New Post

Thursday, 30 March 2017

MATATAH CE 61

♡MATATAH CE♡
   ♡♡♡♡♡♡
             61

©Rabiatu sk msh
      ®NWA
                   
            Labari....Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

   Kamar yanda ya mata alk'awari, goben nayi sai gashi da wuri, tayi murna sosae da ganinshi saboda ba k'aramin kewanshi tayi ba, yanzu akwai shak'uwa sosae a tsakaninsu. Abinci kawai ta barshi yaci ta kwaso littafanta ta zube mishi.
   Cikin sauk'i yanda zata gane ya dinga mata bayani, ba k'aramin burgeta yayi ba yanda yake mata bayani daya bayan daya, rik'e take da littafin anma shi kawai take kallo hankalinta ma ba saurarenshi take ba, saida taji yayi shiru tace "Kayi shiru"
    "kina kallona ne"
      "sorry na daina"
   Yaci gaba da koya mata sosae takejin dadin karatun, Sallah kawai ke tadasu, saida ya tabbatar ta gane sannan ya barta taci gaba da karatun inda bata gane ba ta tambayeshi, har dare ko motsin kirki batasonyi, ta saka littafi tana ta karatu ko abinci tak'i taci.

   "wai bakyajin barci?"
      "zan kwanta, gobe fa ne exam d'in"
   "tohm ai karatun ya isa haka, ga abincinki tun d'azu kink'i kici"
   "ni nafa k'oshi ma, ka barni in k'arasa karatunnan plz Yaya Najib"
   "me? Tun dawowa na banga kinci abinci ba, ajje karatunnan hakanan" rufe idanunta tayi tana maimaita abunda ta karanto, ya taso zai k'wace littafin, da gudu ta canja kujera, haka suka ringa zagaye falon tak'i yarda ya ansa littafin, tana gudu tana karatunta, saida ya gaji ya tsaya.
    Sannan ta zauna, ya d'aukar mata abincin har inda take, ta wani marairaice.
    "Plz ka barni inyi karatunnan"
  "ai ban hanaki ba," ya deb'o a cokali, ya nufi bakinta dashi.
   "bud'a bakin" ta waro kyawawan idanunta, ya d'aga mata kai, kwantar da kanta tayi tana girgazashi, ya d'an rausayar da kanshi yana mata alamar eeh da idanunshi,
   Littafin ta saka ta kare fuskarta, ya sunkuyo ta k'asan littafin, babu yanda ta iya ta bud'a mishi ya bata a baki, "ko kefa, dana hana karatun exam d'innan" tak'i ma kallonshi taci gaba da karatunta, a haka yake bata abincin.

   Suna cikin ci ta bud'a baki zai bata kawai taji babu komai ta tauna cokali, ya kyalkyale mata da daria, ta aje littafin duk ta b'ata rai tana harararshi, sai dariya yake.
    "nama fasa cin abinci"
        "Sorry na daina"
    "nidai bazanci ba tunda hakane"
    "da gaske bazan k'ara ba" ya rik'e kunnuwanshi da hannayenshi biyu, sannan ta hak'ura yaci gaba da bata, saida ta kusan k'oshi duk hankalinta na kan littafi, taji ya cika mata baki da abinci, batasan sanda ta saka littafin ba ta fara dukanshi, shikam dariyarshi kawai yake.
     "kaje ka kwanta dukka hanani karatuna"
   "nak'i, tare zamu kwanta"
       "ni ba yanzu ba"
    Ya ware hannuwanshi, "nima haka" ya k'aro wani abincin zai bata, ta girgiza kai, "ni bazan k'ara ansa da cokali ba, da hannunka zaka bani" ya fad'ad'a fara'arshi harda nad'e hannun riga.
    "shi yafi komai sauk'i" tana mishi dariyar mugunta, yana saka mata hannun ta cijeshi, da sauri ya janye yana k'ara, ta mik'e da gudu tabar wurin tana mishi daria.
    "Saida safe"

   Haka suke karatun kullum cikin nishad'i, idan tana tare dashi mantawa ma take da wani auren Yasseer dake kanta, duk wani damuwarta kaucewa take ta bata wuri,  kullum bata da wani buri daya wuce zama da Najib, idan tana tuna zamansu da Yasseer da ko abinci bata iya ci a ganshi, idan yana d'aki ita zata tsaya a wajene ko nesa dashi, bai jata a jikinshi ya nuna mata abunda yakeso ba, bai koyar da ita kalan soyayyar birni ba ballantana ta mishi a matsayinshi na mijinta, soyayyar kwanciyar aure kawai ya koyar mata yanda zata mishi, da kuma soyayyarshi daya gina a zuciyarta ya tafi ya barta da k'aton tabo, zaman shekara biyu tayi da kwanaki a k'yauye ba tare da yaa nemeta ba, kuma shine yasan inda take, ya manta da jaririn cikin daya tafi ya barta dashi, da kuma igiyoyin aurenshi dake kanta.
    Idan ta zauna ita kad'aine take tunawa dashi, sai dai tayi ta sharan k'walla kawai, bada son ranta take kuka ba idanta tunashi, don batason bama zuciyarta dalilin da zataji haushinshi, domin shine mutum na farko daya fara nuna mata soyayya da kulawa a rayuwa, shine mutum na farko daya nuna tausayinshi a kanta, ta dad'e tana mishi uzurin butulcin daya mata kasancewarshi d'an adam kuma ajizi.
   K'aran dukan k'ofan Najib ne ya fito da ita daga d'akin,
     "wai ko shirin exam d'in bakiyi ba? Halan har yanzu karatun kike"
    "A'ah unifoam kawai zan saka"
   "tohm ina jiranki" har ya juya kuma ya dawo, "kuka kikayi ko?" girgiza mishi kai tayi, "ki fad'amun gaskia"
    "Da gaske ba kuka nayi ba"
  "tohm kije ki shirya" ta juya zata tafi, ya k'ara tsayar da ita "Saudat!" cak ta tsaya,
   "bansan meye damuwarki ba, anma ina jinta har cikin zuciyatah, kullum burina ki kasance cikin farin ciki, bazan tab'a bari kiyi kuka ba inda muna tare," kai kawai ta d'aga mishi, tana toshe baki ta shige d'akinta da gudu,
    Tana shiga toilet ta k'ara fashewa da kuka, “shima haka yace, 'kindaina kuka indai muna tare, hawayen farin ciki kawai nakeson gani a fuskarki (Yasseer)' yanzu gashi ya tafi yaa barni, banda wani dalilin kuka yanzu bayanshi, shine kawai silar damuwatah!!

   Cikin lokaci kad'an ta gama shiryawa ta fito, ko littafi ma bata d'auka ba, daa ko toilet zataje da littafi, ko brush take tanayi tana dubawa har dare ya raba tana karatu, anma yanzu yaa zauna mata, data amsa question paper lokaci kad'an ta gama rubuce ta, ko wani abu ya shige mata saita tuna da lokacin da Najib ke koya mata muryarshi na dawo mata yanda yake koya mata cikin k'warewa duk yanda zata gane. Shi yake kaita exam ya d'aukota ko wurin aikinma yak'i komawa sai dai yaje ya dawo, Momie har fad'an batason zaryarnan take mishi, sai dai ya bata hak'uri ta barshi na sati d'ayane kawai.

   Gobe zata gama exam d'inta,  suna d'akin Momie ita har Najib d'in, wayanta ta d'auka tana kiran wani layi, da yake hankalinta nakan karatu bataji mai take cewa ba saida ta gama ta fara fad'a.
    "Yau naaga d'an banzan yaro, kai shikenan baka da lokacin danginka baka dana Mahaifiyarka, kullum kai aiki dai, matarka dai"
   Najib yace "Momie broz ne?"
     "shi mana, shikenan kullum aka mishi waya sai yace yana busy zai kira, kuma shi bazai d'auka waya ya kira mutane ba, ya kwashi mata sun tafi k'asar turawa ya manta damunan, barni dashi azuminnan yazo bai dawo gida"
    "Momie broz Yasseer ya kusan dawowa?"
   "ai dolenshi ma ya dawo, shekaranshi nawa a can? Azumi saura wata d'aya na fad'a mishi su dawo anan za'a fara dasu, idan kunyi waya dashi ka k'ara jaddada mishi don ba k'aramin sab'a mishi zan ba ya wuce lokaci"
   "an gama momie, gaskia nayi murna da dawowarshi sosai" shi yake murnarshi, anma Momie fad'anta taci gaba dayi, ita dai Saude iyakarta saurare, ita dai ko son ganin Yasseer d'in Momien ma batayi, don tuni mai irin sunanshi ya gama b'ata damarshi a wurinta, anma dai ta lura gidan suna sonshi, Najib ma yana yawan mata firarshi.

  Ranar da zata gama exam, Najib zai kaita ckul, suna hanyarsu ta zuwa sai firarsu suke cikin nishad'i, yace "yau zaki gama junior ckul d'in, akwai maganar dazan fad'a miki anma saikin fito exam".
   "tohm shikenan kaimun addu'ah in fito lafiya"
    "Ameen dear, best ov luck"
  Tayi murmushi "tnx" sukaci gaba da firansu har suka isa.

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • ABDUL WAHAB 14ABDUL WAHAB 14 ©Rabiatu sk msh            ®NWA Yana Shiga bedrum d'insa ya tura k'ofar yasa Mata key        bai samu damar zura sleepi… Read More
  • ABDUL WAHAB 11ABDUL WAHAB 11 ©Rabiatu sk msh          ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION Suna tafe suna hira, Fatima na nuna masa hanya, tun ahanya Abdul yasa Fatima taiwa Kadija waya gatanan zu… Read More
  • ABDUL WAHAB 12ABDUL WAHAB 12 ©Rabiatu sk msh           ®NWA A falo suka iske Sadeey ta 'bata ranta sosae, tana jinsu ta maida fuskarta gefe d'aya ta qara had'a rai ita a dole an 'bata … Read More
  • ABDUL WAHAB 15ABDUL WAHAB 15 ©Rabiatu sk msh           ®NWA A harabar gidan ya koma saman resting chair ya zauna, ya fiddo wayarshi yana 'kara duba text din khadija sai murmushin jin d… Read More
  • ABDUL WAHAB 13ABDUL WAHAB 13 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Daga fatima har Abdul babu wanda ya iya magana, duk jikinsu yayi sanyi da kalaman sadeey, maganar da hajiya ta mishi ce ta f… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts