New Post

Monday, 31 October 2016

MARYAM KO MARYAMA 156-170

[10:00, 3/22/2016] Rerbee'art: [09:42, 3/22/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿
❣soyayyar whatsapp❣
@OHW
156-160
Sunzo shiga dakin maryam, caraf Maryama ta ji deen ya qanqame hannun ta juya suka tsaya cak suna kallon juna, Tana mshi kallo mai alamar tmby, Shi kuma ya langabe kai kamar qaramin yaro Yana riqe da hannun ta Yace "Masoyiyah mu je daki zamu yi mgn plz, ya qara shagwabe fuska kamn wani bby, ta langabe kai tace "Tohm anma minti biyu na bka na Maryam da Maryama, Da fuskar tausayi yace" hmm Maryam ko Maryama dai? Tace "me kace? Yaja hannunta kawai suka koma inda suka fito
Yana riqe da hannunta yana murzawa Yace "kinqi bni dama muyi magana Maryama tun kafin aurenmu, kinsan naji ciwo kuwa da muka gano gsky anma kika qi amincewa da aurenah? Cikin son abar xancen tace "nipa kana tsaidani na qagara inje inga namcyna ta fada a shagwabe
Daure fuska yayi yace "kibar maganar matanar bniso! Tace "Wace matar kake mgn? Yace "waccan mana, cikin qura mishi ido tace "Ka fada kan ka tsaye kawai kace da namcyna kake, kaa mnta alqawarin mu ko?
Yace "bn mnta b Masoyiyah, sakinta ne kawai bzanyi ba anma bzan taba bata farin ciki ba, deen naki ne ke kadai bn taba tunanin auren Matah biyu b, anma dk taa canjamun tsari, Allah bzan boye miki ba Masoyiyah ko kadan bzan iya wanke haushnta a raina ba! Sauke ajiyar zuciah tayi tace "zanji da wannan taso mu tafi!
Ganin su kawai maryam ta yi sun shigo, deen sai wani daure fuska ake bbu wani annuri, Maryama ta qarasa ta zauna kusa da maryam da ke shararar hawaye ta kamo hannuwan ta duka biyun tace "me ne na kuka namcy bakya so da mukai aure da deen ko? Da saurin ta ta gitgiza kai tace "a'ah wlh, ta qanqame hannun Maryama tace "Bn san ta ina zn fara baki hqr bne namcy bn san ya zama na a gida daya da ke a matsayin kishiya zai ksnce ba, kaico na da wannan cin amana danayi miki,
Hannu tasa tana share hawayen Maryam tace "wannan yaa riga yaa wuce namcy, ni bzan taba kallonki a matsayin kishia ba, Ki yarda da ni bana ganin laifin ki ko daya a kan Abunda Allah ne ya hukunta faruwar sa, idan ma da mai laifi a nan to kuwa ba zai wuce ni ba da har na amince na auri mijin namcy na! Ji tayi shams yaaja wani uban tsoki, Maryama ta juyo tana kallon shi cikin fuskar tausayi tana langabe kai, ta juya taci gaba da goge ma Maryam hawaye!
Juyawa deen yayi ya fita kawai, bataji dadi ba ta juya tana kallon Maryam, maryam tace "sai da safe Amarya, asubah ta gari, girgiza kai tayi cikin damuwa sannan ta shafi fuskar maryam ta juya ta tafi!!
Rabiatu sk msh
[14:12, 3/22/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿
❣soyayyar whatsapp❣
@OHW
161-165
Maryama naa shga daki taga deen na fitowa dga toilet yaa dauro alwalah, Yace "kije kiyi alwalah ina jiranki, ta daga mishi kai ta nufi toilet, dk da taaso ta qara mishi magana kan Maryam don sosae take bata tausayi.
Bayan sun qare sallar sun dade yana kwararo musu addu'o'i sannan suka shafa, Ya kalleta Yace "bnsan ynda rayuwatah zata kasance ba idan bmu tare, Murmushinki yanayin kallon da kkemin yana qaramin sonki, i dnt want to even imagine a single moment wizout uh, ina sonki Maryama! Murmushi tayi tace "nima ina sonka Masoyi!
Tashi tayi ya kamo hannunta Yace "nasan kin gaji da yawah ga hidimar biki bzata brki kici abnci ba, ki zauna zan fara aikina na ciyar dake, shagwabe fuska tayi tace "nidai na qoshi! Yace "aikam dura mikishi zanyi ynzunnan! Don Alqawari nayi bzan taba barinki da yunwah ba kinga ko bzan karya ba dga yau, murmushi tayi ta juyo ta zauna qasa suna fuskantar juna! Shi da kanshi ya ciyar da ita sukaci suka qoshi sannan suka tafi suka kwantah!
Can qarshen gado ta kwanta bayan sun kashe fitila, ya matso inda take ya juyotah suna fuskantar juna, qanqameta yayi a qirjinshi har saida tayi er qara, ya sanya harshenshi cikin bakinta ya kamo harshenta yana tsotsa kamar mai shrn cireshi, sun dade yana kissing dinta ji tayi yaa fara shafata tako ina ta riqe hannunshi, a hankali cikin kasalalliyar murya Yace "yadai? Ta kwanar da kanta a qirjinshi tace "barci Masoyi! Ya qara qanqameta yace "ki kwanta kiyi barcinki Masoyiyah!
Haka sukayi barcinsu kowanne zuciarshi cike da farin ciki, deen na qarajin soyayyar Maryama sosae yanajin kamar ya maidata jikinshi su zama Abu daya!
Maryam kuwah bayan fitarsu taa dade tana kuka kafin barci marar dadi ya dauketa, soyayyar deen ke qara shgarta ga wata irin tsanarta da take hangowah a idanunshi, ji take daman zata iya haqura dashi ta barshi suyi rayuwar farin cikinsu shida Maryama, tasan ba qaramin takura musu take ba!!
Rabiatu sk msh
[20:38, 3/22/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿
❣soyayyar whatsapp❣
@OHW
166-170
Washe gari wurin 8 Maryama ta farka bayan sunyi sallah sun koma, a hankali ta zame jikinta dga nashi ta tashi zaune ta qura mishi ido, wani irin sonshi ne ke qara shgarta lumshe ido tayi ta bude tana qara godema Allah daya bata deen a matsayin mijintah!
Miqewa tayi zata fita taji yaa ruqo hannunta, ta kwanto kan gadon suna fuskantar juna, Yace "ina zaki tafi ki brni Masoyiyah? Tace "kai dai kayi brcinki, wai ma yaushe ka tashi?? Yace "tun lokacin da kka fara kallonah! Hannu ta saka ta rufe fuska, tace "ka koma brcnka na gama! Dayan hannun nata ya kamo yana murzawa Yace "bn yrda ba, babu inda zaki tafi ki barni! Babu yanda zatayi ta koma ta kwanta sukaci gaba da brcnsu basu suka farka ba sai 11.
Ta gama shryawa cikin doguwar riga, suna tsaye da deen ya kaasa dauke idanunshi a kanta sukaji ana knockn, deen ya wani hada rai batace mishi komi ba ta qarasa ta bude qofar, Maryam ce Tace "na jiku shru ne Amarya ko bakujin yunwa ne? Murmushi tayi tace "Ynxu muke shrin fitowa da fatan kin tashi lapia, tace "lpylau Amarya! Harararta tayi cikin wasa tace "su namcy an zama uwargida, itama murmushin tayi da bai iya boye damuwarta ba ta juya ta tafi tana cewa saikun fito!
Deen ya jawota ya rungume ta baya ya dora kanshi samn wuyanta yana shaqar qamshinta muryarshi a marairaice yace "wannan matar ko ina ruwanta da tashnmu barci harda wani zuwa dan shisshigi, dago da kanta tayi tana kallonshi tace "bnfason hka deen, wanda ke sonka yaa gama mka komai a rayuwah, namcyna pa taa riga taa bka haquri, don Allah ka mnta da Abnda ya faru ka bmu damar da zamu baka farin ciki sosae nida namcyna
Taabe baki yayi alamar maganganun basu shigeshi ba, ta girgiza kai kawai tace "muje muyi break fast, Maryam na zaune naa jiransu ta taimaka mata suka zuzzuba sannan suka zauna suka faraci, deen sai satar kallonta yake har taji kunyar Maryam
Sai lokacin ta fara tunanin anya kuwa bata zaqe da yawa ba? Bai kamata ace tun ynxu taa safko taa nuna ma deen soyayyah ba! Wata zuciar tace "soyayyar da kkema deen tafi qarfin ki barma zuciarki, dafe kanta tayi saboda taa rasa tunanin da zatayi!Deen ne ya zunguretah da qafa ta dago tana murmushi taci gaba da cin abncin
Tare suka shga kitchen da Maryam da rana dk da taaso hanata anma ta dage dole sai da sukayi grki tare suna ta firarsu kaman ynda suka saba, dk da Maryam na kunyar Maryama har lokacin, itakam nuna mata take komi yaa wuce tana taso ta tambyeta yanayin zamnsu da deen anma taa rasa ta inda zata fara.
Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • MATATAH CE 56♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡             56 ©Rabiatu sk msh       ®NWA   … Read More
  • MATATAH CE 59♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              59 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More
  • MATATAH CE 58♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              58 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More
  • MATATAH CE 60♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              60 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More
  • MATATAH CE 57♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡             57 ©Rabiatu sk msh       ®NWA   … Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts