♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
68
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
www.babymsh.blogspot.com
Watansu shidda da komawa, suka fara zana s.s.c.e, daman tuni aka saka sunanta, sai karatu ya k'aru, kullum cikin karatu take fiye da lokacin data zana j.s.c.e, tun kafinta fara jarabawar Najib ya biya mata ta rubuta jamb.
Karatun da take da maida hankalinta yasa komai yazo mata cikin sauk'i, babu abunda ya shige mata duhu.
Ranar yayesu sunsha kuka, duk da bata da k'awa ɗaya anma duk ta shak'u dasu, tasha kyaututtuka ba kaɗan ba, duk da bata rik'e wani muk'ami ba, ita ta samu kyautan tsabta, kyautan biyayya, kyautan zuwa da wuri, wacce tafi kowa cin english, maths, har teacher n su mai physic da suka sanyama ido saboda mak'o saida ya mata kyauta, da aka fiddota speach yanda take zuba turanci ba k'aramin burge mutanen wurin tayi ba, en makarantarsu kamar su haɗiyeta don murna, ta samu kyautuka sosai wanda bata taɓa tunanin samu ba.
Da dare kuma Najib ya haɗa mata nashi Partyn, duk wasu Abokanshi da yakeji dasu sun halarta a wurin, tun daga na Abuja har wanda suke aiki a Kaduna, itama ta gayyaci k'awayenta sosae har wanda bata tunani sunzo.
Ba k'aramin haɗuwa Saude tayi a wurin ba, cikin doguwar rigarta fara tas mai kwalliyan duwatsu, duk inda ta saka k'afarta Najib na biyu da ita, sosai suka haske a wurin.
A hankali tace mishi, "nafa lura duk en matan wurinnan kishi suke dani"
"Saboda kinfiso kyau da iya kwalliya ba"
Tayi dariya har hak'oranta suka fito, "Saboda ni nake da saurayin da yafi kowanne dai, kaga dole suyi kishi don nawa yafi nasu"
"laah! Kin nusar dani ma shiyasa su Jabir keta binki da kallo ko, bakinsu ya kasa shiru sai yabawa suke da haɗuwarki, aikam partynnan an tashi hakanan"
"Saboda me?"
"Saboda ina matuk'ar kishinki mana, na gaji ana ganemun matah hakanan"
"haba! Abokankane fa"
"koda en gidanmu ne, bakisan yanda nakesonki da kishinki bane, komai zan iyayi idan wani ya raɓeki"
Shiru tayi don yama rufe mata bakin magana, da yake da wuri aka fara Partyn dare baiyi wani nisa ba aka tashi, abokansu da yawa sunso yima Saude da Najib hotuna a wayansu, anma yak'i yarda, sukace ai indai sun dawo bazai hana suyi mata na biki ba.
Saida aka tashi Ahmad yazo, duk Abokansu sun gama tafiya, tare suka fito da Saude tarbanshi, cikin girmamawa suka gaisa sannan tace,
"mufa da har munyi fushi"
"Haba Matar Aboki, keda nake cewa da zaki tayani ban hak'uri"
"ai kamar nama fishi fushin fa"
"tohh afuwan, wallahi abubuwa da yawa na bari na taho, don dai kawai bazan iya hak'urin nan da sati biyu biki ba sannan inga Saudat ɗinnan data sacemun abokina gaba ɗaya"
Tayi dariya sosae "shiɗinne ma na sace duka ba zuciyarshi ba kenan?"
"ai tunda kina da zuciyarshi, ke kikeda ragamar janshi duk inda kikeso, yanzu banda wani sauran damuwa, don naa tabbatar da abokina ya bada zuciyarshi a inda ta dace"
"anma kinason gulma?"
"inasonji, anma gulma fa babu kyau"
"an gama tunda kinason ji, sirri zan faɗa miki ba gulma ba. Kinga abokina da kike ganinshi, son matane dashi don haka kisan yanda zaki rabashi da kallon mata"
Ta waro ido, "Na shiga daɗi" ya k'yalk'yale da dariya, "yanzu nasan kina sonshi yanda ya kamata, anma maganar gaskia wallahi tunda muka tashi ban taɓa sanin budurwar Najib ba bayanke, bai taɓa soyayya ba, a kanki ya fara, kuma yana matuk'ar sonki, yana tsoran yaudara, don Allah ki rik'eshi amana, kada ki raunana wannan jaririyar zuciyar tashi"
"Insha Allah, kamar yanda nasan shima bazai taɓa barin soyayyatah ba"
"Kai! Wai me kake faɗa mata ne tun ɗazu ka tsayar da matar mutane?"
"abunda basai kaji ba, yau na fara ganinta ma baza'a barni mu gaisa ba"
"nak'i ɗin, komai za'ace ayi gabana"
Mik'ewa tayi, "bara in fara tafiya, barci nakeji"
"tohm masoyiya, kiyi barci mai daɗi" Ahmad ma ya mata saida Safe, anan gidan ya kwana da Najib, washe gari tunda safe ya wuce, duk da Najib yaso ya tsaya sai bayan biki.
Saura sati biyu biki, Momie taje babban wurin sayarda furnitures na Abuja, ta zaɓar mata fitinannun kayan ɗakin masu hegen kyau, gaba ɗaya kayan sun tasarma 3million, koda aka faɗa ma Momie ko ɗar bataji ba ta biya kuɗin.
Kayan kitchen ma mak'udan kuɗi ta kashe wurin haɗa mata su, jin Saude take kamar ɗiyar data haifa, gaba ɗaya taa ɗaukema su kawu duk wani hidima, komai ita takeyi.
Haɗaɗɗen lefe Najib ya haɗoma er gatan tata, faɗan irin haɗuwar kayan da kuma kashe kuɗin ɓata lokaci ne, idan kuka tuna wanda yasai mata a tana Saudenta, akwatinan kansu abun kallone, Momie kanta ta yaba da kayan, don farko jira take kawai ya kawo ta raina saiya ƙaroma Saudenta, sai gashi ma ya wuce yanda take tunani, Saude kam har kukan murna tayi, bazata taɓa mantawa da karamcin dasu Momie suka mata ba, kullum addu'arta Allah ya bata ikon fita kunyarsu, don sun nuna mata gata sosai a rayuwah.
Gyan jiki kam kullum cikin yi mata ake, fatarta tayi kyau sosai sai santsi take, har wani ɗaukan ido take. Ta k'ara kyau fiye da daa, kamar ba Saudat ba.
Sauran sati ɗaya biki su Yasseer suka sauka k'asar, motoci akayi da yawa zuwa tarbansu, banda Saude da Najib suna gida yana tayata aikin tarban babban ɗan Momie. Tana gyaran kitchen bayan ta gama, yana zaune ya kasa ɗauke kallonshi daga gareta.
"kallonnan fa ya fara yawa Masoyi" ta ɗauka plate ta kare fuskarta.
"idan ma na kalla ai MATATAH CE, nake kallo, ki barni in kalleki, hakanan yau naji inason inyi ta kallonki"
"nidai banson kallo fa"
"ni kuma inason inyi ta kallon fuskarki, bazan taɓa gajia da hakan ba" ya janye plate ɗin a hannunta, jin k'arar motocine ya sakashi fita daga kitchen ɗin, ta rakashi da murmushi.
Ɗakinta ta koma, ta sake shek'a wani wankan, ta fito ta shirya cikin wani orange ɗin atamfa, mai zanen yellow da fari, tayi kyau sosai bama kaman data zuba ɗaurin ɗan kwalinta mai kyau, ba wani Make-up tayi ba, anma tayi kyau sosai.
Ɗakin Momie ta wuce, Rabi'ah ce kawai, ta taso da fara'arta ta tarbeta, "Sai yanzu kike fitowa? Har ina shirin zuwa ɗakinki in fito dake"
"waceni in saka matar yaya aiki? Sannunku da zuwa"
"yauwah Amaryarmu, kinga yanda kika k'ara kyau kuwa? Dak'yarma na ganeki"
"ballantana ku Aunty Rabi'ah dake k'asar waje"
"nifa da gaske nake, yanzu dai sai mun zauna kafin hidimar bikinnan ta ida haye miki za'a k'ara koyamun wasu girke-girken"
"tohm Aunty"
Fira suka shigayi da Rabi'ah, da yake Momie bata ɗaki, tana shirin tambayar Rabi'ah Momie sai gashi ta shigo.
Momie tace "yanzu na aika kiranki ashe kinanan"
"sannunku da dawowa Momie"
"yauwah sannunki da hidima"
Sai ga Najib da Yasseer sun shigo a tare, suna dariyansu da alama cikin farin ciki suke, Najib yace "Saudat, yau dai ga babban Yayana Yasseer" ya juya kan Yasseer, "Broda, ga MATATAH, Saude na gaji da wannan saɓanin da kuke samu"
Yasseer yace "A'a'tohh karma sai anyi auren mu haɗu a hanya bamusan juna ba" gaba ɗaya ɗakin saida sukai dariya, kowannensu ka kalla yana cikin farin ciki.
Hakan ya sanya Saude ta jiyo cikin ladabi ta gaishe da Yasseer, wani irin shock yaji sauraren muryarta kawai tun basu haɗa ido ba, gaba ɗaya ya kasa buɗa baki ya amsa, jin yayi shiru ya sanyata ɗago kanta, su duka saida gabansu ya faɗi, da sauri ta ɗauke kanta.
Shikam kasa ɗauke idanunshi yayi a kanta, kallonta kawai yake kaman babu kowa a wurin.
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment