aninta, anma er yarinya da ita da goyo? A daiyi hak'uri a samo dattijuwar Baba, anma dai wannan batayi ba"
   "Tohh ai shikenan" Baba ta faɗa a sanyaye, ita kam Saude tuni ta lulluɓe fuskarta a mayafi, tana ta kukanta marar sauti, yanzu aikinma taga samu taga rashi.
   Abinci aka kawo musu da drinks, bata wani ci da yawa ba dai duk Baba na lura da damuwar data shiga, ana isha'i suka fito gidan.

  Suna fitowa Saude ta fashe da kuka, Baba haja ta kalleta,
     "karki kuka Saude, insha Allah zaki samu inda zaki aiki"
    "A ina Baba Haja? Nidai Saude naaga rayuwa"
   "Haba Saude, ki daina mana, ki barni inyi tunanin gidan da suka sakani neman er aiki"
  Shiru tayi sun samu wuri cikin duhun daren sun zauna, Baba haja na tunani ita dai sai shesshek'ar kuka take.
   "tohh ni Saude ina zan kaiki yanzu?"
   "ki taimakeni Baba don Allah karmu koma garinnan"
   "Yanzu tashi muje gidan Hajia, nasan ko bazata ɗaukeki aiki ba zata taimaka miki" da sauri kau Saude ta maida goyon Hafsat, ta saɓi kayanta suka tafi. Tana Addu'ah a ranta Allah yasa ta dace.

   Gabanta naa faɗuwa suka isa gidan Hajiyar, harma yafi na inda suka fara zuwa girma, ga motocinan da ma'aikata birjik, duk da darene ko ina Haske yake da fitilu masu launuka sun haska gwanin kyau duk hanyar da zasu bi, tafiya sukayi mai ɗan nisa sannan suka isa hanyar da zata sada su da cikin Gidan, gabanta na faɗuwa sukayi sallama suka shiga.
   Dattijuwar macece fara tas kyakkyawar gaske, da jin daɗi da hutu suka ɓoye shekarunta, tana zaune a falo taa gama sallamar bak'i, ta tari su da fara'arta, tana nuna musu kujera su Zauna, Baba Haja ce kawai ta zauna, anma Saude kasa zama tayi.
    "Haja Sai yau muke ganinku?" dattijuwar ta faɗa tana murmushi,
   "Hajia abubuwanne da yawa, yanzu ma en aiki ne nazo kawowa"
    "Ayyah! Wannan ta wajenki ce?"
   Tayi dariya "Ta gida daice, anma itama aikin na kawota, ba'a dace ba nace bara muzo ko kina da buk'ata"
    "tohh wannan er yarinya ina zata iya da aikin gidannan? Kuma Gaskia ban daɗe da ɗaukar en aiki ba"
   "tohh Hajia a duba dai, taimakon da kika saba"
       "tohh ai gaskia...." tayi shiru tana tunani, Saude batasan sanda kukan da take rik'ewa ya kubce mata ba,
    "tohh ɗiyata lafiya kike kuka?"
  Cikin tausayawa Baba Haja tace "Hajia nasan ke kaɗaice zaki iya taimaka mata, rayuwarta tana buk'atar taimako, batasan iyayenta ba tun kafin tayi wayau Allah ya ansa abinshi, gashi babu miji, sai musgunawar dangin mahaifi" nan Baba Haja ta fara bama hajiyar tarihin Saude komai ta faɗa mata sai dai taa ɓoye mata cewar Mijin Saude mutuwa yayi bata da aure, daman Saude taa rok'eta karta faɗa mijinta guduwa yayi ya barta, duk daman Baba Hajar bata sanshi ba.

   Tsabar tausayawar da hajia tayi mata har saida ta zubda hawaye, kuka sosai tayi daman macece mai tausayi bama kamar ga mata, "Sannu kinji Saude, gaskia naa tausaya miki, rashin iyaye ba k'aramin rashi bane, Ga na miji kuma, ni naasan zafin rasuwar miji don har yau inajin ta maigidana, shekararshi ɗaya kenan da rasuwa,"
    "Allah sarki, Allah yaji k'anshi" inji Saude
   "Ameen tare da naki, ai ke keda rashi, da k'uruciyarki babu miji babu iyaye, wallahi na tausaya miki sosai"
   Maganganun hajia kuka suke k'arama Saude,
   Ta share hawayenta cikin son kauda ma Saude damuwa,
     "Ina tsohuwar take? Kawomun itanan in ganta Allah sarki itama tayi rashin mahaifi" Saude ta kwanto Hafsa a goye, cikin tsaftar ta duk da kayanta a koɗe suke, an wanke tas babu k'azanta, kuma bata barinta tayi fitsari a wando.
    "Ya sunanta?" hajia ta tambaya tun kafin a mik'a mata ita,
   Baba Haja ce tace "Hafsat"
    "A'a'ahh ashe takwarah ce, zonan Hafsatul kiram" ta ansheta tana fara'a, itama hafsat ɗin sai washe mata bak'i take.
   Cak ta tsaya tana k'are ma Hafsat kallo, yanda take daria da sauran Abubuwa kallonta kawai take, ta kasa hak'uri dai tace "Baba Haja abun mamaki bai k'arewa a duniya"
      "Hajia wani abun ya faru?"
   "Ke baki gani ba Haja? Wallahi yanayin yarinyarnan Sak na Daddy lokacin yana k'arami, ko zuwan duk da yana babba anma yanayin fara'arsu da dariyarsu ɗaya, ke ni duk yanayinsu ɗaya ma wallahi"
   "aikau hajia nima saida kikayi magana na lura, abun mamaki kam da yawa yake, tunda nazo daman ban tambayi mutumin nawa ba, ina mai sunan Baba?"
   "Aikam saɓani kuka samu Daddy yau ya koma wurin aiki"
   "Allah sarki, mun kwana biyu bamu gaisa ba" Hafsat ta kamo fuskarta tana ta k'iriniyarta a samanta kamar sun saba, itama sosae ta fara jin yarinyar a ranta.
   Baba Haja ma kallonta take "Gaskia duk da basu kama, anma yanayin harya ɓaci"
   Hajia tace "ai daman hakane, sai kiga wani yaa haifa maka ɗa"
   "Hakane fa, kama dai komai na babarta ta ɗauko"
  
  Hajia ta nisa bayan duk sunyi Shiru, "Zan ɗaukeki aiki Saude, anma ina da sharaɗi"
   Harta farajin daɗi, kafin hajia ta k'arasa maganarta, sai kuma murnarta ta koma ciki, "ki faɗi sharaɗin Hajia, insha Allah ko menene zanyi"
    "kin tabbata?"
   Ta ɗaga kai gabanta na ci gaba da faɗuwa, "Indai zaki zauna anan, sai dai ki zauna a matsayin ɗiyata" wani farin ciki ne ya kama Saude da Baba Haja ko wannensu sai murna yake,
     "Nagode! Nagode Hajia! Allah ya saka da mafificin Alkhairi" abunda Saude kawai ke cewa kenan, tama rasa abun cewa saboda murna,
    "Ba komai Saude, hakanan tausayinki ta ɗarsu a raina, zan rik'eki amana, kema ki rik'e amana, zan zame miki gatan da kika rasa, zan baki duk abunda zaki nema a rayuwa indai Allah ya horemun ina dashi, zan baki duk wani farin ciki da zaki buk'atah"
   "Na gode Hajia, ki bani iyayen dana rasa ma yafimun komai, na miki alk'awarin bazan taɓa baki dalilin da zaki koka da halina ba"
   "Naji daɗi sosai Saude, ki saki jikinki kamar gidanku, ni kaɗaice a yanzu, bara a nuna miki ɗakin yayarki da tayi aure anan zaki zauna"
  Ta fara k'wala ma mai aikinta kira, sai gata da sauri ta mata umurnin akai Saude ɗakin ɗiyarta da tayi aure, dare yayi ta huta, hafsat ɗinma cewa tayi ta barta zata bama wacce zata kula da ita tunda an yayeta, Baba Haja ma ɗakin bak'i aka kaita ta kwanta.

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • MATATAH CE 70♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡               70 ©Rabiatu sk msh       ®NWA … Read More
  • MATATAH CE 71♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              71 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More
  • MATATAH CE 73♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              73 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More
  • MATATAH CE 72♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡             72 ©Rabiatu sk msh       ®NWA   … Read More
  • MATATAH CE 69♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              69 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts