New Post

Sunday, 16 October 2016

ABDUL WAHAB 34

ABDUL WAHAB 34

©Rabiatu sk msh
          ®NWA

Fatyma ta dafa kafad'arta cikin tausayawa tace "shi yayanmu ne yake miki hakan? Cikin jin haushi tace "A'ah ni nakeyi mishi, fatyma tace "Allah ya baki ha'kuri, anma dai bai kyauta ba yayanmu.

Tace "kema kya fad'a, ni na gaji da zaman gidannan, tashi zanyi in shirya kawai mu tafi, 'kara a aura mishi wadda yakeso fatyma, kinsan ina son yayanmu, yana amfani da wannan damar ne kawai yana wula'kantani.

Fatyma tace "duk bata kai haka ba sadeey, wlhy yayanmu yana sonki, ina soyayyar da kike mishi da har kika kasa sakin jiki dashi? Don Allah ta yaya zakuci ribar soyayyarku idan kuna haka?

Sadeey tace "yauwah, daman nasan ay ba yarda zakiyi dani ba, bazaki ta'ba ganin laifin yayanki ba fatima, tace "nifa ba haka nake nufi ba, ki tsaya ki fahimceni, idanma yayanmu bai sonki aike kina sonshi, kefa macece sadeey kinsan yanda zaki shawo kanshi.

Tace "ba wani ni ban sani ba, komi ma na mishi ba burgeshi nake ba, kullum saiya fadamun rashin khady ne kawai ya sanyashi aurena.

Fatyma tace "shikenan tunda baki sani ba, ni bari in fad'a miki, sadeey saurarenta kawai take cikin jin haushi tama maida ita 'karamar yarinya, fatima kam taa dage sai kora mata bayani take.

Anan ta yini har bayan isha'i sannan kabir yazo tafiya da ita, jikkarta ta bud'e ta mi'ka mata wata laida, tace "Menene? Fatima tace "tsaraba ce, kedai ki ajiye ranar da zakiyi amfani dasu kimin waya zan gaya miki kona menene, tace "tohm nagode.

Hijab ta saka ta rakata har wurin motarsu, suka gaisa da kabir cikin raha sannan suka wuce, ko a gaishe dasu hajia da mami bata ce ba.

***
Yau sauri yake ya koma gida kafin tayi barci saboda tunanin shawarar daya yanke, don yana cutuwa da yawa kullum surar sadeey 'kara rikitashi take, cikin sa'a sanda ya shiga d'akinta tana toilet tana wanka, taa ajiye lemu a cup saman bed side, lalla'bawa yayi, ya saka 'kwarar maganin dake hannunshi a ciki ya motsa sannan ya fita da sauri.

Yana fita ta fito daga wankanta, saida tayi 'yan shafe-shafenta sannan ta ciro kayan barcinta ta saka, ledar da fatima ta bata ta gani, cewa tayi bari ta d'auko taga menene a ciki, powder ce ta fara fiddowa, tace "yanzu fatyma powder ma saita koyamin amfani da ita? Gaban mirrow taje ta shafa, taga taayi mata kyau sosae.

Ta 'kara ciro turare a 'yar kwalba, ta sha'ki 'kamshinshi yayi mata dad'i sosae, ta shafe jikinta ko ina dashi, sannan ta maida ledar ta kwanta hankalinta kwance bayan ta shanye lemon data ajiye.

Dedicated to Mr. Smiles😃

❤❤Rabiatu sk msh❤❤

Related Posts:

  • MAKASHINKA 5-6```MAKASHINKA...```            5-6 ©Rabiatu sk msh~ Har washe garin dawowarta duk bata cikin nutsuwarta, duk yanda ta ƙagara ta gama karatunta ta dawo nigeria sai ta… Read More
  • MAKASHINKA 3-4```MAKASHINKA...```           3-4 ©Rabiatu sk msh~ Momie ta kalle ta tace "lafiyarki kuwa? Sadeey Tace "lafia lau momie me kika gani? Momie tace "dukkin fita hayyacinki da ala… Read More
  • MAKASHINKA 3-4```MAKASHINKA...```           3-4 ©Rabiatu sk msh~ Momie ta kalle ta tace "lafiyarki kuwa? Sadeey Tace "lafia lau momie me kika gani? Momie tace "dukkin fita hayyacinki da ala… Read More
  • MAKASHINKA 5-6```MAKASHINKA...```            5-6 ©Rabiatu sk msh~ Har washe garin dawowarta duk bata cikin nutsuwarta, duk yanda ta ƙagara ta gama karatunta ta dawo nigeria sai ta… Read More
  • MAKASHINKA 1-2```MAKASHINKA...```              1-2 ©Rabiatu sk msh~ Wannan littafin sadaukarwa ne ga ```Sadeey S Adam``` (Kishiya), ban yarda wani ko wata ya canjamin wani a… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts