New Post

Sunday, 23 October 2016

MAKASHINKA 47-48

```MAKASHINKA...```
          47-48

©Rabiatu sk msh

Cigaban labari....
Ruwa aka dinga yayyafa ma sadeey bayan doguwan suman da tayi, momie ta kira Abba a waya ta sanar dashi duk abinda ke faruwa.

Ana shirin tafiya da ita asibiti taja numfashi ta farfaɗo duk taa fita daga hayyacinta, duk tambayoyin da ake mata a ruɗe take taa kasa bada amsa sai dai binsu take da kallo.

Abba na zuwa yace su shiga mota su tafi gida tunda sadeeyn bata cikin nutsuwarta, har ɗaki momie ta rakata ta kwantar da ita don ta samu hutu sannan ta fito ta barta.

Idonta a buɗe anma taayi shiru sai tunani take idanuwanta na kallon sama, ji tayi kamar an riƙe mata hannu, ta duba babu komi ta janye hannun zata juya taji an ƙara riƙeshi sakeshi tayi ta fara ƙoƙarin ɗaga shi.

A sannu take suffar mutum ta fara bayyana dishi-dishi yana ƙara duhu har ya koma mutum lafiya lau, ba tare data ɗaga kanta ba cikin sarƙewar murya irin ta wanda ya gama tsorata tace "wanene kai?" yace "ki ɗago fuskarki ki kalleni".

Ko a cikin mafarki ba zata taɓa mantawa da wannan muryar ba, ko ina a jikinta kyarma yake dakyar ta iya saita idanunta a kanshi, haƙoranta na bugun juna ta kasa furta komi yace "ki saurareni sadeey, magana ce mai muhimmanci nakeso in sanar miki, nasan a yanzu babu sauran yarda tsakanina dake, kin riga da kin gama tsanata, wlhy har yanzu baki da wani mai sonki sama dani, ki saurareni zan miki bayanin komi".

Wata irin ƙara ta saka da har sai da su Abba suka jiyo da sauri suka taho, hannu shamsuddeen ya saka ya rufe mata baki yace "karki min haka sadeey, ki saurareni rayuwarki tana cikin haɗari, babu laifina a ciki.

Bata ce komi ba taci gaba da kukanta mai sauti sai ga Abba da momie sun buɗe ƙofar sun shigo, kowanne cikinsu ya kaɗu da ganin shamsuddeen, shi kanshi cikin mamaki yake cikin sauƙi baza'a iya fassara yanayin daya shiga ba.

Abba ne ya ciro waya da sauri zai kira police, Shamsuddeen ya fara ja da baya zai fita ta ƙofa, wata ƴar ƙaramar bindiga Abba ya zaro yana nunashi da ita yace "karka sake ka motsa in fasa kanka da bindigarnan"

Cikin dakewa shamsuddeen yace "Anma kasan kuskuren da kayi na nunamin bindiga da kuma kiran police ko? Abba yace "kaine dai kayi kuskure daka shigo gidannan, ran yayana da iyalanshi daka ɗauka bazaka taɓa tsira ba kaima saika rasa naka ran"

Shamsuddeen Yace "nine nan zan ɗauki fansar duk wanda yake da hannu a kashe iyayen sadeey da hannuna zan kasheshi," Abba yace "idan ka rayu ko? Zan ga ta yanda zaka fita daga gidannan!

Murmushi shamsuddeen ya karayi hannunshi na ɗage a Sama, Yace "ka manta zan iya ɓacewa?" tun kafin Abba yayi magana sai dai suka daina ganin shamsuddeen, suka shiga dube-dube a ɗakin sadeey babushi.

Sadaukarwa Ga Sadeey S Adam

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • MARYAM KO MARYAMA 41-60Rabiatu sk novels [11:59, 3/11/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣soyayyar whatsapp❣ @OHW 41-50 Washe gari yaa kama ranar monday, suka shrya maryam da maryama suka fito zasu tafi school, Mary… Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 61-80[14:07, 3/12/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣soyayyar whatsapp❣ @OHW 61-70 Maryama ce kwance tana chat da abn qaunarta wani irin farin ciki takeji dk sanda suke tare, murmushi tayi tace Ma… Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 81-100[14:07, 3/14/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣soyayyar whatsapp❣ @OHW📚 81-90 A rude Maryam ta duqa tana tattara wayar, Maryama tayi tsaye kamar ana hura mata wuta a qirji don sosae … Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 21-40[10:39, 3/10/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣Soyayyar whatsapp❣ @OHW 21-30 Tana bude datar messages da yawa suka shgo mata, anma naashi ta fara dubawa, da wayarta glaxy s5 wadda Abokinta A… Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 100-110[14:17, 3/15/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣soyayyar whatsapp❣ @OHW 100-105 Ta miqa hannu zata yaye labulen falon kenan wayarta tayi qara har sai data tsorata, ta duba taga sunan Aboki A … Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts