♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
56
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
www.babymsh.blogspot.com
Tun a hanya yake jiyo tashin daddaɗan k'amshi daga ɗakinshi, bai ida yarda a ɗakinshi bane saida ya shiga, tsayawa yayi yana mamaki fitarshi har an gyara ɗakinnan yayi kyau haka, tohh waya shigar mishi ɗaki? Dubawa yayi duk wani takardunshi daya ajje inda zai ɗauka baiso su rikice mar, da kayanshi dayake ajjewa inda zai buk'ata, duk dai wani abu mai amfani bai gani ba, ranshi ya ɓaci ya juya kai tsaye ɗakin Momie ya shiga.
Tun bakin k'ofa yace "Momie kin saka aimun gyaran ɗaki ne?"
"A'ah kaida kace bakaso a shigar maka ɗaki kuma"
Saude ta faɗo mishi rai yaga tana fitowa, lallai itace ta mishi shisshiginnan, Momie tace "Lafiya meya faru?"
"Ba komi Momie" ya juya da hanzari yabar ɗakin, dubata ya shigayi har kitchen bai ganta ba, can ya hangota tana tafiya ita kaɗai, da sauri ya tardata ya kama kunnanta sosai, ya ruɗe ta juyo harta buɗa baki zata kurma ihu, ya saka hannu ya rufe bakin.
A kunne ya raɗa mata "idan kika sake kikamin ihu kunnan naki zan cire" aikam ta nutsu don ba k'aramin rik'o ya mata ba, idanunta sunyi jajir don azaba kamar tayi kuka.
A tsakiyar falon ya tsaya da ita, anma bai saketa ba cikin kakkausar murya yace "waye yace kizo kimun gyaran ɗaki?"
"ba kowa"
"Dakyau isassa, idan baki maidamun duk kayana inda suke ba sai kinyi mugun shan wahala" kai ta ɗaga mishi, itadai Addu'anta Allah yasa ya saketa, yana sakinta ta fara tafiya inda ta ajje takardunshi, kamar wacce tayi harda kowanne saida ta ajje inda ta ɗauka cikin tsari,
"Na gama" ta juya zata tafi, "Dawonan" ya tsayar da ita sannan ya tafi ya fara dubawa, ko takarda ɗaya batayi kuskuren ajjewa ba, yasha mamaki sosae, sai yama rasa mezaice mata.
"Tohh maidasu inda suke" yace ba tare daya kalleta ba, ta maida kowanne tana mishi bayanin inda yake, tana gamawa ta k'ara juyawa zata bar ɗakin duk a takure take.
"Wannan ya zama na k'arshe da zakimun shisshigi a abunda ya shafeni, zanfi jin daɗin zaman ɗakina yanda yake da, don yanzu k'yank'yaminshi ma nake da kika shiga cikinshi, Momie ta kawoki gidannan, don haka indai zuciyar mutanene a jikinki karki k'ara nunamin fuskarki" ɗaga kai kawai tayi ba tare data ce komi ba, ta tafi kawai tana hawaye, sai yanzu taga wautarta ma na shige mishin da takeyi.
Tunda ta shiga ɗakin bata fito ba, ranar monday tunda safe yabar garin ya wuce Kaduna inda yake aiki, saida ta fito Momie take faɗa mata yayanta ya tafi basuyi bankwana ba, murmushi dai kawai ta mata. Saida ya tafi ta fara samun sakewa a cikin gidan, Hafsat kullum da gwarancinta saita tambaya ina Daddy, saboda shak'uwah ce sosae tsakaninsu, yanaji da Hafsat sosai kamar shi ya haifeta.
A wurin aiki kullum Najib ba sukuni, ko yaushe cikin tunanin Saude komai yake fuskarta ce ke mishi yawo, hakanan inya tuna wani abun da tayi shi kaɗai yayita murmushi, saiya gane tunanin Saude ne fa yake yayita jin haushin kanshi, duk yanda yaso ya yakice tunaninta a ranshi ya kasa.
Abokinshi Ahmad ne ya k'wank'wansa mishi kujerar da yake, ya dawo a ɗan razane, "Yadai?" ya tambayeshi, "Dai-dai, naga alamun kwana biyunnan tunani yaa aureka"
"ba wani tunani, abubuwanne da yawa"
"Ka faɗama abokinka hakan, bawai Amininka ba daya gama sanin duk wani motsi naka"
"kuma laifi ne idan mutum yayi tunani?"
"babu laifi, anma kamar kana da damuwa kuma kak'i ka faɗamun"
"nifa babu abunda ke damuna"
"Ok daman shigowa nayi, naga an tashi ko anan zaka kwana?"
Dariya yayi, "A'ah yanzu nake shirin fitowa" ya mik'e bayan yaa gama tattara takardun gabanshi, "ban baka labarin Saude ba? Da tana wurinnan zaka ga yanda zata tattara takardunnan bazakace batayi makaranta ba"
"Saude er k'yauye?"
"ita fa"
"kai kam kana son labarinnan Saudennan"
"Haba ni mezai sakani maganarta"
"Muje ko?" suka jera a tare suka fito, kowa ya shiga motarshi suka tafi.
Da dare Ahmad yaje ɗaukoshi gida zasu fita restaurant da yake shima baida aure, ya buɗe motan ya shiga, ya jawo zai rufe kenan ya fara dariya harda rik'e ciki,
Ahmad ya fasa tada motan ya tsaya yana kallonshi, donshi kanshi wani lokacin mamakinshi yake idan yana dariya don bai saba gani ba,
"wai kai lafiyanka?" bai tankashi ba yaci gaba da dariyanshi "dakai nake fa, kai daman indai anga kana dariya mugunta ne, Allah ya taimakeka bani kake mawa ba"
"nida bak'yauyarnan mana, idan kaaga yanda tayi zata rufe mota randa zan kaita gidan sista Husna, naa tabbata saika fini dariyarnan"
"Sauden dai?" Ahmad ya faɗa da cikin fara k'osawa da zancenta da Najib ke mishi,
"ita mana" kaɗa kai kawai Ahmad yayi yaja mota suka tafi don haushi ma ko magana bai k'ara mishi ba.
Suna cin abinci anma shi dak'yarma yayi cokali Uku ya ajje, sai zancen zuci yake, yadai fito fili yace "kuma kasanme?" Ahmad ya girgiza kai, "wlhy zakasha mamaki idan kaci girkin da er k'yauyennan tayi, ko a restaurent ban taɓa cin mai daɗinshi ba"
Ahmad yace "Ita Sauden ba?"
"Kaa canka dai dai" inji Najib.
"Yanzu kana da magana ne bayan tata? Tunda labarinta ne kam yanzu za'a fara jinka kana dogon surutu"
"Kamar yaya?"
"kamar yanda kake shirin bani kunya mana, duk haɗaɗɗun babies ɗin da suka rikice ma soyayyarka, ka rasa wacce zaka so sai wata er k'yauye can Saude, kullum kana cika bakin bakaga macen da ajinka zai kai ka sota ba"
"Haba! Banson iskanci fa, er k'yauye fa kuma zawara, ta inama kake tunanin dacewarmu?"
"kai ke wannan tunanin, anma a yaren So shi babu ruwanshi da wani dacewa"
"ni don Allah daina tayarmun da zuciyah, tayaya ma zanso wannan yarinyar? Ko kaɗan bata dace dani ba wallahi"
"ka daina yaudarar kanka, don tuni zuciyarka ta faɗama soyayyar Saude"
"nida nake da zuciyar ban sani ba sai kai?"
"ka taɓa sanin alamomin So?"
"Na taɓayin Soyayya ne dazan wani san alamomin so?"
"kaji matsalan, bakasan yanda akeji idan an fara soyayya ba shiyasa ka kasa yarda da kanason Saude, uku kawai zan faɗa maka ka yarda da abunda nake faɗa" shirun da Najib yayine ya bama Ahmad damar ci gaba da magana.
"Kana yawan tunanun Saude ba?" ya ɗan tsaya yana tunani, Ahmad yace "ka cemun eeh kawai"
"tohh eeh ina jinka"
"kullum kana yawan yimun maganarta, baka da zance dai saina Saude tun sanda ka dawo, na biyu kenan"
Najib ya gyara zama, tabbas sai yanzu ya fahimci duk maganganun Ahmad hakane,
"Na Ukun fa?"
"Na fahimci Saude duk abunda tayi a baya, burgeka yake yanzu ba?" baki buɗe Najib ke kallonshi yana murmushi yama rasa bakin magana "kuma naa tabbata komai kake kanajin daman Saude na kusa dakai ko babu wani dalili"
Najib na dariya yace "tohh malamin soyayya, darasi yayi daɗi har kaa faɗi huɗu baka sani ba"
"Na biyarma zan faɗa maka yanzu, sai wani murmushin jin daɗi kake ina maka firarta, wannan ma babban alaman kana sonta ne"
Dariya yayi sosae ya bashi hannu suka tafa "Tohh aini malami na dukkaa rikitani ma"
"Hahhah bafa ajin maths muke ba, maganar soyayyah ce"
"ai wani lokacin yaren mathematics ɗinma sai yafi na So sauk'in ganewa"
"ba kamar ga sabon shiga ba"
"hakane, anma fa ni har yanzu ban yarda inason Saude ba, baka ganta bafa, ni haushin shigarta ma nake"
"kana son Saude fa, ka daina yaudarar kanka, kawai ka maida ita kalar macen da kakeso"
"Kayi magana ananma zanyi tunani akai"
"Yauwah kokai fa"
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment