♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
11-15
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
www.babymsh.blogspot.com
Saida Gwaggo ta gama dukanta son ranta, ta farfasa mata jiki ko ina zafi yake mata, tun tana ihu har tayi shiru kawai sai dai ajiyar zuciyah, anan ta barta tana jiyyar kanta ta wuce ɗaki tana ci gaba da faɗa, can kuma ta lek'o,
"Saude! Jira kike sai nace ki tashi ki ɗaura girkinnan? Ko wani kika ajje dazai miki wanke wanke da sharar,"
k'ara fashewa tayi da kuka, yanzu banda gajiyar da tayi, ga dukan da tasha, da kuma yunwar da takeji tun safe har bayan sallahr la'asar bataci komi ba, kuma duk ita tayi girkin safe da ranar, kuma yanzu wani aikin zatayi, ta yunk'ura zata tashi, ta kasa, k'afarta ma dak'yar take motsata,
Cikin muryar kuka tace "Gwaggo ina abincina?"
A harzuk'e ta yaye zanin da tayi labule dashi ta fito,
"Kikace me?" tayi k'asa da kanta, "Ban ajje miki ba, tunda ba ajiya kika bani ba, Shi matsiyacin uban naki daya tashi mutuwa meya bar miki? In banda wahalarki daya bar mana, yarinya sai shegen bak'in jini," tayi shiru tanajin yanda gwaggo ke balbalo mata masifa, harta gaji don kanta ta wuce ɗaki,
"Kuma karki tashi kiyi aikinnan har in fito in sameki"
Tana kuka ta tashi da jan jiki ta tafi ta ɗauko tsintsiyar, daga zaune haka ta dinga sharar tana hawaye harta gama don batason taka k'afarta saboda yanda take mata zugi, haka wanke wanke ma a zaune ta yishi, tanayi tana jan k'afa taje ta duba sanwa harta gama, saida akayi sallahr isha'i sannan ta samu ta huta, abincinma ba'a bata ba sai dai tabi dare taci k'amzo duk da gwaggo Bilki ta zuba mishi ruwa, shima bawai don ya isheta ba.
Daren ranar kasa barci tayi, ko ina jikinta na mata ciwo, ga k'afarta ko matsata batasonyi, sai juyi take a k'asa inda ta shimfiɗa tsammokaran kayanta, sai dai taji saukar ruwan sanyi a jikinta, ta murgina a firgice, tana zazzaro ido sai dai ganin Gwaggo tayi tsaye saman kanta, ta jefa mata bokitin dake hannunta.
"Tashi maza ki ɗebo mana ruwan Girki, tunda ke kullum sai ance kiyi" tayi tsaye tak'i tafiya, saida ta tabbatar Saude ta tashi, tanabin bango tana hawaye ta fito daga gidan, kamar mai koyon tafiya, dak'yar ta isa rafin tana haɗa hanya har gari ya fara wayewa, anan tayi sallah sannan ta ɗebo ruwan, duk yanda taso kaasa ɗauka tayi, ta samu wuri ta zauna tana kuka, ga yunwa har wani dishi-dishi take gani.
Ji tayi an dafa kafaɗarta, a hankali ta ɗago daga duk'ar da kan da tayi, suka haɗa ido ya zuba mata shanyayyun idanuwanshi dake k'ara kashe mata jiki,
"Ina kwana"
"Lafiya lau, har jikin naki ya warke ne kika fito da safennan?" ta girgiza kai tana k'ok'arin fara wani sabon kuka,
"Gaskia marik'anki basu da imani Saude ko kaɗan, kinci abinci?" ta girgiza mishi kai, kallonta kawai yake cikin tausayi,
Laida ya mik'a mata da madara da biredi a ciki,
"Ga wannan idan kinje gida saiki haɗa" tun kafin ya ida mik'o mata ta anshe daga hannunshi saboda matsananciyar yunwar da takeji, da taga laidar ma zata mata wahalar kuncewa, sai dai ta yageta kawai taci gaba daci, ya saka hannu ya share hawayen da suka zubo mishi.
Ya ɗaukar mata bokitin ruwan, "tashi mu tafi in rakaki" ta mik'e anma ta kasa tashi, "Sannu kinji, bara inzo" ya tafi cikin hanzari ya tafi cikin gari, da tambaya aka nuna mishi gidan wani mai kamu suka taho dashi, har inda take tananan yanda ya barta,
"tashi zaune kinji Saude a kama miki k'afarnan zakifi jin daɗinta"
Tace "tohh" tana k'ok'arin tashi zaune, mai kamun ma kanshi saida yayi mamakinta, ganin batayi gardama ba, ya ɗaga kai yana kallon Yasseer,
"Anma fa sai an samu mai rik'eta"
"Ba matsala, bara in rik'eta" ya zagaya inda take, ya kamota ya rik'e sosae sannan aka fara mata kamun,
Wani irin yanayi ta tsinci kanta a ciki saboda rik'on daya mata, gaba ɗaya ta k'arasa rasa kuzarinta, ko kukan zafin ciwon ma kasa yi tayi, sai k'ara shigar da kanta take a jikinshi tana jin wani irin nishaɗi, ji take daman ta k'arar da rayuwarta a haka,
Shima kwatankwacin halin data shiga, gaba ɗaya ta dagula mishi lissafi er mitsilniyar da takeyi a jikinshi, kaɗan-kaɗan zaice "Baba ba'a gama ba?" da wata irin kasalalliyar murya, shi kuma duk ya ɗauka tausayinta ne yake,
Dubu ɗaya ya bama wanda ya mata kamun, ya dinga mishi godia harya tafi, sannan ya kalli saude,
"Kiyi zamanki nan ki huta, kinga dai baki lafiya" cikin sanyayyar maganarta tace "dukana zatayi idanna daɗe"
"Ay kin riga da kin daɗe, ko yanzu kika koma zata dakeki ne, kinga nima yau bazanje inda nake koyarwa ba don dai in tayaki zama" ta ɗaga mishi kai, don itama hakanan ta tsinci kanta da son zama dashi, wani irin farin ciki takeji da tun zuwanta duniya bata taɓa jin kamarshi ba,
"Kallon ya isa haka, idan kin huta akwai maganar da nakeso muyi dake" ta maida kallonta gefe cikin jin kunya,
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment