[16:27, 3/18/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿
❣soyayyar whatsapp❣
@OHW📚
131-135
Jikin Maryam ya shga kyarma hnkalinta tashe ta rasa meya kamata tayi? Dagewa tayi cikin bacin rai ta tillar da wayar jikin bngo ta fada kwararratse! Mai gadinne ya dawo cikin gudu yace hajia an sakashi motar, tace "tohm ganinan, ta nufi daki cikin sauri ta dauko mayafi suka tafi asiti.
Suna zaune bayan an shga dashi emergency danginshi har sun iso kowah yayi jugum cikin tashin hnkali, sai da aka dauki lokaci sosae sannan likita ya fito su duka suka nufi inda yake, Momien deen tace "likita ya jikin dana? Meke damunshi?? Yace "karki damu hajia Munyi qoqari sosae wurin ceto rayuwarshi, ta bngarenmu dai babu matsala! Maryam tace "tohm miye matsalar likita?? Yace "rayuwarshi na cikin hadari saboda son wani abu daya qwallafawa zuciarshi! Su duka suka hada baki sukace miye wannan abn?? Likita Yace "wacece Maryama?? Momien deen tace "gatanan Maryam ce Matarshi! Yace "koma miye Maryama ce sanadin ciwon nan nashi, kuma na tabbatar yana buqatarta kusa dashi! Idanunshi biyu anma bzai iyayin komi ba zuwan Maryama kusa dashi ne kawai zai taimaka wurin dawo dashi dai dai, su duka suka matso kusa da Maryam suna cewa ta shga ta ceto rayuwar mijinta, dafe kanta tayi ta duqe wurin kanta nayi mata baraxanar tarwatsewa, so take tayi kururuwah ko zata sami sauqin zuciarta anma babu dama!!
***
Bayan azahar da kadan Maryama ta isa jahar kaduna cikin qauyensu, daqyar take tafiya tana riqe da kanta saboda wani irin matsanancin ciwo da yake mata, tana shga gdan guggo ta taso da murnarta zata tare ta sai kuma taga yanayin da take ciki, tsayawa tayi turuss tana cewa "yau ni mezan gani ni matar ibrahim? Meke faruwa dake ne maryama kamar wadda akayiwa satar farin ciki?? Shgewa tayi dakin tana cewa "gajiah ce kawai guggo, yau motar dana shgo ce muna tafiya ana zakuda mana en ciki, ga rana harta samin ciwon kai! Gwaggo tace "eyyah ki shga ki kwanta bari in samo miki magani!
Hka ta wuni kwance Abubuwah da yawa na damunta, ta rasa wanda zata tunkara ya bata shawara, tunda take qawarta daya kuma aminiyarta Maryam da wace fuska zata tunkaretah ta fada mata mijinta na sonta har yana iqirarin aurenta?? Ahmad ma da yake Abokinta ynxu saita kalle idonshi tace mijin qawarta na sonta? Da wane ido zai kalleta?? Tabbas ya kamata tasan abnyi tun kafin deen ya tashi lalata musu qawance da Maryam, Tohm meya kamata inyi? Wata zuciar tace ki amince da auren Ahmad kawai shi kadaine ya rage miki mafita, tashi tayi zaune cikin gamsuwa da shawarar da zuciarta ta bata, ta jinjina kai tace "sai inga ynda shams zai tilastamin aurenshi inhar na zama matar Ahmad, wayarta ta dauka cikin zumudi da niyyar kiran Ahmad, kiranshi ne ya shigo cikin hanzari ta dauka ta kara a kunnenta!
Rabiatu dk msh
08032133670
[17:33, 3/18/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿
❣soyayyar whatsapp❣
@OHW
136-140
Shru sukayi nadan lokaci kowanne Yana saqa abnda zai cema dan uwanshi a zuciah! Yace "Ya kke Abokiyah?? Tace "Abokiyah dai? Masoyi tana daria, Ahmad Yace "bn gane ba Maryama, kina nufin kin aminta da soyayyah ta? Maryama tace "tabbas Ahmad naa amince! Yace "zaki aure ni? Tace "qwarai ma kuwah!
Sanyayyar Ajiyar zuciah yayi cikin farin ciki Yace "bakisan iyakar farin da kka sanyani ba Abokiyah, oh masoyiyah! Su duka sukai daria yaci gaba da cewa "mutum mai sa'ah ne kawai zai iya samu kyakkyawar mace mai ilmi, mai hankali, mai natsuwa kamarki ba, nazo dunia a sa'a, sa'ar da nayi ta biyu a rayuwatah shne samunki a matsayin masoyiyah! Tace "ta farkon pa? Yace "zaboki da nayi a matsayin qawatah, ba qaramin sa'ah nayi ba!
Daria sosae Maryama tayi mai bn sha'awah cikin jin dadi lokaci guda harta manta da tana da damuwah tace "meyasa kakeso nah Ahmad? Yace "babbar mana! Kina da kyau, da zazzaqar murya, da kuma tausayi hankali da tunani, jikinki mai kyau, tafiyarki mai jan hnkali, anma wannan ba shine dalilin da yasa nake sonki ba! Tace "tohm meyasa! Yace "ina sonki ne kawai saboda inasonki!! Na qagara inga kin zama tawa abnda nake jira knan, anma bzan iya jira na wani lokaci ba saboda bzan iya rayuwah in babu ke bah!!
Cikin jin dadi tace "kai na dabnne a cikin maza Ahmad, nayi dace dana samu namijin da yake matuqar sonah! Abnda na dade ina nema knan, bnyi tunanin zanso wani namiji a duniar nan ba kaman ynda naso deen, nasoshi sosae qaddara tazo ta rabani dashi! Tace koda yake share kawai mezai sanyani tunanin deen tunda ynxu ina dakai?? Ahmad yace "ynxu fadamin nida deen wa kkafiso? Tace "bzan boye mka ba Ahmad naso deen sosae dk tsarin rayuwatah nayi tane dashi, kullum cikin mafarkin kasancewa matarshi nake, Anma ynzu babu namijin da nakeso kamarka! Yace "ngde Maryama wannan kadai ya isheni alfahri!! Cikin jin dadi cike da soyayyah sukaci gaba da firarsu
Da dare tana zaune da kwanon tuwo a gabnta, maganar deen da sukayi da Ahmad yaa dawo mata da soyayyarshi sabuwah, wayarta ce can gefe kira ke shgowa ta dauka cikin kasala ta duba taga sunan Maryam ne! Daukah tayi ta sanya a kunne kafin tayi magana Maryam ta rigah ta cikin kukah tace "ki taimakeni Maryam kizo katsina! Tace "inzo katsina kuma? Kukan me kke Maryam?? Maryam tace "shams ne...." maryama tace "shams ne me yake miki dgayin aurenku? Kici gaba da haquri kawai anma ni bzan iya zuwa katsina ba! Maryam tace "kiyi haquri Maryama taimakamun zaki! Maryama Tace "bzan iya ba takwarah, nida katsina har abadah!! Ta kashe wayarta gaba daya!!
Maryam ta sulale cikin nadama da dana sani, gashi batasan gidansu Maryama ba balle ta nemotah ta nemi gafararta da kuma taimakonta!!
Rabiatu sk msh
|
0 comments:
Post a Comment