New Post

Thursday, 30 March 2017

MATATAH CE 59

♡MATATAH CE♡
   ♡♡♡♡♡♡
             59

©Rabiatu sk msh
      ®NWA
                   
            Labari....Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

   Ranar Monday kenan washe gari da wuri ta farka, barcinta kaɗanne, ta kasa mantawa da abubuwan da suka faru, kayanda ya kawo mata ta dinga ɗagawa tana gani, taji daɗinsu sosae.
    Tunawa tayi da yau fa zai koma, gashi har rana tayi k'ilama ya tafi, dirowa tayi daga saman gadon tayi hanyar ɗakin Momie, tama manta da riga da wandon kayan barci ne a jikinta, tana sauri ta koma ta saka hijabi sannan ta tafi.
   Da yake sauri take saida ta faɗa ciki ma sannan tayi sallama yana Zaune da Momie suna magana, shima jallabiyace a jikinshi da alama ko shirin tafiya baiyi ba.
   Kasa magana tayi tana tsaye dai tana kallonshi, komai ya sakama kyau yake mishi, idan ta ganshi cikin k'ananan kaya saita ɗauka duk sunfi mishi kyau, idanta ganshi a manyan kaya ma haka, yau da ta ganshi da jallabiya ma ba k'aramin kyau ya mata ba, ta manta ma da Momie a wurin. Saida ta tuna a kunyace ta gaisheta, tace
   "kinyi mamakin ganin yayanki bai koma ba ko?"
   "eeh Momie, meyasa?"
       "saboda ke" ya riga momie bata amsa, waro ido tayi tana daria, sannan ta kalla Momie.
   Ɗaga mata kai tayi "nima dai haka yacemun"
   "Daddy so yake ya sakaki a makaranta, kinason karatu?"
   "eeh inaso sosae"
      "Yauwa ki shirya yanzu ya kaiki, daman a garinku ai kina makaranta ko?"
   "A'ah banyi nisa ba, anma dai...." kuma sai tayi shiru idanunta ya kawo k'walla.
  Momie cikin tausayawa tace "kawu Ado ko?"
   Girgiza kai tayi, "Mijina dai yana koyamun a gida"
     "ki daina kuka Saude idan kin tunashi, addu'ah zakina mishi, abinda mamaci ke buk'ata kenan"
  Share hawayenta tayi "Insha Allah Momie" Najib tashi yayi ya fita kawai, Momie tace "tohh yi sauri kije ki shirya, sai kizo ki break fast"
   
   Da wuri suka isa makarantar, tsadajjiyar makaranta ce a garin Abuja, sai yaran wane ne ke a ckul ɗin, akwai ɓangaren nursery, primary, junior and senior secondry ckul. Kai tsaye ɓangaren shugaban k'aramar makarantar suka wuce (junior), cikin girmamawa ya amshesu, bayan sun gaisa Najib ya mishi bayanin daya kawosu.
   Kallon saude yayi ta cikin gilashin daya saka, "what's ur name?"
   "My name is Saude" ta bashi amsa cikin wani dadaɗan turanci kamar wata baturiya, yaci gaba da mata en k'ananun tambayoyi na en primary duk kusan taa haye, na sec ɗin daine take cewa batasan wannan ba, wanda ta sani kuma ta bashi amsa.
    "congratulations Mr. Zamu ɗauka Saude a aji uku (J.s3) duk da yayi mata girma, anma nasan insha Allah karatun bazai mata wahala ba don da alama tana ganewa, sai dai kuma a samu wanda zaina koya mata a gida"
   "Insha Allah, wannan ba damuwa bane, nagode sosae"
   "jin daɗinmu ne"

   "Saude wa za'a rubuta mata jikin admission ɗin?"
   Kallonta yayi, "ya sunan babanki?"
   "Saude Yasseer za'a sakamun"
  Yamutsa fuska yayi, "Yasseer ba sunan baban Hafsat bane?" ta ɗaga mishi kai, wani irin haushinta yaji, cikin muryar ɓacin rai yace,
   "sunan babanki nace ki faɗamun" duk sai taji ba daɗi da yanayinshi ya canja,
    "Muhammad"
        "Saudat Muhammad za'a saka mata" saida ya tabbatar an gama mata komai daya dace, ya biya kudaɗe da yawa,  sannan suka tafi  ko kallan inda take baiyi, wani irin haushinta yakeji. Anan ckul ɗin aka bata unifoam da littafai, suka wuce gida washe gari zata fara zuwa.

   Har sukaje gida yana fushi da ita, yanayin parking da sauri ta buɗe ta fita, don karma ta k'ara ɓata mishi rai, sauri take taa kusan shiga ɗakinta taji taji ya kira sunanta.
    "Saudat!!" saida ko ina ya amsa sunan cikin kanta, har k'asan zuciyarta takejinshi da kuma yanayin daya faɗa, bata taɓa sanin haka sunanta yake da daɗi ba sai yau daya k'ayatar dashi, saida ta rumtse ido tama kasa juyawa, ta kasa ci gaba da tafiya sai dai ta tsaya wuri ɗaya.
    "Saudat!" ya k'ara kiran sunanta, still dai bata waiwaya ba, ya ɗanyi tafiya gab da inda take, magana yake mata yanda ita kaɗai zataji.
     "Yau zan tafi, ko kaɗanne kina sakani cikin tunaninki, plz a sanmin wurinda za'a dinga tunawa dani cikin inda ake tuna baban Hafsat"
  Jinshi gaf da ita ya saka ta jawo mayafinta ta rufe fuska,  ta kasa bashi amsa tana jiran ya tafi, zagayawa yayi inda take yana lek'en fuskarta ta cikin mayafin da sauri da rufe wurin, ya juya ɗaya bangaren nanma ta rufe, haka suka dingayi saida taji kamar ya tafi ta buɗe fuska, da sauri ta zaro ido data ganshi gaf da ita.
     "Zan tafi ko damuwa bazaki ba ko?" girgiza mishi kai tayi,
   "banda amsa ko?" shiru ya juya zai tafi, a hankali tace "Yaya Najib" ya juyo yana kallonta, "Allah ya dawo dakai lafiya"
   Ya sakar mata murmushi, "Ameen".
     A ranar ya wuce kaduna, bayan ya tabbatar da ya samar mata mai lesson da drivern dazai kaita ya ɗaukota.

  
Page ɗin yau yayi kaɗan na sani, plz kumin uzuri donma banso ku jini shirune, na gaisheda duk wani Masoyan littafinnan, k'aunarku da nake batta da iyaka❤

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • HAFSATUL KIRAM 26-27[12:44PM, 4/19/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &n… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 31-32[6:39PM, 4/21/2016] Rerbee'art: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                        &nbs… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 23-25[2:03PM, 4/18/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &nb… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 28-30[11:20AM, 4/20/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &n… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 28-30[11:20AM, 4/20/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                       &n… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts