```MAKASHINKA...```
27-28
©Rabiatu sk msh
Zuwan yayanta ya hana shamsuddeen ya fara koya mata, duk inda zataje da yayanta take zuwa kullum suna tare, har ya gama weekend ya koma Abuja inda yake aiki.
Cikin Weekdays sun fara samun shaƙuwa da Shamsuddeen, tana ɗan sakin jiki tayi fira dashi, duk da firar tasu yana gaya mata ne yanda zata sarrafa motan kafin ya fara bata da kanta.
Ranar wednesday ƙawarta hafsat ta gayyaceta partyn murnar dawowan yayanta Nigeria yaa kammala karatu, bata cikason zuwa party ba, anma yanda ƙawayensu ke labarinsa kowa yana so yaje ya saka mata sha'awar son zuwa partyn itama.
Tana yin sallar magriba ta shirya cikin ankon da zasu saka, mini-skirt ash colour da pink ɗin riga marar hannu, taayi matuƙar kyau ta tubke dogon gashinta a tsakiya, sannan ta ɗaura After dress ɗinta a sama ta yafa gyalen, taayi kyau sosae sai zuba ƙamshi take.
Fitowa tayi ta shiga ɗakin momma dake saman sallaya tana azkar, sallama ta mata sannan ta tafi riƙe da gift ɗinta a hannu, har shamsuddeen ya fiddo mota har ƙofar da zata fito yana jiranta daman haka ya saba mata.
Ya buɗe mata baya ta shiga, sannan suka tafi.
Sai da sukaje dai dai hall ɗin da za'ayi partyn, tana daga baya kafin ta fita ta ɓalle maɓallan after dress ɗin, sannan ta ajiye mayafin, ya koma daga ita sai ɗan ƙaramin sket da ƙaramar riga, ta zagayo da dogon gashinta gaba.
Ta cikin madubi shamsuddeen ke hangota, kasa rufe bakinshi yayi, a ranshi yace "Allah yayi halitta anan, kyau har ya wuce kyau" tace "tohh shamsuddeen zuwa zakayi ka dawo ko zaka jirani?
"oh! Wai kina nufin fita zaki? Ta ɗaga mishi kanta tana kallonshi duk taa haɗe gira,
"haba ranki shi daɗe" ta ƙara haɗe rai "na faɗa maka, zaka iya kirana da sadeey"
"Tohh, sa...sadeey, gani nake kamar bai dace ki shiga irin wannan wurin da shigarnan ba, bai kamata duk wani namijin da ba muhallinki ba ya kalleki da kalar shigar nan ba,"
A harzuƙe take kamar takai mishi bugu "lallai samun wurinka yayi yawa deen, yanzu don na fara maka wasa da dariya kana ganin haƙorana zaka fara rainani? Shyasa har yau kaƙi ka ƙarasa koyamin motar kenan duk inda zanje ka bini kana samin ido?
Cikin karyewar zuciya yace "Allah ya huci zuciyarki, saboda na damu dakene shiyasa nake faɗa miki gaskia, yanzu ko maƙiyina bazanso inji zaije wurin party ba, ko baki da labarin abinda ya faru dasu afnan A YINI ƊAYA? Na tabbata idan kika karanta littafinnan na (Princess Amrah da Rabiatu sk msh) zuciyarki zata nutsu ki daina zuwa wurin party.
"Tsakaninki da Allah ina kikacema su momma zakije? Ta yatsina fuska "gidansu hafsa mna zanyima yayanta sannu da zuwa, kuma ay ba ƙarya nayi ba"
Yace "wurin hafsa da yayanta zakije sadeey anma ba gidansu ba, kinga kinyima momma ƙarya kuma kin munafunceta da wannan after dress ɗin da kika saka, ki duba kiga suturar dake jikinki banbancinta da babu duk ɗaya ne, ki taya mijinki kishin kanki mana,"
"sadeey, shifa jikin mace duka al'aura ne, don me zaki buɗe jikinki ko wanne ƙazami ya kalla? Allah yayi muku daraja sadeey, anma bansan meyasa kuke saka suturun da basu dace ba, wlhy ban taɓa tunanin kina fita haka ba, kullum cikin unifoam kawai nake ganinki da yanda baki kula kowa ba ƙaramin burgeni kike ba"
A hankali ta fara jawo after dress ɗinta tana rufe jikinta, cikin lallausan lafazi shamsuddeen ya gama tunasar da ita, ba ƙaramin daɗi yaji ba ganin yanda maganganunshi sukai tasiri a ranta.
Yayi murmushi yace "yanzu a haka wlhy baki ga yanda kikai kyau ba sosae, zan jiraki ki shiga kikai gift ɗin"
Tace "A'ah nifa na fasa shiga wurin partyn nan, bama kamar da bada iznin momma zanje ba, don labarin Arewa stars daka bani ba ƙaramin firgitani yayi ba, wannan ne na farko daman, shima Allah ya yafemin," yace "Ameen sadeey, muje ko? Ta ɗaga mishi kai tana murmushi.
Yaja mota suka nufi hanyar gida, wurin 9:45
Sadaukarwa ga Sadeey S Adam (kishia) ina fatan ko a ina kike kina cikin ƙoshin lafiya, fatan Alkhairi a gareki.
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment