ABDUL WAHAB 24
©Rabiatu sk msh
®NWA
Ranar d'aurin aure, sadeey ta daure ta shirya tunda safe saboda yanda fatima ke fushi da ita ta'ki zuwa bikinta, taa riga mamie tafiya don bataso mutane suyi yawa bataje ba.
Doguwar hijabi ta saka da ni'kab don koda zasu had'u da Abdul ko kad'an bataso su had'a ido, harta shige gidan bata ganshi ba falon, d'akin hajia ta shiga duk cike da mutane tana ta hidima ta gaisheta ta fito, can d'akin da fatima take da 'kawayensu ta shiga.
'Dakin cike da 'kawayensu wanda suka kwana, fatima naa hangota mantawa tayi da tana fushi da ita ta taso ta rungumeta, taaji dadi sosae da zuwanta, 'kawayenta sai 'korafin bataje ba sai yau suke mata, bata da amsar da zata basu sai dai ta mantar da maganar, haka sukaci gaba da fira sai dai lokaci lokaci gabanta na fad'uwa duk taa rasa miye dalili.
'karfe biyu bayan sallar juma'a aka d'aura Auren Fatima tare da angonta kabir, gaban sadeey ne ya fadi sosae har sai data firgita, innalillahi wa inna ilaihirraji'un, ta fad'a fili kallon fatima kawai sadeey keyi ganin yanda take cikin farin ciki, dai dai lokacin kira ya shigo wayar fatima.
Cikin nishad'i ta d'auka ta amsa sallamarshi, tayi fari da ido kamar yana gabanta, tace "ina tayaka murna dear na yau kaa zama ango," dariya tayi sosae sannan tace "sosae ma kuwa," kallonta kawai sadeey keyi ba 'karamin burgeta tayi ba, sai da wata 'kawarta ta ta'bota ta dawo tunani.
Murmushi tayi sannan ta sauke ajiyar zuciya, cousin din fatima ce ta shigo ta wurin dangin hajiarsu, tace ma fatima "ga amarya fa da bata laifi," fatima tace "gani pa, ko ya ranki? Tace "hakan,
"ashe ba d'aurin aurenki bane kawai harda na yayanmu? Sadeey da fatima sukayi saurin kallonta, fatima tace "kamarya? Don itama batasan da maganar ba, zahra tace "nima naayi mamaki, yanzu naji suna maganar d'akin hajia, kuma da kunne na naji Allah daurin aure biyu akai kuma na yaya Abdul ne, ya akai baki sani ba?
Fatima tace "shine ay nake tunani, don kanta ya kwance, tace "'kila dai bakiji dakyau ba.
Sadeey kam dafe 'kirjinta tayi saboda yanda ya tsananta mata bugu, kanta ya sara yana mata azababben ciwo, kasa daure rad'ad'in da zuciyarta keyi mata tayi ta mi'ke a sanyaye ta fita daga cikin 'kawayensu.
Babu inda babu mutane gidan, saita wuce toilet din d'akin da suke kawai ta rufo, wani irin kuka ta fashe dashi na tausayin kanta, tabbas a yaune ta yardar ma kanta taa gama rasa yayanmu, duk yanda taso ta manta dashi taa kasa, shikenan wata tayi nasara a kanta taa aure mata wanda takeso.
Kuka sosae take, ciwon kanta na 'kara tsananta, duk yanda taso ta rarrashi kanta ta daina kuka taa kasa.
Dedicated to Mr. Smiles😃
❤❤Rabiatu sk msh❤❤
0 comments:
Post a Comment