New Post

Monday, 7 November 2016

HAKA SO YAKE 1-2

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_1 - 2_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

"Uhim, Uhim" tayi gyaran murya sannan tace " Sunana SUWAIBA amma wasu mutane sunfi kirana da SUBEECOOL, wad'ansu kuwa suce SUBEEY Amma ni wadda nafiso shine SUBEEY, hakan yasa mutane kowa yake kirana da subeey, natasone a gidan kanwar mahaifina, Inada yayana mai suna ABDUL AZEEZ, ina matukar son yaya ABDUL a cikin  zuciyata, yaya Abdul mutum ne mai son mutane da kuma son barkwanci, Inajin dad'in zama dashi sosai,  uhimm.." ta kara yin gyaran murya sannan taci gaba dacewa "Wai na manta bangaya muku kaman ninaba, ni farace, doguwa, kirara fulani domin asalina ni'yar kyauyen yola ce,
   Inada kyau amma saidai kash inada matsala d'ayah...."

"CUT " yafad'a yana dariya yad'an tsaya yana kallon wayarsa, kafin yad'ago kansa ya kalleta yace "video yayi kyau kinga yadda kika fito kuwa kamar wata ba'indiya, wannan ai zan iya d'aurashi a Instagram"
   Subeey ta murgid'a masa  baki tana hararansa cikin wasa tace "kagani koh yaya abdul gaskiya banaso, ni karka sakani a instrgrm kaifa kace zaka ajiye a wayar dan tarihi" takarasa maganar cike da shagwaba,
  Abdul ya yayi dariya yace "to naji zan ajiye amma, gaskiya zan daura a instrgrm, kin sani koki sami mai sonki" yakara bushewa da dariya

A Lokaci d'aya naga yanayin fuskar subeey ya chanza, ta Tsuke fuska tana hararanshi taja mayafinta tanufi hanyar fita daga d'akin, abdul yayi saurin cewa " ina kuma zakije bamu gama video ba fah"

  Subeey tajuyo edonta har yayi ja sosai murya a sanyaye tace " kajira harna samu mai sona sai muci gaba" Bata jira yayi maganaba tafita tabar d'akin,

   Sunanta yarika kira yana dariya, amma taki ko juyosa da sauri taja kofar d'akin tafita,

Da fitarta d'akinta ta nufa, tunkafin ta karasa kuka ya kubuce mata, ai kuwa  tana shiga d'akin  ta fad'a kan gado tafashe dakuka, zuciyarta cike da haushin kalamin da Abdul yafad'a,
    Kuka tayi sosai saida edonta yasoma kumbura, sannan tatashi tazo bakin mirror, tana kallon kanta, a hankali tasa hannu ta share hawayenta,
   Sannan takara kai Hannu ta tab'a edonta d'aya da batada lafiya,  tana murzata a hankali, nanfa kuka yasoma dawo mata, cikin shashshekar kuka tadafen edon tana cewa  "Saboda kene yaya abdul baya sona, narasa wata darajar a cikin jikina.." Ta fashewa da kuka  tana danna edon nata,
   Cen kuma bayan wasu dakiku ta tsayar da kukata tana hawaye takara d'ago kanta tana kallon kanta ta jikin mirror tace " yaya abdul ina sonka, wlh ina sonka HAR cikin ZUCIYA ta, amma narasa yazanyi na fahimtar  dakai MIYE SO, kayarda dani yaya abdul ..." Ita kad'ai take magana saikace wata zararriya, saikuma takara fashewa da kuka...

Via OHW📚📲

Related Posts:

  • ABDUL WAHAB 9ABDUL WAHAB 9 ©Rabiatu sk msh           ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION Tun daga ranar kullum Abdul neman hanyar da zai 'kara ganin khadija yake, gashi cikin rashin sa'a Ya… Read More
  • ABDUL WAHAB 8ABDUL WAHAB 8 ©Rabiatu SK msh           ®NWA Kauda fuskarshi yayi gefe, nan take yanayin khadija ya canja ba tare da taace mishi komi ba ta juya tabar wurin, da sauri yab… Read More
  • ABDUL WAHAB 6ABDUL WAHAB 6 ©Rabiatu sk msh~           ®NWA Tunda suka fito sadeey bakinta bai qarayin shiru ba, sai yaba kwalliyan Abdul d'inta take, hotuna kam taayi mishi ba adadi d… Read More
  • ABDUL WAHAB 10ABDUL WAHAB 10 ©Rabiatu Sk msh           ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION Sauke numfashi Abdul yayi sannan ya jingina da kujera, wayarshi ya ciro ya fara neman raheem, tun k… Read More
  • ABDUL WAHAB 7ABDUL WAHAB 7 ©Rabiatu SK msh        ®NWA Da sauri Abdul ya kashe wayarsa, duk ya tsure cikin duhu yake ma khady alamar ta taimaka mishi, tayi sauri ta danna wayarta tayi kamar ita aka … Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts