New Post

Saturday, 29 October 2016

MAKASHINKA 53-54

```MAKASHINKA...```
           53-54

©Rabiatu sk msh

www.babymsh.blogspot.com

Yaci gaba da cewa...
Sai dai ganin Abba nayi yaa zare wuƙar dake jikin shaheed ya chaka ma daddy,  ya zare zai ƙara chaka mishi na riƙe hannun nashi ya tillar dani wuri guda, munsha faɗa sosae da mutanenshi har wani yayi nasarar chakamin nima wuƙar, saboda tsananin azaba kasa yin komi nayi, suka rirriƙeni ina kallo suka kashe daddy da momma sadeey akan idona na kasayin komi"

Suka dawo kaina zasu ƙarasa kasheni sadeey banda sauran zaɓin daya wuce guduwa, daƙyar na tsere musu anma da tunanin sun kasheni saboda mugun raunin da sukai min, hakanne ma ya bawa Abba ƙwarin gwiwan saka police nemana," ya saukar da ajiyar zuciyah yana kallon sadeey da hawaye ne kawai ke zuba a idanunta jikinta duk sunyi sanyi, hannunta ya saki batasan sanda ta saki wuƙar ta faɗi ba, ta rungume shamsuddeen.

Cikin kuka take cewa "naa zargeka Yaa deen, na manta duk soyayyar dake tsakaninmu da yardar da mukai da juna, na tilasta ma kaina tsanarka, kayi haƙuri ka yafemin, don Allah kayi haƙuri Yaa deen" shafar kanta yake yana hawaye Yace "bazaki iya tsanata ba sadeey saboda soyayyar gaskia muke ma juna, na kasa ceton Daddy da momma ki yafemin, mu duka munyi kuskure.

Tace "Ya isa hakanan Shamsuddeen, muje mukai ƙararsu a kotu, mu faɗa ma police komi su suka kashemin iyayena" Yace "wacce hujja garemu sadeey? Su fa ba irin mutane bane, suna da ƙarfi da iko ga kuma kuɗi sadeey, bazamu iya jayayya dasu ba zasu kashemu ne"

Tace "kenan me zakayi? Yace "Abba da momie kawai suka ragemin sadeey, domin itama da saka hannunta a ciki, kamar yanda suka kashe iyayenki bada sanin kowa ba haka nima zan kashesu, wannan ɓacewar da kika ga inayi wani mutum ne dana taimaka mawa ya bani sirrin", ya zaro wani abu ya nuna mata yana mata bayanin yanda ake amfani dashi duk bata gamsu ba dai.

Tace "kar kayi haka Ya deen, kabar hukuma tayi aikinta" Yace "hukuma babu Abinda zata iyayi sadeey" tace "karka kashesu ya deen kaima doka zata iya hawa kanka" yace "na gama yanke shawara sadeey" tace "zamuyi tunanin wata mafitar anma ba wannan hanyar ba.

Yace "anma kwana biyu na baki, kiyi tunanin yanda zamuyi" tace "na yarda" sannan Yace taje gida kar ayita nemanta shru, ba don taaso ba ta tafi ta barshi anan ta shige cikin gida.

Aikam Abba ya saka momie a gaba yanata yi mata faɗan tabar sadeey ta fita gashinan ba'a ganta ba, ƙilama makashinnan ne shamsuddeen ya ɗauketa, sai gashi taayi sallama ta shigo, Abba da momie duk suka tsaya suna kallonta ganin fuskarta tayi kumburi alamar tasha kuka.

Su duka haushinsu takeji, kamar tayi kururuwa mutane su taru ta faɗa musu Abinda momie da Abba suka mata sannan su tayata kashesu, Anma kamar yanda shamsuddeen yace shiru yafi kamata suyi har a samo mafita.

Abba yace "daga ina kike? Wani takaici yazo mata iya wuya, daƙyar ta iya cewa "garden" ya fara "ki daina nisa da momienki sadeey, na faɗa miki ki cire damuwa a ranki....." bata tsaya saurarenshi ba, bazata kuma iya ɓoye tsanarshi data ɗarsu a zuciyarta ba, ta kaɗa kai kawai ta wuce ɗakinta.

Abba cikin tsarguwa yace ma momie, ina zargin fa yarinyar nan taa fara lura da abinda muke ciki, ki ƙara saka ido a kanta banso yaronnan ya samu damar dazai faɗa mata komi," momie tace "insha Allah Alhaji, ina zan bari asirinmu ya tonu? Yace "ke kika sani dai"

Sadeey ta shiga ɗakinta da tunani kala kala, duk dai bai wuce na yanda zata ɗauki fansar iyayenta da Abba yayima kisan wulaƙanci bane, hawayenma ta nema ta rasa sai dai wutar ɗaukar fansar ɗake huruwa a ƙirjinta.

Sadaukarwa ga sadeey s adam

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts