New Post

Thursday, 13 October 2016

HAFSATUL KIRAM 28-30

[11:20AM, 4/20/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

          2⃣8⃣

A rud'e ya d'auketa ya fita da ita zai saka mota, mai gadi Ya taso yana cewa "lapia ranka shi dade? Cikin rud'ewa yake mishi bayani! Yace "bud'emin gate asibiti zamuje!

Mallam mai gadi yace "ranka shi dade ay sai dai ayi mata na hausa, anyi sa'a kuwa bni rabuwa da maganinshi bari in dauko, da hanzari yaje d'akinshi ya d'auko, Umar dk yaa rud'e sai jijjigata yake, jiqa maganin akai ya d'ura mata a baki ynda zai shga cikinta! Yana shafa mata ruwa a fuskarta!

Tana bud'e ido ta fara kwarara Amai baqiqirin a jikin umar dk taa 'bata mishi jiki, shikam sannu kawai yake mata taa kasa magana jikinta baa qwari dk yaayi laqwas kallansu kawai take tana lumshe idi daqyar saboda wahalan da tasha!

'Daukarta yayi ya kaita d'akinshi, ya kwantar da ita saman gado yaa kasa canza mata kaya ko hijabin yaa kasa cire mata, sai dai ya kunna mata A/C, toilet ya shga yayo wanka ya gyara kanshi!

'Kasa ya saukar da filo saitinta ya kwanta, baiyi wani barcin kirki ba hnkalinshi naa kanta, itakam barcinta takesha cike da gajia ga wahala kuma!

Ana kiran sallar Asuba ta bud'e idonta a hnkali, lokacin yaa fita masallaci bai tasheta ba, ta shga toilet tayo alwalla ta fito ta tada sallah bata koma d'akinta ba, hannunta naayi mata zogi sosae, daurewa kawai take

Gari har yaa fara haske ya shgo tana zaune saman sallaya taa gama azkar, riqe tana da hannunta sai cije baki take saboda azaba ya shgo, ta miqe da sauri zata bar d'akin, Yace "ina zakije? Tace "break fast zan had'a mka, gari harya fara haske!

Yace "da baki lafiyar? Tace "ay zai bari ne, ta wuceshi zata fita ya riqota ya maidata kan gado ta zauna, ya ciro maganin Aljihunshi ya fara shafa mata a hannunta Yace "mallam mai gadi yaace idan aka shafa miki insha Allah zai daina miki zafi!!

Batace mishi komi ba, kallonshi kawai take riqe da hannunta, cike da shaqi batasan ma sanda ya gama ba, shima tsayawa yayi yana kallonta da sauri ta sadda kai, ya dafa kafad'arta da duk hannunshi, Yace "Tabbas hafsatul kiram, momie taayi gsky! Bzan taba samun mata kamarki ba, ke mace ta gari ce, kowanne namiji zaiyi alfaharin samunki a matsayin mace, naa dad'e ina cutar dake, don Allah ki yafemun hafsatul kiram, bnda wani farin cikin daya wuce samunki a matsayin mace! Kin sadaukar da taki rayuwar saboda ki ceci tawa kawai! Dk da kinsan zaki cutu, don Allah ki yafemun!

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥
[1:01PM, 4/20/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

          2⃣9⃣

Dago kanta tayi ba tare dasun had'a ido ba tace "Ay kai mijina ne yaa umar, tsare haqqoqinka, yi mka biyayya, dabin umarninka yaa zamemin dole, ka daina kunyata ni wurin neman yafiya a wurinah! Ni matarka ce!!

Tashi tayi ta fita, ta barshi zaune jikinshi duk yaayi sanyi da kalamnta, kaasa motsawa yayi maganganunta naayi mishi yaawo akai

'Dakinta ta wuce ta kwanta, sai kallon silin take tana juye juye, jinta take a wata duniyar daban, taa kasa gane farin ciki take kome? Yanayin data kaasa ganewa kenan!

Tana cikin tunanibya shgo da shirin tafiyarshi office, ya ajiye mata take away Ya duqa saitin fuskarta ta rufe ido, Yace "ba rakiya? Tace "Allah ya kiyaye hanya, ya dawo dkai lafiya! Bai samu fuskar qarayi mata magana ba dk kunyarta yakeji ma yaayi sukuku, Yace "idan kina buqatar wani abu kimin waya! Batace mishi komi ba harya tafi!

Da marece Umar ne da deezy zaune wurin wani shaqatawa! Yaayi shru yaa rasa ta inda zai fara mata, fuskarshi cike da damuwa yaa kasa bud'e baki ya mata magana! Tace "zumah kaa kurani kaayi shru, gashi da alamar damuwah a fuskarka, hafsatul kiram ce ta 'bata mka rai ko?
     Ya girgiza kai yace "tabbas inada damuwah! Anma b daga hafsatul kiram bane, tabbas na cika son kaina, naa damu da farin cikinah ne kawai bn damu da nata ba, deezy naa cutar da rayuwar hafsatul kiran da yawa! Anma yaa isa hka, babu wani mijin da ya isa ya bautar da matarshi, ya quntata mata ya cutar da ita kamar ynda nayi mata, inason matata hafsatul kiram, kiyi haquri da soyayyarmu! Miqewa tayi tsaye kamar wadda aka tsikara!

Tana nunashi da yatsa tace "meka daukeni ne Umar? Kaa maidani kamar wata qwallon da zaka buga duk sanda kakeso? Kaason irin sonda nake mka anma duk sanda na saki jiki muna soyayya saika barni? Yace "ki fahimceni deezy, hafsatul kiram matatah ce, nasan dole zakiji ciwo a zuciarki, wannan ciwon shi hafsatul kiram ta dade tanaji a zuciarta! Bxan iya ci gaba da aikata kuskure guda d'aya a rayuwatah ba! Inason hafsatul kiram.

Bai jira me zatace ba ya ra'bata gefenta ya wuce, tace "ka saurareni Umar, bzaka ta'ba rabuwa dani irin hka ba! Ko waiwayenta baiyi ba ya wuce yabar wurin!

Yana isa d'akin hafsatul kiram ya wuce tana gaban madubi, tsayawa yayi yana kallonta yaa kasa d'auke idonshi a kanta, ba qaramin kyau tai mishi ba, wannan ne rana ta farko daya fara ganinta babu hijabi, juyawa tayi suka had'a ido taga ita kawai yake kallo ko qiftawa ba yayi! Sai lokacin ta lura bata saka hijabi ba kunya dk ta lullu'beta ta jawo hijabinta ta saka!!

Lurv my princess Amrah

♥♥Rabiatu sk msh♥♥
[1:56PM, 4/20/2016] Rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
                          🎄
                       🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
              🎄🎄🎄🎄🎄
                 🎄🎄🎄🎄
                    🎄🎄🎄
                       🎄🎄
                          🎄
           NA
  Rabiatu sk msh

          3⃣0⃣

Sannan ya saki ajiyar zuciah ya qaraso inda take, tsayawa tayi tana kallonshi ba tare dasun had'a ido ba, hannu yasa ya cire mata hijabin, ta sadda kanta kunya dk taa lullu'beta.

Hannu ya sanya ya dago da fuskarta yace "nafison ganinka a haka hafsatul kiram, kinyi matu'kar yin kyau! Tayi murmushi har lokacin idanunta a 'kasa, ya zaro takardu a cikin aljihunshi ya miqa mata, tace "na menene? Yace "ki gani da kanki!

Takardun asibiti ne, Awon H.I.V, duk babu ta dago ta kalleshi Yace "zan miki alqawari tsakaninah dake, daga Yau babuni babu wata mace, babu ni babu shan duk wani abin dazai sakani maye, ki yarda dani hafsatul kiram Inasonki sosae, zan sanyaki farin ciki har 'karshen rayuwatah!

Rumtse ido tayi dadi naa ratsa mata zuciah, ji take kamar taafi kowa farin ciki da dace, lallai maha'kurci mawadaci, 'bude baki tayi zatayi magana taama rasa me zata fad'a, murmushi kawai take a fuskarta!

Wayarshi ce tayi ringing, ya ciro ya duba sunan deezy a screen d'in, hafsatul kiram ya kalla yaga bashi take kallo ba ya maida wayar silent ya ajiye, wani kiranne ya 'kara shgowa bai d'auka ba harta qara katsewa, kusan sau biyar da yaga bata da niyyar daina kira ya kalli hafsatul kiram Yace "ina zuwa, da murmushi a fuskarta ta d'aga mishi kai ya fita falo ya d'aga wayar!

Muryarta da alamar kuka take magana "zumah don Allah karka gujemun, bzan iya rayuwarda babu kai a tare dani ba, inasonka karka cutar dani ta wannan hanyar! Yace "kiyi haquri deezy hafsatul kiram ita kad'aice matata, da ita kad'ai zan kasance har abada! Tace "kana nufin kaa daina sona?? Bai bata amsa ba ya kashe wayar! Ya juya ya koma wurin hafsatul kiram!

Wurgi tayi da wayar ta tarwatse zuciyarta kamarta fashe duk abnda ke kusa da ita saida tayi wurgi dashi, ta fad'a saman kujera ta saki wani irin kuka!

Lurv my princess Amrah😘

♥♥Rabiatu sk msh♥♥

Related Posts:

  • HAFSATUL KIRAM 36-37[4/28, 3:50 PM] ✍🏻rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                     &nb… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 38-39[5/1, 10:54 AM] ✍🏻rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                     &nb… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 40-43[5/2, 10:29 AM] ✍🏻rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                     &nb… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 33-35[6:17PM, 4/23/2016] Rerbee'art: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                        &nbs… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 31-32[6:39PM, 4/21/2016] Rerbee'art: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                        &nbs… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts