ABDUL WAHAB 6
©Rabiatu sk msh~
®NWA
Tunda suka fito sadeey bakinta bai qarayin shiru ba, sai yaba kwalliyan Abdul d'inta take, hotuna kam taayi mishi ba adadi duk da ba tsayawa yake ba, shiga sukai sukama hajiya sallama, Allah ya kiyaye hanya ta musu tare da gargad'in karsu dad'e
Raheem ne ke driving shida fatima a gaba, Abdul da sadeeynshi a baya, ta dasa da surutun nata, data isheshi gashi marar son hayaniya wayarshi ya ciro yaasan abnda ta fiso kenan watau selfie, ya dinga musu har suka isa wurin partyn! Sannan ya samu tayi shiru.
Raheem nayin parking duk suka fito anma bnda abdul, har lokacin ba'a fara ba! Sadeey bata jira kowah ba tayi gaba wurin qawayensu, duk inda ta wuce saita tsaya sun gaisa tana nuno musu inda Abdul yake duk da bai fito ba, fatyma daman tuni sun tafi ita da Raheem da yaga Abdul baida niyyar shiga hall d'in yace "qanwatah muje kimin budurwa cikin qawayen naki!
Zuga guda ta kwaso ta qawayenta ta taho, suna tafiya tana basu labari fuskarta kawai zaka kalla ka gane cikin farin ciki take, yana hangosu ya dafe kanshi, shi Al'amarin sadeey har yau yaa'ki daina bashi mamaki, shi ba mai son magana ba, idan sunzo kome zaice musu? Lalla'bawa yayi ya fice yana neman wurin 'boyo cikin hotel din yana tafiya cikin sauri saboda yaaji sadeey taa taho nemanshi.
Karo ya kusan kai mata cikin duhu tana waya, da sauri ya matsa ta juyo tana kallonshi har suna had'a baki yace "kece? Ta juya idanunta sannan tace "wani abu? Kafin yayi magana yaajiyo sadeey na tahowa tana kiran Yayanmu, Yayanmu, Yayanmu...
Da sauri ya fara waige waige, wuri ya samu ya la'be yana maida numfashi, khadija kam dariya ya bata sosae a ranta tace ko 'boyon me yake? A haka har sadeey ta iso wurin tana dube dube ta kalleta tace "don Allah khady kinga yayanah? Wani fari kyakkyawa hka, yana sanye da skye blue din kaya, yana da saje mai kyau da baqin gashi kwantacce, zaki ganshi yana tafiya cikin nutsuwa mai kyau da tsari...
Tana magana anma khadija kallonta kawai take yanda take bayyano suffofinshi, Gaskia ne sadeey ta fad'a Abdul yaa had'u iyakar haduwa, Matsalarshi guda rashin fara'a, ita bata tsaya bama ta kula da had'uwarshi ba sai ynzu da sadeey ke mata magana.
Saida sadeey ta ta'bota ta sauke ajiyar zuciyah, yarfar da hannu tayi tace "baki ganshi ba? Girgiza mata kai kawai khady tayi
Juyawa sadeey tayi zata tafi wayar Abdul ta fara ringing ta jiyo da sauri ta dawo
Dedicated to Mr. Smiles😃
❤❤Rabiatu sk msh❤❤
0 comments:
Post a Comment