New Post

Monday, 31 October 2016

MARYAM KO MARYAMA 41-60

Rabiatu sk novels
[11:59, 3/11/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿
❣soyayyar whatsapp❣
@OHW
41-50
Washe gari yaa kama ranar monday, suka shrya maryam da maryama suka fito zasu tafi school, Maryam da mukullin motah a hannunta Maryama ta kalleta tace "Yau wazaiyi driving dinne? Maryam tace ke mana tana miqa mata mukullin, damn hka maryama takeso ta bude motan tana cewa "wato ke ki zauna ki huta ni kuma ki barni da drivin, Maryam tace "yi haquri qawah gobe ni sai inyi...
Sun jera sun taho da yake Maryama akwai farin jinin mutane kowah ta gani wanda ta sani saita daga musu hannu, wasu qawayen nata kuwa suna dan tsayawa su gaisa, Maryam taja hannunta tace "nasan hali damn shyasa nace mu taho da wuri, ba don hka ba nasan bzamu samu lecture safennan ba, Abokinta Ahmad ta hango ta kalli Maryam tace "shima Ahmad din bzaki barni mu gaisa ba? Maryam tace "muje anma 10mnt na baki, tana daria maryama tace "an gama ranki shi dade
A hankali cikin sanda ta qarasa inda yake sannan ta saki qara dai dai kunnanshi, sosae yaa tsorata cikin zafin rai ya jiyo suna hada ido yaga itace ya saki murmushin jin dadi yace "kin sanme Abokia? Wlhy tunaninki kawai nakeyi, tace "ba waninan ka rasa abnyi dai kake zaune hkanan, ni gaurancinnan naka yaa isheni hkanan qara in samar mka mashinshinia, Yace "inkin tashi saiki hada da knki don naaga kema ba mashinshinin gareki ba, Maryam ta rigata mgn tace "injiwa ya fada mka? An samu gwarzon daya sace zuciar Maryama, dk ruwan idonta dai deen yaayi nasara!
Tunda ta fara mgn Ahmad shru yayi kamar wanda wuta ta dauke mawa! Sai da Maryama ta kada mishi hannu sannan yayi firgigit ya dawo tunaninshi, Tace "yadai? Yace "Abokiah na rasa rashin sa'ar da naxo da ita duniarnan, naa kasa samun macen da zata soni, dk budurwar da nayi qoqarin inso tohm a makare nake zuwa sai in iske wani yaa rigani..
Yana rufe baki text ya shgo a wayarshi, Maryama taa rigashi kai hannu ta dauka budewa tayi ta fara karantawa da qarfi, "shin so zai iya zama laifi Ahmad? Nayi zatan wanda yace yana sonka ba abn gudu bne a wurinka! Miye na rasa da bzaka iya mallakamin soyayyarka ba??
Maryam daria suka bata, Maryama kuwa dago kanta tayi tana murmushi tace wannan ma dk cikin rashin sa'ar soyayyar ne? Yace "nipa Abokia har yau mace daya kawai nakeso, kuma naa rasa ta, Tace "tohm kaci gaba da zama hkanan har mu gaji mu bada kai sadaka, su duka sukai daria, hka sukaci gaba da firarsu su uku har lokacin shgarsu lecture yayi
Rabiatu sk msh
[13:29, 3/11/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿
❣soyayyar whatsapp❣
@OHW
51-60
Akan hanyarsu ta komawah ne suna sauraren waqar "complicated" ta rihanna Maryam sai bi take, Maryama tasa hannu ta kashe tace "ni waqarnan taa isheni, qara muyi shru in bzaki saka mna karatun qur'ani ba, Maryam tace kin kyautah damn da maganar da nakeso in miki, tace "inajinki ba tare da taa juyo ba, tana qara maida hnkalinta wurin drivin
Maryam tace "ni namcy gani nake kamar Ahmad sonki yake! Kafin ta rufe baki Maryama taa fara daria harda hawaye, ta bata rai tace "me akai kuma na daria, sai da Maryama tayi mai isarta sannan tace "kema takwarah da abn daria kke, wannan yaron ya za'ay muyi soyayyah dashi, bzai wuce 4yrs ya bni bpa, da yake taa riga taa gama ba Maryam haushi don ita bata ga abn daria ba, juyawarta tayi ta qyaleta
Gefe daya kuma Maryam haushin yanda Maryama ta fita samari take, da kuma yanda ta fita kyau nesa ba kusa ba, tunani take anya in sukaci gaba da jerawa da Maryama zata samu saurayi?? Gaa deen din da kullum take lbrnshi, ji take damn ita ta samu kamarshi, batasan sunzo gida ba har Maryama ta gama parking sannan ta tabotah
Suna shiga falon fiddausi ta rugo da gudu tana musu oyoyo ta fada jikin Maryama, dagata tayi sama daqyar tana nishi tace "kai little sis gsky kin fara nauyi, Tace "wai hka balah driver yacemin dazu da zamu ckul wai na zama 'bulelia, da naji haushi kam na samu tooth pick nayi ta tsira mishi a wuya yana hka, ta nuna matah ynda mutum keyi in an mishi cakulkulo, daria sosae Maryama take tace "in kkaja muku ya fada daku wani wurin pa?? Maryam ta kalla taga ko itama dariar take? Tsoki tajaa ta nufi dakinsu, a sanyaye Maryama ta ajiye fiddausi tabi Maryam dakin, don tunda take da maryama basu taba fada ba ko cikin wasa ne, qaunar juna ne kawai tsakaninsu!!
Sanda ta shga Maryam har taayi shrin wanka, bata kalli ko inda take ba ta fada toilet, Maryama ta kwanta kan gado tana jiran fitowar Maryam, koda ta fito doguwar rigah kawai ta saka saboda zafin da ake ta nufi hanyar fita, Maryama tasha gabnta tace "wai mike damunki ne takwarah? Kiyi haquri don Allah bn dauka zan bata miki rai bne! Anma tsakaninah da Ahmad Abotah ne kawai ba mgnr soyayyah! Murmushi yaqe tayi don batason Maryama ta gane tana mata hassada, kuma tanason Maryama sosae batason abnda zai kawo musu rashn fahimta a qawancensu! Dafa qafadar Maryama tayi tace "shikenan namcy, nima kawai bnji dadi bne anma ya za'ay inyi fushi dake? Dariar takice taban haushi! Daria Maryama ta qarayi sannan tace "shikenan muje muci abnci ko? Maryam din tayi daria tace "eeh tunda naa huce
Ina fatan dai masu karatu na gane banbanci Maryam da maryama!!
Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • ABDUL WAHAB 39ABDUL WAHAB 39 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Tafiya kawai take tana jefa ƙafarta harta fito daga gidan, batasanma unguwar ba ta tsaya tana kallon hanyar da zatabi t… Read More
  • ABDUL WAHAB 38ABDUL WAHAB 38 ©Rabiatu sk msh            ®NWA Tun daga ranar ta koma rufe 'kofarta da makulli ta barshi a jiki, bata fitowa ko falon d'akinta sai Abdul bainan, ta k… Read More
  • ABDUL WAHAB 40ABDUL WAHAB 40 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Ɗaga mata gira yayi yana murmushi, tare da fatima da raheem suka haɗa baki sukace "April fool", baki sake da mamak… Read More
  • MAKASHINKA 1-2```MAKASHINKA...```              1-2 ©Rabiatu sk msh~ Wannan littafin sadaukarwa ne ga ```Sadeey S Adam``` (Kishiya), ban yarda wani ko wata ya canjamin wani a… Read More
  • MAKASHINKA 3-4```MAKASHINKA...```           3-4 ©Rabiatu sk msh~ Momie ta kalle ta tace "lafiyarki kuwa? Sadeey Tace "lafia lau momie me kika gani? Momie tace "dukkin fita hayyacinki da ala… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts

 
tha