New Post

Sunday, 23 October 2016

MAKASHINKA 21-22

```MAKASHINKA...```
           21-22

©Rabiatu sk msh

_Washe gari_

Da wuri sadeey tayi shirinta natafiya makaranta domin ta san yau babu driver,

Daddy ma haka tundda wuri ya shirya saboda yanada meeting da safen nan,

Saida ta kammala shirinta caf sannan tadauko jakarta tafito falo, nan taci karo daddy yana gyaran hularsa zaifita,  takarasa gurinsa tace "morning daddy" yajuyo yana murmushi yace "morning too doughter, kin tashi ƙalau?"

Sadeey Tace "lafia lau daddy, bari inje in gaida momie, sai  inzo in karbi  makullan motan koh?" Takarasa maganar tana kokarin barin gurin,

   Murmushi daddy yayi sannan Yace "mukullan mota!, a a bahaka mukayi dakeba, ai saikin iya mukai dake ko? Kiyi  sauri dai kije kigaidata kifito, yanzu nayi waya da saddiq za'a turo miki da driver, kuma yace wannan ne karo na ƙarshe da zai sake turo driver a gidannan,  saboda sun gaji da irin  raunata sun da kikeyi, ki kiyaye kinji sadeeyn daddynta" yakarasa maganar yana dariya,

Don haushi ko tsayawama sadeey batayi ba, cike da bacin rai  ta juya ta nufi ɗakin momienta, tana shiga dakin tarafa bubbuga kafafunta a kasa, tana kumbure2

  Momie dake zaune gefen gado tana kallonta, tasoma dariya "toh uwar ganin laifi, yau kuma waya taboki tunda safen"

  Cike dashagwaba tana yarfa hannu tace "ba daddy bane, wai za'a kara kawomin wani driver, nifa so nake abani motar nan natuka  dakaina.." takarasa maganar tare da zaunawa gurin momie,

     momie tayi murmushi tace "yanzu wannan duk shine abin bata fuska haka, nidama kinga yadda kika koma, dakika sha tokar nan kamar wata fatalwa, kiyi murmushi mana"

  Sadeey takara tsuke fuska, domin bata samo goyon bayan momie ba, tamike tsaye cike da shagwaba tace "momie harda keko kina goyon bayan kar a barni nayi tuki koh, shikenan" tana karasa maganar tanufi kofar fita,

  Momie tana dariya tana kiran sunanta amma haka tayi kunne uwar shego da Momie ko juyota batayiba tafita

  Sai bayan tafita momie tayi murmushi tace "fitinanniyar yarinya" takara yin murmushi,

Tana fita falo tatarar da daddy zaune yana jiran driver,  kusa dashi takarasa ta zauna, fuskar nan a kumbure, ganin yanayinta yasa daddy ko uffan baice da itaba, itama shiru tayi ta soke kanta kasa, cike da takaici,

Sun jira shiru shiru drivern bai zo ba, harta kusan makara gashi daddynma yana sauri, ganin hakan ya sanya daddy cewa suje ya ajiyeta makarantan gudun karta makara.

Suna fita harabar gidan  suka shiga mota daddy yayi driving sukayiwa mai gadi hon, yazo ya bude musu gate, sannan suka fita,

Lokacin Shamsuddeen ya gaji da ɓoyan jiran fitowar sadeey kamar yanda ya saba da kullum zataje makaranta saiya laɓe ya ganta sannan yake tafiya,

Yana juyawa yaji kukan motar daddy, daman ya haddace kukan motar, tsayawa yayi cak yana jiran wucewarsu,

Daddy nakawowa da motarsa ya tsaya da motarshi dai dai inda shamsuddeen yake a tunaninshi shine drivern da aka turo.

Yana ganin mota ta tsaya, idanunshi basu tsaya a ko ina ba sai fuskar sadeey, data haɗa rai ta juyar da kanta gefe ɗaya, tana zaune gefen daddynta da yake shi yake driving da kanshi.

Daddy yasauke glass ya dube shamsundeen yace "malam ya bazaka shiga ciki ba tun ɗazu muna jiranka, shine  har zaka koma?"

Shamsudden ya fara sosa ƙeya, yana mamakin maganar daddy, cikin rawar murya yasoma magana "ba..ni...ba" ganin yana inda-inda  a gurin maganar yasa daddy ya dakatar dashi dacewa "shikenan ba wani abu, yanzu dai ta riga da ta makara, nima na makara, ka shiga ciki hajia zata baka mukullin mota, saika dauketa ku wuce makarantar, sannan daddy ya juya gurin sadeey data hade rai tana kallon shamsudden, ta ganshi wani cakus dashi, ba wani shirin kirki bane a jikinsa, daddy yace "sadeeyn daddy, kifita ga driver nan, zaije ya janyo motar saiku tafi, nima sauri nake inada meeting da safen nan, danine zankaiki har makaranta yau, kisauka yana jiranki"

Da mamaki shamsuddeen ya buɗa baki zaiyi magana don baimasan me daddy ke magana akai ba, daddy yayi saurin juyo gurinsa  ya rigashi dacewa "Ka kulamin da sadeey sosae, kaine drivern farko dana ɗauka ba tare da nayi bincike a kanshi ba, kada ka bari sadeey tayi ƙorafi a kanka"

Mamaki ne ko farin ciki ya hana shamsudden magana? A zahiri da baɗini yanason aikin don daman abinda ya daɗe yana nema kenan, ga kuma kusanci dazai ƙara samu da sadeey harya bayyana mata soyayyarshi, amma zata soshi yana matsayin  drivernta kuma? Bai tsaya jiraba kawai yashige cikin gidan karbo makullan mota,

Kafin daddy ya gama lallashin sadeey ya shiga ya fito ta motar da sauri,

Yana karasowa kusa dasu, tafita daga motar daddy, sannan takarasa bakin motar da shamsudden ya janyo ta buɗe ta shiga tana kumbure kumbure, shamsudden yaja mota suka tafi.

Tana daga bayan a zaune, haushi duk ya gama cikata, yanzu da ba'a samu drivernnan ba ƙila yau daddy yasa a fara koya mata mota, kalci tayi cike dajin haushin shamsudden,  ta gyara kai, a zuci tace "zai gane kurensa, nazama drivern sadeey"
  Murmushi mugunta tayi kadan, takara gyara zamanta, sannan tadaga kafarta sama ta dora  saman seat dinda shamsudden yake driving ta baya, ta dinga yawo da ƙafarta wurin fuskarshi, kamar zata hanashi ganin tati, bai tankata ba yaci gaba da tuƙunshi, hannu ya saka da niyyar ɗauke ƙafar tata daga wurin fuskarshi.

Wata irin tsawa ta mishi "karka kuskura ka taɓamin k'afa  kamin datti, don raini ƙafata zaka taɓa?" Numfashi yaja saboda razanar da yayi, ya jinjina kai lallai aikinnan babba ne.

Tayita mishi Abubuwa kafin su isa makarantar,gate taga an buɗe mishi yana niyyar shiga da motar cikin makarantar ta fara masa mashifa "ka ajiyeni nan karka karasa dani ciki" saboda batason kawayenta suganta,
  Ko kallonta baiba yaci gaba da tukinsa,
  Takara daka mashi tsawa "kai malam magana nake maka kayimun shiru saikace wani gunki"
    bai saurareta ba har saida ya direta inda ake tsayawa da motoci sannan ya fito da sauri ya buɗe mata.

Don takaici kasa ce mishi komi tayi sai dai kallon data dinga watsa mishi, da sauri  khadija taka ƙaraso inda suke tana cewa "sai babban hajiya sadeey, wani sabon driver aka chanza kuma, gaskiya kin iya mulka direbobi"

Ta harareta cike da takaici, sannan tadan kalli shamsudden kadan, sai kuma ta juya gurin khadijat  tace "banni dashi wannan  yamafi sauran rainamin hankali, yanda ya fara kawoni yau, haka zai gama shi yau, dubeshi dan Allah.." ta dalla masa harara tare dajan tsaki, sannan taja hannu khadijat suka wuce,
  Saidai kallonta kawai yake, sai bayan ta wuce, yayi murmushi!, sannan ya koma cikin motar, yatada motar yabar makarantar,

Suna cikin tafiya kafin sukarasa class, Khadija tace "nikam sai inga dakin haƙura da wannan driver naki, koba komi ya fisu miki biyayya daga gani ba ruwanshi, gashi kyakkyawa kuma"

sadeey taja tsoki tace "kema kika kula da hakan, ni kaɗai nasan abinda na shirya mishi anjima, dan rainin hankali"

Sadaukarwa ga Sadeey S Adam (Kishia)

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts