New Post

Sunday, 16 October 2016

ABDUL WAHAB 26

ABDUL WAHAB 26

©Rabiatu sk msh
          ®NWA

A firgice ta farka, tana fad'in innalillahi wa inna ilaihir raji'un, du'kar da kanta tayi yaa daina mata ciwo, fara tariyo duk abinda ya faru a ranar tayi, sai kuma ta 'dago kanta da sauri tana 'kare ma d'akin kallo, ta saukesu akan Abdul dake zaune gefen gado yaa zuba mata ido.

Da sauri taja baya kamar wacce taga abin tsoro, ya sakar mata murmushi yace "barkanki da tashi," batasanma sanda ta sakar mishi harara ba, cikin fad'a tace "inane nan? Yace "gidanki mana, gidan mijinki," ta waro ido cikin fargaba, Yace "sannu sadeeyna, yana matsowa inda take, da sauri ta matsa gefe tace "wlhy badai gidana ba yayanmu, ni bnda wani miji,"

Yace "kiyi ha'kuri dai karki sakama kanki damuwa, kinga ba lafiya ne dake ba," ya mi'ke ya d'auko magungunanta da ruwa ya tsiyaya a kofi ya mi'ka mata, kauda kanta tayi, Yace "ki daure kisha maganin don Allah," tace "bazan sha ba wlhy, ni garamun ma mutuwa da wannan cutar da kake shirin yimun.

Yace "cuta kuma sadeey? Tace "eeh mana, kasan baka sona, baka taba sona ba, da wacce kakeso mezaisa ka aureni? Da sigar lallashi yace "waye ya fad'a miki bani sonki sadeey?

Dafe kanta tayi tace "bani sonji yayanmu, bani sonjin duk wani kalamai daga bakinka, kaa riga ka makara," kukan da take ta so tayi ne ya 'kwace mata, Abdul yace "shikenan naji, don Allah ki daina kukannan, ki daure kisha maganin.

Mi'kewa tayi ta d'auki hijabinta dake gefenta ta saka ta sauko daga kan gado, yana tsaye har lokacin yana kallon ikon Allah, ta nufi 'kofar fita bedroom d'in, da sauri Abdul ya mi'ke yace "ina kuma zakije sadeey? Ta yamutsa fuska tace "inda ka d'aukoni mana, wlhy bazan zauna ba, bazan zauna a gidannan da wanda bai sona ba.

Yace "don Allah ki daina mana, kinsan kuwa ko 'karfe nawa yanzu? Tace "ko 'karfe nawa ne bazan kwana a gidannan ba," dafe kanshi yayi yaa rasa ma me zaiyi?

Tana niyyar fita yasha gabanta, taja baya, duk yanda yake tunanin lamarin da sau'ki yaa wuce tunaninshi, duk lallashin da yayi mata kasa ha'kura tayi, ya kasa maidata ya zaunar da itama da'kyar ya samu ya rufe d'akin ya fita.

Anan ta du'ke ta saki kuka, tana tausayin kanta, Yanzu mami ce zata yarda a had'a baki da ita a mata haka? Kamar basu suka haifeta ba za'a daura mata aure bada saninta ba, kuma a kaita gidan mijinta ba tare da saninta ba bata cikin hankalinta.

Sulalewa tayi saman carpet ta kwanta, tana kuka kamar ranta zai fita, ga haushin Abdul da takeji haka kawai yama raina mata hankali, saboda soyayyar da take mishi ne yake mata yanda yakeso.

Da tunani kala kala barci marar dadi ya dauketa anan saman carpet.

Dedicated to Mr. Smiles😃

❤❤Rabiatu sk msh❤❤

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts