```MAKASHINKA...```
49-50
©Rabiatu sk msh
Tsoro ne ƙarara a fuskar Abba tun bayan ɓacewar shamsuddeen yana ta zagaye ɗakin da bindiga yaa kasa tsayawa wuri ɗaya, zufa na kwarara ta ko ina a jikinshi yace ma momie "mun shiga ukku zai kashe mu"
Momie tace "miye na saurin tsorata kuma Alhaji?" ya share zufa yaa kasa cewa komi sai sadeey ce tayi ƙarfin halin magana duk da kanta a ɗaure yake "Abba bafa ku yace zai kashe ba wanda suka kashemin mahaifana zai kashe, kuma ƙarya yake shine ya kashe su na ganshi da idona" Abba Yace "mutum ne mai hatsari sadeey, dole ne mu tsorata da Al'amarinshi" sadeey tace "mugu bazai taɓa tsira ba Abba, bazan taɓa bari ya kashemin ku ba kamar yanda ya kashemin iyaye".
Police ne suka ƙaraso gidan, Abba baice mata komi ba ya juya ya fita momie ta bi bayanshi, suka tafi su ƙara ma police bayani.
Duƙar da kanta tayi ta fara shessheƙar kuka mai ƙona zuciya, ta daɗe a haka sannan ta ɗago jin numfashi kusa da ita ta fara kalle kalle har lokacin kuka take, cikin kukan ta fara magana da ƙarfi.
"Shamsuddeen! Nasan kana jina, ka yaudareni, kaaci Amanatah, kaayi amfani da soyayyar da nake maka, Anma yanzu wannan soyayyar taa daina tasiri, naa tsaneka, bazaka taɓayin nasara a kaina ba, saina kama ka, na miƙa ka ga hukuma, ko in kasheka da hannu nah, naa tsaneka Shamsuddeen"
Tana gama faɗar haka ta ƙara fashewa da kuka, Duk da bazan iya ganin shamsuddeen ba, anma daga inda yake laɓe ina iya jiyo shessheƙar kukanshi kona miye?
Miƙewa tayi jikin ta ba ƙwari ta fito falo, inda Abba ke ci gaba da yima police bayani duk tashin hankali ƙarara a fuskarshi, "bansan inda ya samo siddabarunnan ba, anma yananan a raye ganinshi ne kawai ba'ayi, ko tsafi yake dole ne ku kamashi domin rayuwar yarinya tana cikin haɗari saboda yanda yake bibiyarta,"
"insha Allah Alhaji zamuyi iyakar ƙoƙarinmu"
"ba iyakar ƙoƙarinku ba, dole ne kuyi, ku gaggauta samoshi" sannan ya saka hannu aljihu ya kawosu kuɗi Aljihunshi ya miƙa musu sukai sallama suka koma.
Anwar ne ya shigo gidan fuskarshi cike da alamomin tambaya ganin police sun fita daga gidan, Yace "momie, Abba me police suke a gidannan?" Abba yaja tsoki Yace "ka rufa mana baki tunda Al'amurran gidannan ba damunka sukayi ba," Yace "Abba dai ya kamata in sani ko?" Abba yace "ban cikin yanayin, tambayi uwarka ko ƙanwarka" sai lokacin yasan da sadeey a falon ya juya suka haɗa ido, da sauri ya miƙe saboda Abinda ya tuna zai bar falon.
Ba wanda ya ƙara magana sai shiru da suka yi gaba ɗaya kowa da Abinda yake saƙawa, Ranar a ɗakin momie sadeey ta kwana duk da kusan babu wanda ya runtsa a gidan gaba ɗaya tsanar shamsuddeen takeji a ranta yanda ya kawo mata matsala a rayuwar, ya rabata da duk farin cikinta.
Washe gari ma gidan kamar gidan makoki, Abba kamar bazai fita ba sai da rana tayi sosai sannan ya fita aiki, Anwar daman bai shiga Al'amarinsu, momie da take da bashin barci Abba na fita ta kwanta taci gaba da barcinta.
Sadeey jin shiru ya mata yawa, ga tunanin daya matsa mata har ya sakar mata ciwon kai, ta miƙe kawai ta fito daga gidan gaba ɗaya, can ta fita gefen garden don ta samu sauƙin tunanin.
Ƙamshin furanni na ratsata, iska mai daɗi na kaɗawa, duk da haka zuciyarta ba daɗi tafiya kawai take.
Jin numfashi takeyi kusa da ita, batayi wani yunƙuri ba ta ci gaba da tafiyarta kawai, jin Abin yaƙi ƙarewa yanata ƙara matsowa inda take, tayi dubarar tsayawa cak tana ƙara nazarin inda take jiyo numfashin.
Cikin zafin nama ta miƙa hannu ta taɓoshi da sa'arta kuwa dai dai hannunshi ta kama ta riƙe, cikin dakewa tace "yau sai inga ta yanda zaka tsere min shamsuddeen" yana ta ƙoƙarin ƙwacewa anma ta riƙeshi gam tana cije baki.
Suffarshi ta bayyana dishi-dishi ba gaba ɗaya ba, ta fara ƙiƙiniyar janshi ta fita dashi daga garden ɗin yana cijewa bai mata magana ba dai yana kallon ikon Allah.
Wata irin fizga yayi ma hannunshi ya ƙwace, ita kuma ta ɓulle gefe ɗaya ta faɗi kanta ya bugu sosae.
Juyawa yayi zai bar garden ɗin, ko meya tuna kuma ya dawo? Ya daɗe yana shawara a ranshi sannan ya ɗuka inda yake ya ɗauketa a hannunshi.
Sadaukarwa Ga Sadeey S Adam
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment