```MAKASHINKA...```
11-12
©Rabiatu sk msh~
Zama tayi tana kallonshi cikin jin haushi da ƙara ƙuluwa, duk da haka bai bar dariar ba, saida yayi mai isheshi harta fara ƙosawa sannan ya tada motar suka tafi.
Yana riƙe daria yace "wai ƙanwata me kikayo ne naga kin fito da farin ciki haka? Ta harareshi kamar idonta zai faɗo tace "nicema na fito da farin cikin ko Ya Anwar? Neman aiki naje aka ɗaukeni, meya hana ka shiga ka jiyo?
Wata dariyar ya ƙarayi yace "meya haɗa likita da er sanda? Na ɗauka ma da wannan ɗan sandan daya rakoki za'ayi? Sadeey ta ƙuta, don taa lura Ya Anwar so yake zuciyarta ta fashe don haushi, ta juya kawai ta ƙyaleshi.
Saida ya shiga da ita cikin gida har hanyar shiga, sannan ta fita yana daria har lokacin bata kulashi ba ta tafi, saƙo taji ya shigo a wayarta, taja tsoki kawai don taa riga da tasan ko waye, don tsananin jin haushi anan ta jefar da ita sannan ta shiga gidan.
Can saman kujerun falo ta hango ƙawarta khadija zaune an cika mata gaba da kayan ciye ciye, nan ta manta da damuwarta saboda farin cikin ganinta da gudu ta ƙarasa inda take ta faɗa mata tana daria.
Khadija ma dariyar take ganin yanda sadeey take murnar ganinta, tace "anma dai ai kin barni in nuna miki fushin da nake dake, Allah sadeey baki da kirki" sadeey tace "naa amsa laifi na, anma wlhy khady kina raina koda yaushe"
Khadeey tace "banga alama ba, shikenan tun bayan rasuwar su daddy kika dawonan gidan Abba kin mnta da kowa, tun tafiyarki india bani cika wata ɗaya banzo gidannan nemanki ba, numbarki ma bata shiga, wlhy sadeey nayi kewarki da yawa.
"nima haka khadeey, kuma naji daɗin ganinki sosae, tashi muje ɗaki ki huta akwai labarai," suka miƙe tana riƙe da hannunta har ɗakinta ta zaunar da ita, suna tafiya khady tace "anma dai ina labarin shamsudden an ganoshi kuwa? Sadeey ta girgiza kai nan take yanayinta ya canja tace "har yau dai, ayda tunda kikazo zan baki labarin na kashe macucinnan da hannunah, sannan hankalina zai kwanta idan har na cika burina na kashe MAKASHIN iyayenah, khadeey tace "Allah dai ya bayyana wannan mugun marar Amana a yanke mishi hukunci dai dai dashi, sadeey tace "Ameen fa"
Sun shiga ɗakinta, Kamar ance ta kalla, can ta hango wayarta saman mirrow tana haske, gabanta yayi mummunar faɗuwa, jikinta sai kyarma yake, khadija tace "lafiyarki kuwa sadeey" cikin sarƙewar murya ta furta "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, khadija na shigo da waya ɗakinnan? Tace "A'ah ban ganki da ita ba"
Sadeey tace "Aljanine, Allah Aljanine khadija, tun a ƙofa na jefar da wayata kin ganta a saman mirrow, ya takurama rayuwatah, komi nake gana sane yana tare dani, duk Abinda nakeyi yaa sani," ita dai khadija duk batasan me take nufi ba, ta ƙarasa gaban madubin ta ɗauko wayar tana dubawa, buɗe saƙonnin tayi ta fara dubawa.
Na farko momie ce ta tura mata "kiyi sauri ki dawo kina da baƙuwa," sannan ta duba na biyun da ƙarfi ta karanta.
```ina yima baƙuwarmu sannu da zuwa```
~masoyi~
Khadija tace "ni banga wani abu a cikin saƙonnan ba, na momie ne dana masoyi kawai" da sauri sadeey tace "ba wani masoyi Aljanine, duk alamu sun nuna..."
Khadija ta dafa kafaɗarta tace "ki kwantar da hankalinki ki faɗamin abinda ke faruwa, kinbi kin tsorata daga anmin msg ɗin sannu da zuwa" ajiyar zuciyah kawai take, daƙyar khadija ta lallaɓata ta fara dawowa dai dai, bata matsa mata da saita faɗa mata ba ganin yanda yanayinta ya koma lokaci ɗaya.
Sadaukarwa ga sadeey s adam (kishiya)
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment