New Post

Sunday, 23 October 2016

MAKASHINKA 3-4

```MAKASHINKA...```
          3-4

©Rabiatu sk msh~

Momie ta kalle ta tace "lafiyarki kuwa? Sadeey Tace "lafia lau momie me kika gani? Momie tace "dukkin fita hayyacinki da alamun damuwa a tattare dake, kinma kasa sakewa da ɗan uwan naki,!

Tace "A'ah momie gajia ce ga zamam jirgi kuma," Abbah yace "hakane, kai Anwar kaje ka rakata ɗaki, tayi wanka ta huta, anma karki daɗe ki fito kici abinci.

Tace "tohm shknan Abba," kafinma ya ƙarasa magana har tayi gaba Anwar yaa bita a baya, yana ƙara nuna mata yanda gidan yake, don ita mamaki ne ma ya kamata duk ina Abba ya samu kuɗin gina wannan gidan?

Ƙofar ɗakinda aka gyara mata ya buɗe mata, a hankali ta tura ta shiga, gaskiya ɗakin yaa haɗu sosai, babu abinda babu a ciki na buƙatar budurwa, ciki da falo ne, an ƙawatashi da haɗaɗɗun kujeru, da kuma saitin gado mai kyau da tsada, ɗakin yaa burgeta sosae, duk da baikai nata na gida kyau da tsadaddun kaya ba.

Wardrobe ya buɗe mata yana nuna mata kayan da aka tana dar mata, kallonsu kawai take, duk kusanma ƙananan kayane, da kuma dogayen riguna, sai ƴan tsirarun kayanmu na hausawa.

Saman gadon ya kwanta ya ɗaga kanshi sama, kallonshi ta tsayayi tana son tace ya ɗan bata wuri anma batasan yanda zata faɗa mishi ba, ya juyo inda take yace "ba wanka zakiyi ba? Komai akwai a cikin toilet ɗin, kiyi sauri ina jiranki in tayaki fira.

Buɗa wardrobe ɗin tayi ta zaƙulo wasu kaya bata tsaya ma ta duba kowanne bane ta shige toilet ɗin.

Saida ta shirya tsaf sannan ta fito, daƙyar take tafiya saboda yanda kayan suka matseta sosae, kuma ita ba wata mai ƙiba ba, riga da siket ne na atamfa, sai ƙaton ɗan kwali data yafa saboda yanda ƙirjinta ya matse kamar tayi numfashi rigarta tsage.

Har lokacin yana kwance saman gadon yana kallon toilet ɗin, tana fitowa yace "wow! Kinga yanda kikayi kyau,? Anma dai cire ɗan kwalinnan naki zaki, waye barenki (wanda ba ɗan uwa ba) a gidan,?

Tace "kayanne sun matse da yawa ya Anwar, sai nakai anmin ƙari," Yace "wannan dai shine dai dai jikinki, ki cire kallabinnan da kika yafa ko in cire miki shi.

Tace "yaya...! Yayi daria ya rufe bakinshi, sannan ta ƙarasa gaban madubi, tayi ɗaurin kallabinta mai kyau, tsayawa tayi tana kallon kanta cikin madubin saboda yanda tayi kyau sosae.

Cikin madubin ta hango kamar tsayuwar mutum yana kallonta da sauri ta juyo, bataga kowa ba sai Anwar da har lokacin yake kwance saman gado yana latsa waya.

Da sauri ta ƙara maida kallonta ga madubin, bata ga kowa ba, ganin Anwar ne a ɗakin kawai ya hanata ƙwalla ihu, anma iyakar tsorata taa tsorata sai kyarma jikinta yake.

"text ya shigo a wayarki," jinshi dai dai inda take, tsoro bai barta ta ƙarasa tantance muryarshi ba, ya sanyata zabura tayi hanyar fita da gudu, yana kiranta anma taƙi tsayawa, a ƙofar ɗakin nata ta wuce Abba da momie suna laɓe, bata kula dasu bama ta wuce ƙasa tana ƙwala musu kira.

Yana fitowa duk suka matso inda yake suna tambayarshi ya akai? Cikin takaici yace "nima ban sani ba, kawai tsorata tayi, Allah Abba kuna da matsala, yanzu sai kun wani biyomu kuna laɓe?

Momie ta fara wallahi tallahi bai ko saurareta ba yayi ƙasa, suka rufa mishi baya, tana ganinsu ta koma bayan Abba ta ɓoye, tana maida numfashi sai shessheƙa take tace "Ya Anwar ka ganshi? Abba akwai mutum, Allah akwai wani mutum dake cikin ɗakin can.

Momie ta jawota ta rungume tace "kamar ya da akwai mutum ina kika ganshi? Ta haɗiye miyau daƙyar tace "a cikin mirrow kuma harya miƙomin waya yace anyomin text.

Anwar yaja tsaki, yace "nine fa na miƙo miki waya anyo miki text ba wani ba, gata a hannuna haka kawai kin tada mana hankali da guntun tsoranki," ya miƙa mata wayarta kamar karta amsa, har lokacin jikinta rawa yake daƙyar ta fito daga jikin momie ta koma saman kujera ta zauna riƙe da wayarta a hannu.

Kasa buɗe saƙon tayi, sai dai ta ƙura ma wayar ido, wayar taga tana latsa kanta, ba tare data taɓata ba, ta shiga ma'ajiyar saƙonni da kanta, saƙonni guda biyu.

```bazanso wani ya dinga ganemin surar jikinki a haka ba, ina matuƙar kishinki```
                     ~masoyi~

```na faɗa miki ki daina tsorata dani, don Allah masoyiya, bani da burin tsoratar dake```
                      ~masoyi~

Wani abu ta haɗiya daƙyar, sannan ta ɗago kanta, duk ita suke kallo, a hankali Abba ya fara magana, "na rasa ta yanda zan sama miki kwanciyar hankali sadeey, na lura daɗewarki a ƙasar waje, bai hanaki daga dawowarki kin fara tunawa da mahaifanki ba, ko kina nufin har yanzu kina nan da soyayyar SHAMSUDDEEN?

Hawaye ne suka fara kwararo mata, kuka ya ƙwace mata taci gaba da girgiza kai da ƙarfi, "tabbas naso shamsuddeen Abba, naayi mishi halacci sosae a rayuwarnan, anma dame ya sakamin? Ya zama MAKASHIN iyayena, da kuma ɗan uwana da maka shaƙu sosae, naso ace na ganshi kafin ya gudu, da hannuna zan kasheshi, in ɗauki fansar iyayena daya kashe, tabbas daman hausawa sunce MAKASHINKA yananan tare dakai, ni kaɗai na rage mishi, ƙara ya kasheni nima na huta.

Momie da Abba suka haɗa ido, shima idonshi ya kawo ƙwalla,  yace "tabbas maganarki hakanne, yaronnan yayi mana bazata, yayi mana abinda bamu taɓa tunani ba, yaa rabani da ɗan uwana da matarshi da kuma ɗanshi, bayan daya gama mishi duk wani gata a duniya fiye da ɗan daya haifa a cikinshi....

Miƙewa tayi zata koma ɗakinta, momie tace "abincin fa? Tace "zanci anjima," sannan ta wuce duk suna zauna sukai jugum, kamar yau ne akai mutuwar.

Abba yace da Anwar yana kallonshi, "saura ka dawo mata da farin cikinta, ta manta da komai, kuma ta fara sonka.

Sadaukarwa ga Sadeey S Adam (kishiya)

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • HAFSATUL KIRAM 9-11[10:50, 4/11/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                        &n… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 13-14[15:24, 4/13/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                        &n… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 12🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                           🎄   &… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 16-17[13:35, 4/14/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                        &n… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 13-14[15:24, 4/13/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                        &n… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts