ABDUL WAHAB 28
©Rabiatu sk msh
®NWA
Ta durqushe a wurin tana kuka ita kam duk da tana son Abdul bazata iya zama dashi ba don ba ita yakeso ba yana daiso ya raina mata hankaline a tunaninta
Shima yana shiga dakinsa ya fada kan gado ya rasa ya xai bullowa Sadeey, soyayyarta sai dada ninkuwa take a cikin xuciyarsa. Ya rasa yadda xaiyi, barci ma qaura yayi daga idanunsa hakan yasa ya miqe ya shiga toilet ya dauro alwalla ya fito ya dinga sallar nafila yana Addu'ar Allah ya karkato masa da hankalin matarsa.
Ita ma kasa barci tayi hakan yasa ta fada toilet tayi wanka tare da alwala ta fito tana ta yin nafilfili har kusan asuba barci barawo ya saceta a nan kan sallayar. Shi kuwa sai da akayi kiran farko sannan yayi raka'a tanul fajr da aka yi kira na biyu ya fito don xuwa masallaci, bai shiga dakinta ba ya wuce masallaci. Ana idar da sallah ya shigo gidan ya xarce dakinta yana shiga har lokacin tana kwance kan sallayar tana barci. A hnkl ya shiga tada ta yana kiran sunanta a hankali.
Cikin natsuwa ta bude idonta ta sauke su akan nasa, da sauri ta miqe tare da daure fuska ta shige toilet don yin alwalla. Kodata fito bata iske shi a dakin ba, ta tabe baki ta kabbara sallarta don ita har lokacin haushin shi take ji.
Dakinsa ya koma ya kwanta kan gado don barci yake ji sosai. Ai kuwa bai dade da kwanciya ba barci yayi awon gaba dashi. Ita kuwa bata koma barcin ba sakamakon wata addababbiyar yunwa da ta isheta. Hakan yasa ta fito ta shiga kitchen don duba abinda xata ci. Ta bude fridge taga leda ta dauko ta bude taga nama ne a ciki na kaxa mai rai da lpy. Nan t shiga kitchen ta dumama ta sannan ta diba a plate ta dauko Lemu ta koma dakinta.
❤❤Rabiatu sk msh❤❤
0 comments:
Post a Comment