New Post

Sunday, 5 March 2017

MATATAH CE 46-50

♡MATATAH CE♡
   ♡♡♡♡♡♡
          46-50

©Rabiatu sk msh
      ®NWA
                   
            Labari....Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

  Kwana biyun da Yasseer ya mata alk'awari, bai k'ara ba ranar sunday da dare harma ta fidda rai da dawowarshi taa kwanta, ta jiyo bugun gidanshi da sauri ta tafi ta buɗe,
   Tsayawa tayi tana kallonshi cikin hasken farin wata, er tafiyarnan da yayo harya k'ara komawa ɗan gayun fiye da daa, kyanshi yaa k'ara fitowa, ga wani haske daya k'arayi, tama rasa ta inda zata bayyana mishi farin cikin da taji da dawowarshi, kamar ta rungumeshi takeji sai kallonshi take tana washe baki,
   Shima tsayawa yayi yana kallonta, wai nan mijintane ya dawo anma batasan yanda zata tarbeshi, Rabiah ya tuna dako igiyar shanya bata taɓa shiga tsakaninsu ba ballantana ta aure, anma data ganshi zata rungumeshi cikin farin ciki tana faɗa mishi daɗaɗan kalamai, anma ita da take matarshi batasan yanda zata tarbeshi ba, wani haushinta ma ya fara ji, tun farko meya kaishi aurenta? Er k'auye da ita duk taa canja mishi lissafi,
   "Sannu da dawowa"
      "Yauwah sannu da gida" ya wuceta ya shiga cikin gidan, tabi bayanshi yana zama ta kawo mishi abinci ta ajje.
     "A'ah na k'oshi da abincinnan, a gajiye nake kwanciya ma zanyi"
   Tace "tohh" sannan ta koma gefe ta zauna, ya gama rage kaya ya tashi ya shiga ya watsa ruwa, sannan ya dawo ya saka kaya mararsa nauyi duk tana zaune tana jiranshi, ya haye gado ya kwanta, itama bata matsa mishi ba ta raɓa gefe itama ta kwanta babu wani dogon magana a tsakaninsu.
  Washe gari ma tunda wuri ya fice, bayan ya bata kayan tsarabarta, da abubuwan daya sawo mata, yana fita ta fara buɗawa tana murna, ɗinkuna ne masu kyau kalar na birni dai dai jikinta, kala biyar da hijabbai harda takalma, ita kaɗai ta ɗinga murna a gida.
  Ta buɗa sauran kayan mayukan shafawa da kayan wanke kai, harda kayan abinci, tsarabar birni kala-kala, babu ma wanda tasan amfaninshi,

   Saida ya kusan dawowa ta shiga wanka bayan ta gama aikin gidan, cikin kayan Gwanjon daya sai mata ta zaɓi wanda tafiso a ciki ta saka, sannan ta zauna shafa, tana cikin shafa mai yayi sallama ya shigo, ta amsa.
   Yana yaye labulen yayi tsaye yana kallonta,
   "Menene kike shafawa Saude?"
  "Man shafawan daka kawomun ne"
  Ya k'arasa shigowa ɗakin duk takaici yaa cika mishi zuciya, "Yanzu Saude blue band ɗinne man shafawa? Abun da akecin bread ne fa"
   Ya duk'a yana shinshina kanta jin warin Shampoo da takeyi, k'amas babu ruwa a jiki, duk taa tsorata ganin yanda ranshi ya ɓaci, ya kama hannunta yana shinshinawa,
    "Dame kikayi wanka?"
   "Wannan sabulun mai ruwa"
"wanne irin sabulu kuma?"
Tashi tayi daga inda take ta ɗauko mishi shampoo ta mik'a mishi ya saki baki yana kallonta, duk ta marairaice da ita,
   "Saida naji k'amshin sabulu gareshi nasan wanka za'ayi dashi, kuma kumfa gareshi sosae har saida na k'ara watsa wani botikin ruwan sannan kumfan ya fita"
   Tana k'arasa maganar ya kwashe da dariya, donshi dariyama ta bashi, saida yayi mai isarshi sannan yace ta ɗauko kayan ya fara nuna mata yanda zatayi amfani dasu.

Bayan Wata Biyar.
Saura wata ɗaya ya gama bautar k'asa, zamansu ba yabo ba fallasa, tana matuk'ar girmamashi,  shima yana k'ok'arin kyautata mata, yanzu yaa daina daɗewa baije gida ba, kuma duk sanda zai dawo da sabuwar damuwa yake zuwa, gashi yanzu ya kusan gama bautan k'asa, baisan yanda zaiyi da Saude ba, don bama zai iya tunkarar gidansu da ita ba,
    Cikin watan ne ta fara laulayin ciki, wahala yake bata sosae, ya koma kusan komai ma shi yake mata, duk tayi yaushi ta rame, abunda ke k'ara mishi damuwa kenan,

   Sauran sati ɗaya ya gama bautar k'asa ya ɗauketa suka tafi gidan Kawu Ado, daman daga ganinsu shida Gwaggon suka ɓata rai, ko shimfiɗar tabarma ba'a musu ba, saidai suka tsuguna kan k'afafunsu suna gaishesu, babu wanda yayi amsawar kirki a cikinsu,
   Yasseer ne yayi magana "baba dama zuwa nayi in faɗa muku na kusan komawa gida insha Allah"
   "tohh naji, sai akayi yaya?"
  "maganar Saude ce, zata zauna anan tunda har yanzu iyayena basu san da auren ba, idan na samu lokaci zan dawo insha Allah"
  Tunda ya fara magana take kallonshi, ita batasan da maganar zai tafi ya barta ba,
   "Idan ka barta anan sai yaushene zasu san da auren naku? Ni duk wannan bai shafeni ba, Saude dai na samu na aurar da ita, don haka babu sauran wani abu tsakanina da ita, duk yanda kaso kayi da ita, anma karka sake ka kawomun ita nan"
   Hularshi ya cire saboda zufar data karyo mishi, "Akwai matsala ne idan naje da ita Baba"
   "Aini nafison a samu matsalan idan kunje, anma bazaka bar Saude anan ba, ka ɗauka matarka ku fice, idan zasu saka wuk'a su gutsuttsura ta bai dameni ba, babu sauran alak'a tsakanina da ita, don haka banma ce ku k'ara zuwa inda nake ba"
   Su duka kasa motsi sukayi, anma Saude daɗi taji sosae da Kawu yace da ita Yasseer zai tafi,
   "ku tashi ku tafi nace" kawu ya k'ara daka musu tsawa, jiki a sanyaye Yasseer yayi hanyar fita, itama ta tashi ta bishi.

  Tun daga ranar itama ta fara shirin tafiya, kullum cikin zumuɗin tafiyar take, saboda murnar tafiya birni ma ko lura da fushin da yake da ita batayi ba, ko kaɗan ya daina sakar mata fuska, bala'in haushinta yakeji, gashi kullum bata lafiya,
   Ana gobe zai tafi tana kwance tana barci, yayi tagumi yana tunanin wannan k'addararren aure, bazai iya sakin Saude ba, kuma bazai iya tafiya da ita ba, bai tanaji kalmomin dazaiyima iyayenshi, iyayen Rabiah da itama Rabiahr bayanin matsayin Saude a wurinshi, Saude Matarshi ce kuma harda ɗanshi a cikinta, ta yayama zasu tsaya harya musu bayanin er k'auyen daya aura daga zuwa bautar k'asa?.
    Yana Zaune har akayi kiran Sallahr farko, ya kalli inda take kwance tana sharar barci, kallonta yake cikin tausayawa a fili yace,
   "Kiyi hak'uri Saude, ki yafemun anma bazan iya zuwa gaban iyayena dake ba, bani da zaɓi ne bayan wannan, kiyi hak'uri ki raini ɗanmu har girmanshi, bazan taɓa mantawa da zaman da mukai ba" jin da  Yasseer yayi hawaye nason zubo mishi, ya mik'e da sauri ya ɗauka jikkarshi ta tafiya, a hankali ya buɗe gidan ya fita cikin duhun Asuba.

****
Cikin mafarki ta ganta cikin daji, gudu take iyakar k'arfinta, tana tafiya tana waiwayen baya, gaba ɗaya duhu take gani ta ko ina, batasan sanda k'afarta ta faɗa cikin wani zurmemen rami ba, ta k'walla ihu.
   Cikin ramin wani tsananin rayuwah ne ya baibayeta, ta ko ina ji take rayuwar ta juya mata baya, sai kuka take tana neman agaji daga Mahaliccinmu, tana hawaye tana rok'on Allah ya kawo mafa ɗauki.
  A hankali taga haske ya fara bayyana ta cikin ramin data faɗa, har wurin yayi haske sosae, ta ɗaga kanta tana kallon wajen ramin, idonta yayi tozali da kyakkyawar fuskar Yasseer yana mata murmushi, hannu ya mik'a mata alamar ta taho, da sauri ta tashi cikin farin ciki ta mik'a mishi hannun ya rik'e gam, wani farin ciki da bata taɓa ji ba ya ziyarceta, sai murmushi take tana murna,
   Yana cikin fiddota daga ramin data faɗa tana cikin jin daɗi, sai kuma taji ya saki hannunta ta koma ciki, tana shiga duhun ya k'ara lulluɓeta. A firgice ta farka tana Addu'ah a ranta, ta duba inda Yasseer yake kwance babushi ba alamarshi.

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • MATATAH CE 58♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              58 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More
  • MATATAH CE 61♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              61 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More
  • MATATAH CE 57♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡             57 ©Rabiatu sk msh       ®NWA   … Read More
  • MATATAH CE 59♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              59 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More
  • MATATAH CE 60♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              60 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts