New Post

Sunday, 5 March 2017

MATATAH CE 16-20

♡MATATAH CE♡
   ♡♡♡♡♡♡
         16-20

©Rabiatu sk msh
      ®NWA
                   
            Labari....Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

   Yaseer ya kalli Saude data tattara hankalinta wuri ɗaya tana saurarenshi,
   "Kince iyayenki sun rasu ko?" ta ɗaga mishi kai,
   "Da gaske kawu Ado k'anin mahaifinki ne uwa ɗaya uba ɗaya?" ta k'ara ɗaga mishi kai,
   "Banson ɗaga kannan, magana nakeso muyi kinji"
   "tohh"
   "Bayan rasuwar mahaifanki duk danginki babu wanda ya amsa rik'onki sai su?"
   "eeh, saboda kawu Ado bai taɓa haihuwa ba, kuma dangin mahaifiyatah suna gudun rik'ona wai hidima zan zamar musu, kuma idan aka tashi aurena dole sai sunmin kaya ɗaki da duk abunda akeyi, shiyasa ma ko zuwa inda nake basuyi, don kar baba Ado yace zai haɗasu dani"
  Ya jinjina kai, "Kenan sunsan halin da kike ciki?"
   "eeh mana labari yana je musu, anma babu wanda ya taɓa zuwa tun bayan rasuwar mahaifana"
   "to meyasa bazaki koma wurin kakanninki ba?"

Duk'ar da kanta tayi ta k'ara fashewa da kuka,
   "Babu ko ɗaya, kawu Adon fa shine kawai ya ragemun"
  "Ayyah sannu kinji, yi hak'uri daina kuka, Allah yaji k'ansu"
  Ya dafe kanshi yana sauraren kukan nata, hakanan yaji yanason ya taimaka mata, anma ta yaya?
  Ta mik'e tsaye, "k'afar babu zafi yanzu, bara in tafi gida, ngde sosae da taimakon da kaimun"
   "A'ah ni nake da Godia" ya faɗa shima yana mik'ewa tsaye,
   "Sabodame?" ta tambayeshi cikin mamaki,
   "Saboda kin bani dama na taimakeki mana, harna samu lada" ta ɗanyi daria,
  Ya ɗaukar mata bokitin ruwan, tare suka jera suka tafi, duk da tasan abunda zata iske gida, anma yau sai taji hankalinta bai wani tashi ba, idan har tana tare dashi bata da wani fargaba,

  Suna tafiya, sun kusa shiga gari, rana tayi sosae ana kiran sallahr azahar, ya katse musu shirun da sukai da cewa,
   "naga a k'auyenku auren wuri kuke, ya akai har ynzu ke bakiyi ba?"
   "lokaci ne baiyi ba, anma duk sa'anni na an musu aure harma da wanda suka haihu"
   "Hmm hakane, aina ɗauka kece bakya kula samarin"
   Tayi daria, "A'ah fa, kawai dai kawu Ado ne bai yarda ba har yanzu, anma kaga ɗan gidan sarkin noma ya daɗe yana naci, da ɗan gidan Alh musa duk garinnan babu mai kuɗinshi, harma da manyan mutane, kaga Yayan Kabiruwa ma mun daɗe muna soyayya, ynzu yama tafi birni neman kuɗi, anma kawu Ado yace bai tashi aurar dani ba, kuma nima bansan dalili ba"
   "A'a'ahh, tohh kicemun k'anwar tawa farin jini ne da ita" tayi saurin saka hannayenta biyu ta rufe idonta tana dariya,

Kallonta yaci gaba dayi, Saude yarinyace anma ba sosai ba zata kai 15yrs, jikinta ɗan k'arami, anma tana da diri komai nata a cike yake dai-dai, farace tas, kuma duk da a k'auye take tana da tsafta, ga hankali da nutsuwa duk da ba ilmine da ita ba, bata cikin duhun jahilci, tana da kaifin tunani da iya magana,
   Shi kaɗai ke tunaninnan a zuci har kawu Ado ya wucesu da k'aton ice a hannu yana muzurai ya nufi rafi, don tsabar masifa ma, bai lura dasu ba harya wuce, har k'ofar gida ya ajiye mata ruwan, sannan ya mata sallama ya tafi,

Bayan sati ɗaya...
Kullum Yasseer cikin tunanin yanda zai ceto Saude daga halin da take ciki yake, ko kaɗan baida wani nutsuwa ko wurin aiki yaje, gaba ɗaya tausayinta ke kamashi idan yana tuna halin da take ciki,
   Yau ya shirya ya tafi gidan, tun daga soro yake jiyo ihun kukanta, ba shiri ya ɓurma cikin gidan, canya hangota wurin murhu, Gwaggo Bilki na k'ok'arin saka hannunta cikin wutan, sai kuka take tana son janyewa, ganinshi ya sanyata dakatawa,
  Ranshi ya ɓaci, ga saude nan duk'e tana zubar da hawaye, suka jiyo sallamar kawu Ado daga waje,
    Tun kafin yaji abunda tayi, ya daddage ya kwaɗa mata mari, "Shegiya wahalalliyar banza, ai tunda ba wani ya bamu ajiyarki ba, baki gaji da shan azaba ba"
  Yasseer ya rumtse idanunshi, yanajin kamar shine aka mara, kawu Ado ma baisan da zuwanshi ba, tunda ba shiga gidan yake ba,
   Bai san sanda bakinshi ya suɓuce mishi ba, sai dai ya tsinci kanshi da cewa "Baba zaka bani auren Saude?" su duka suka maida kallansu kanshi, ba kamar Saude data buɗa baki cikin mamaki, shi kanshi saida yayi maganar sannan ya gano wautarshi,
    Gwaggo bilki tayi wani malalacin murmushi, don tasan yanda yake ɗan birninnan iyayenshi bazasu taɓa amincewa da Saude ba, "Mizaisa mu hanaka aurenta kuwa? Aymu jin daɗinmu nema zaka rabamu da jaraba, ko Malam?"
   Ya kalleta da mamaki, ganin yanda ta amince da wuri haka duk da yaron ɗan birni ne, "eeh, eeh mana, duk sanda ka tashi ka turo iyayenka kawai"

  Shiru yayi, tayaya ma zai iya kaima iyayenshi maganar auren er k'auye daga zuwa bautar k'asa? Yasan bazasu taɓa amincewa bama,
   "Tohh Baba nagode," sannan ya juya ya tafi jikinshi a sanyaye, Kawu Ado ya juya yana kallonta,
   "tayaya zaki saurin amincewa dashi? Bayan bamusan danginshi ba, bamusan asalinshi ba"
   "tohh ina ruwanmu da wani asalinshi? Ya tafi da ita birnin mana a yanke mata kai, ai dai mun huta, ni wallahi na gaji da ganin yarinyar nan"
   "Hakane kuma, harma mun huta"
    Tace "eeh mna," Saude dai na duk'e tana jinsu, hakanan ta kasa gane farin ciki ne take koko mamaki, anma dai tashin hankali yafi mata yawa,

Sai bayan kwana biyu da maganar ya k'ara dawowa gidan, ya faɗa musu iyayenshi bazasu samu zuwa ba, bazasu ma amince da auren ba,
   Kawu Ado yace "Toh mu ina ruwanmu da sai sunzo? Nidai na baka auren Saude, kuma nasan kai kayan ɗaki ba damunka zasuyi ba, indai ka samu inda zaka ajjeta, kazo kawai a ɗaura aure"
   "k'waraima kuwa, sadaki ai shine aure," inji gwaggo Bilki,
   Jikinshi duk yayi sanyi, ya musu sallama ya tafi,

   Wani ɗan k'aramin gida da yafi kama da bukka, ya samu ya kama haya, katifarshi da kayan girkinshi, komai dai nashi ya kwaso ya maida a gidan, Cikin sati ɗaya aka ɗaura aure, ba tare da sanin iyayenshi ba, babu wanda yasan daga inda yazo, babu wani bincike, duk don SANADIN K'IYAYYAR da Gwaggo bilki, da kawu Ado suke mata,
   Ranar ɗaurin aurenma tsirarun mutanene suka taru aka ɗaurashi, wani Abokin kawu Ado ya samu yayi ma Yasseer ɗin waliyyanci, anma fa shagali sosae gwaggo Bilki tayi kodan ta samu kuɗi safga, da dare aka ɗauka Saude aka kaita gidanta, ko abunda basu so basu haɗata dashi ba,

****
K'arar Vibrating ɗin wayarshi ne ya dawo da ita daga tunanin da take, duk ta jik'a fuskarta da hawaye, ta zabura ta koma wuri ɗaya ta dunk'ule , tana kuka jikinta sai kyarma yake,
    Daga can waje yace "lafiyarki kuwa?" Kasa magana tayi saboda tashin hankalin data shiga jin katifa na girgizawa saima ta k'ara 'karfin kukan,
       "Meya faru dake Saude? Kimun magana mana" tayi shiru dai duk ta haɗa zufa ju take kamar ginin ɗakin zai faɗo mata, kuma tsabar tsoro ya hanata ta tashi ta gudu, gashi da katifar taa ɗan daina girgizawa sai taci gaba,
    jin kukan nata yak'i k'arewa ne ya sanyashi tahowa ɗakin.

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • HAFSATUL KIRAM 23-25[2:03PM, 4/18/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &nb… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 23-25[2:03PM, 4/18/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &nb… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 23-25[2:03PM, 4/18/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &nb… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 26-27[12:44PM, 4/19/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &n… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 28-30[11:20AM, 4/20/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &n… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts