New Post

Sunday, 16 October 2016

ABDUL WAHAB 3

ABDUL WAHAB 3

©Rabiatu sk msh~
          ®NWA

Sadeey na shiga ta iske barci yake, ta 'bata rai kamar ta tadashi kuma saita fasata d'auki magenta ta fita falo ta zauna hrda kunna kallo.

Yana jin fitarta ya 'bude ido had'e da saki sanyayyar ajiyar zuciah, fuskar khadija ce ke dawo mishi kamar ynzu ne ya had'u da ita, zazzaqar muryarta ce ke mishi yawo a qwalwa, bai ankara ba ya lula duniyar tunaninta.

Sai da ya farga, sannan yaja dogon tsoki shi a dole sai yaji haushinta, yabi bango da harara kamar tana kallonshi, sannan ya miqe ya shiga toilet yayi wanka tare da brush sannan ya fito.

Sai da ya shirya tsaf cikin qananan kayan da suka anshi jikinshi yayi kyau sosae kwantaccen gashin kanshi sai sheqi yake, a falo yaja burki yana kallonta cikin mamaki.

Miqewa tayi tana murmushi ta qaraso inda yake, ya had'e rai ko kula batayi ba tace "sannu da fitowa yayanmu! Abdul bai bata amsa ba cikin shan mur yace "me kikeyi anan? Ta nuna mishi t.v da hannu tace "kallo nake! Yace "kallo? Tace "eeh, sai nayi break fast kuma? Yace "a dakina kuma?

Ta rausayar dakai tace "tohm wake gyarawa idan bani ba? Nazo in tashe ka ne naga kana barci! Zai sake magana kuma ya fasa saboda wani 'bacin ran daya taso mishi, sudai mata ko a ina haka suke da hawan kai!

Har yaakai 'kofa zai fito ta 'kwala mishi kira, ya tsaya da saurinta ta qarasa inda yake, ta marairece fuska tace "ni yayanmu sai wani shamin murr kake badai takura maka nake ba ko? Da'kar ya iya d'aga kai yana murmushin ya'ke, tace "anjima nida fatyma zamuje birthday partyn qawarmu, zaka kaimu? Ta qara narkar da murya jin yayi shru tace "don Allah" girgiza mata kai kawai yayi ganin tana niyyar makarar dashi!

Matsowa tayi dab dashi ta d'an dafa kafad'arshi yace "ke miye haka? Tace "mepa? Ni ba er uwarka bace? Donna ta'baka miye? Tana niyyar qara matsowa yace "shikenan naji ku shrya kawai," bai jiya me zatace ba ya fita ya barta tana murna don daman taa dad'e tanason ta gabatar dashi a abokanta saboda yanda take fad'a musu had'uwarshi, tasan kowacce zatayi fatan samunshi a matsayin miji!!

My facebook page: Rabiatu sk novels

Dedicated to Mr. Smiles😃

❤❤Rabiatu sk msh❤❤

Related Posts:

  • MARYAM KO MARYAMA 156-170[10:00, 3/22/2016] Rerbee'art: [09:42, 3/22/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣soyayyar whatsapp❣ @OHW 156-160 Sunzo shiga dakin maryam, caraf Maryama ta ji deen ya qanqame hannun ta juya suk… Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 171-180[17:49, 3/23/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣soyayyar whatsapp❣ @OHW 171-175 Da dare suna zaune suna fira da Maryam taaje yi mata sai da safe, Maryama tace "namcy kin wani shgo kin kwanta … Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 191-200[15:32, 3/24/2016] Rerbee'art sk: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣soyayyar whatsapp❣ @OHW 191-195 Ranar aka daura auren Maryama da Ahmad, tana zaune ta qura mishi ido ko qiftawa batayi tama rasa mezatayi, d… Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 191-100[15:32, 3/24/2016] Rerbee'art sk: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣soyayyar whatsapp❣ @OHW 191-195 Ranar aka daura auren Maryama da Ahmad, tana zaune ta qura mishi ido ko qiftawa batayi tama rasa mezatayi, d… Read More
  • A YINI ƊAYA 1-2[11:20pm, 19/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀     💀💀           💀💀  … Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts