New Post

Monday, 31 October 2016

MARYAM KO MARYAMA 171-180

[17:49, 3/23/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿
❣soyayyar whatsapp❣
@OHW
171-175
Da dare suna zaune suna fira da Maryam taaje yi mata sai da safe, Maryama tace "namcy kin wani shgo kin kwanta kizo muje falo muyi fira, tace "brni kawai takwarah wlhy dk yau kasala nakeji, kedai kije deen na jiranki! Riqe baki Maryama tayi dariar farin ciki da mamaki dk sukazo mata tace "namcy na kardai harmun samu baby? Zaaro ido tayi tace "rufamin asiri takwarah kwana nawa nayi a gdan mijin? Babu pa abnda ya shga tsakani nah dashi ko a ruwah zansha?
Maryama tsayawa tayi tana kallonta cike da mamaki, Maryam ta sadda kai lokacin taji kunyar abnda ta fada, Maryama ta dafa kafadarta tace "karki damu namcy har ynzu nice babbar qawarnan taki bzan taba daukarki a matsayin kishia ba, har yau baki da wnda zai taimaka wurin magance miki damuwarki, ki kwanta cikin farin ciki don Allah, saida safe! Murmushi maryam tayi tace "tohm namcynah!
Tana shga dakin fuskarta ba yabo ba fallasa anma daga gani cikin damuwah take, kamotah yayi ya rungume ta baya ya fara kissing din wuyanta, bata hanashi ba har tsayuwar ta fara gagarsu ya dauketa chak ya ajiye saman gado, bakinshi ya saka cikin nata yana shafo gashinta a hankali sai wani lumshe ido suke, ya saukar da hannunshi a baya yana shafata a hankali taji yana zagayowah da hannunshi, riqe hannun tayi tana qoqarin tashi ya riqeta idanunshi a lumshe cikin kasala Yace "miye hka Masoyiyah? Tace "barci, Yace "wanne barci ne daxai hanaki farantama masoyinki? Da iliminki pa Maryama! Batace komi ba ta tashi ta matsa daga inda yake tayi kwanciarta! Shma kwantawa yayi ya juya mata bata alamar yayi fushi.
Sai da 1week dinta guda ya qare babu abnda ya shga tsakaninta da deen, dk yanda yaso qiya mishi tayi yayi lallashin yayi fushin daga qarshe ce mishi tayi bzata taba yrda dashi ba sai yaa fara amsar Maryam a matsayin mata, tun daga lokacin ya daina matsa mata ya qyaleta kawai
Ranar daxai koma dakin Maryam grki na musanman sukayi dinner, bayan sun gamacin dinner suna zaune a dinning Maryama tace "nizan tafi in kwanta, Yace "ki zauna ina da magana daku, Yaa dade yana musu nasiha kafin Yace "kwana dai dayane zaku dingayi, ina fatan hkan Yaa muku! Maryama tace "Yaayi ranka shi dade, anma kafinnan naa baku sati daya, kusha amarci! Bude baki yayi zaiyi mgn, Maryama bata jira abnda zaice ba ta shgewarta daki!
Tashi yayi ya fasa cin abncin yayi shgewarshi dakinshi, Maryam ta dafe kanta ta duqe taci gaba da kuka, tana shawarar ta qyaleshi tayi tafiyarta daki ko taje ta qara bashi haquri??
Rabiatu sk mashi
[19:04, 3/23/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿
❣soyayyar whatsapp❣
@OHW
176-180
Miqewa tayi cikin rashin kuzari ta nufi dakin nashi, a hankali ta tura kofar ta shga yana kwance ya daga kanshi sama, a hankali ta qarasa inda yake ta tsuguna bakin gadon cikin raunanniyar murya ta fara bashi haquri.
Juyawa yayi ya shareta ta duqar da kanta ta shga rai rai wani sabon kukan, tausayi ta bashi sosae kukan yake ratsa mishi zuciah, filo ya dauka na nufin fita yana tsaye ta fada qirjinshi yana ci gaba da kuka, kasa daurewa yayi ya fara shafa bayanta yana lallashi, itama narkewa ta qarayi dk taa wani rikitashi, a haka lbr ya canja tsakanin Maryam da deen ba qaramin wahala tasha a hannunshi ba, daqyar ya samu barci ya dauketah!
Washe gari Maryama ita tayi musu break fast, daurewa kawai take saboda wani irin kishi dake kamata saboda lura da tayi da abnda ya faru, Maryam kuma sai daurewa take don kar Maryama ta gane, deen kuwa fuskarnan tashi sharr dga gani yana cikin farin ciki!
Suna zaune a dinning suna fira Maryama cin abnci take kawai, anma zuciarta dk baa dadi! Kirane ya shgo a wayar deen ya fiddota yana kallon Maryama, Yace "Abokinki ne, gsky bni da krki da bni kiranshi mu gaisa, Maryama tayi murmushi kawai, Ya dauka wayan, nan taga yanayinshi yaa fara canzawa, miqewa yayi yana kiran Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un tun yaushe?? Itama miqewa tayi tana kallonshi cikin firgici tace meke damun Ahmad din?? Yace "wai pa yana kwance asibiti bai lpy fiye da sati daya! Tsayawa tayi tana kallonshi hankalinta a tashe, Yace "kije ki dauko mayafi muje asibitin, Maryam ma ta nufi daki yace "keda baki lpy ina zakije?? Komawa tayi ta zauna sbd yanda takejin jikin nata kamar iska xai dauketa!!
Suna isa asibitin dakin da Ahmad yake cike da en uwanshi, kowannensu cikin damuwah wasu ma na sharar hawaye, da sauri ta qarasa inda yake idanunshi a rufe yaayi muguwar rama, wata daga cikinsu en uwanshi tace "wannan wane irin cuta ce? Rashin lpyr taashi ta yau taafi ta kullum, mutum daya bude ido saiya qara suma?
Maryama na duqe inda yake hawaye na zuba a idanunta tace "don Allah ka farka Aboki karka tafi ka barmu, danginka na cikin damuwah kowah burinshi yaga kaa tashi, don Allah karka tafi ka barmu Aboki, kukane ya qwace matah ta duqe taci gaba da kukanta
Hawayenta ne ya sauka kan goshinshi a hankali ya fara qoqarin bude ido, a kanta ya sauke idanunshi yana ganinta ya gama hannunta ya riqe tsam yana cewa "don Allah Maryama ki tsaya karki gujeni, bzan taba iya rayuwah babu ke ba, ki zauna tare dani karki qaramin nisa! Sai kuma ya koma ya qara lumshe ido!
Da sauri en uwanshi suka fita kiran likita, Yaa dade yana mishi aune-aune sannan ya dago kai yace "shocked ne ya samu, akwai abnda yakeso! Idan har bai samu ba zai ita mutuwa cikin 48hrs!
Cikin zafin rai deen ya Matso inda Maryama take yaja hannunta tana ciccijewa, Yana fadin bzan tana yrda a rabani dake ba Maryama, Maryam taa rabamu a baya anma bzan taba haqura dake a ynzu in barma wani ba!!
Godia da fatan Alkhairi ga dukkan Masoyan Maryam da Maryama...lov uh oll
Rabiatu sk msh
May

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts