ABDUL WAHAB 14
©Rabiatu sk msh
®NWA
Yana Shiga bedrum d'insa ya tura k'ofar yasa Mata key
bai samu damar zura sleeping dress ba hka ya fad'a kan tafkeken gadonsa cike da tunanin khadijansa
yana jiran kiranta a ko wane lkci dan hka wayar na gefensa duk bayan mintuna saiya duba ya gani kodai a silent ya Sakata?
gaskiya idan kahadija ta amince da soyayyarsa baiga wata 'ya mace da xai so bayanta ba duk da Yana tausayin Sadeey to amma yarinyar ta cika surutu ga rawar Kai
ita ko irin alkunyar Nan ma bata nuna wa sai surutu kamar bishiyar kanya na xuba...
khadija kuwa akwai alkunya ga bata da yawan surutu duk maganar da xata fito daga bakinta to mai ma'ana ce.
A haka dai bacci yayi awon gaba dashi ba tare da yaji muryar abin alfaharinsa
******
Tana zaune a parlour tana kallo amma bata fahimtar komai Kawai tunanin Abdul d'inta take
ji take babu macen da ta fita sa'a dayin dacen masoyi na hak'ik'a
Murmushi take tayi kamar tana ganin Abdul d'in,ita tunaninta idan ta Kira shi a waya tayaya zata furta masa cewa ta amince da soyayyarsa???
Hannu tasa ta rufe fuska sbda kunyar abinda bakinta zai furta
Ta d'auki wayarta ta Shiga contact ta duba number sa da tayi saving da my Abdul....!
tayi saurin gogewa ta Maida my luvly....!
tayi murmushi ta furta "my luvly" ta sake yin wani murmushin sannan tace "to wane sunane latest Wanda yafi my luvly dad'i"? ta tambayi kanta.
tayi saurin goge sunan cikin smiling najin dad'i ta Maida sunan My Soulmate......!
Tayi ta fad'in sunan a cikin zuciyarta tana kuma fatan Allah yasa Abdul ya zama soulmate d'in nata
Nasan ynxu Yana jiran kirana a ko wane lkci amma gskya inajin kunyar furta masa, to ya xanyi???
Wata zuciyar tace to me xai Hana kiyi masa text?
Hakan kuwa akayi dan a lkcin ta d'auki wayar ta Shiga sms ta rubuta masa text kamar hka
"Ur request has been
Accepted
U can't control wat
life throws on u,
at first i thought a
day will never come
4 me to live wit u.
I luv u too My Abdul".
Tsowon mintuna tana karanta text d'in ta kasa yi masa sending,saida ta karanta yafi a k'irga sannan ta tura masa tana ganin ya Shiga tayi saurin kashe wayarta dan tasan xai kirata kuma tanajin kunyar d'agawa a ynxu
Yana Zaune akan dining suna lunch
Sai d'iba yake kad'an2 dankuwa Yana cikin damuwa Yau har kwana biyu khadija bata kirasa ba to ko bata sonsa ne..
A haka suka kammala cin abinci suka koma parlour kamar yadda suka Saba Sadeey ce ke ta xuba surutu Fatima ta biye Mata, shima Yana d'an Shiga hirar tasu jefi jefi.....!
K'arar wayarsa yaji da alama text ne ya shigo,ya d'an jaa tsoki sannan ya ciro wayar,ynxu hka ma ba wani important txt bane
new number daya gani ne yasa shi saurin bud'awa
aikam txt d'in khadija ya gani,yayi saurin kallon Fatima itama ta gane me ya gani,tayi saurin kanne ido d'aya alamun yayi controllng Kansa kar Sadeey ta gane
Da sauri ya mik'e ya fice Sadeey kuwa tayi saurin cewa "yayanmu ina xakaje muna hira"?
ko juyowa baiyi ba bare ta samu damar da xai bata amsa.
Dedicated to Mr. Smiles😃
❤❤Rabiatu sk msh❤❤
0 comments:
Post a Comment