New Post

Saturday, 5 November 2016

A YINI ƊAYA 26-33

[5:18pm, 16/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀

   👹💀            💀👹
                 👺

          
     *Na Princess Amrah*
     *Da Rabiatu sk msh*

            Page 26-30

"Asalin k'ungiyar ta samo tushiya ne tun muna zana jarabawar jss, Shareef da Shareefat wanda suke twince ne masu k'aunar junan su da had'in kai tsakanin su.
      Tare ake kawo su makaranta kuma tare ake zuwa d'aukar su, duk abunda Shareef ya samu baya cin shi sai ya kawo ma Shareefat haka itama take.
      Ni kuma k'awata d'aya wato Afnan, duk da nake marainiya baba na ya rasu tun ina k'ank'anuwa ta hakan bai hana mahaifiya ta kaini wannan babbar private School d'in ba mai suna *SALDEFI INTERNATIONAL SCHOOL,* duk yaron da zaka gani a makarantar to d'an masu hali ne in banda ni da rufin asiri ne kawai kuma mahaifiya ta tana so na samu ilimi mai kyau.

     Afnan na k'auna ta sosai nima kuma ina k'aunar ta, har gidan su an sanni nima kuma gidan mu an santa. Sai dai kuma akwai banbancin halayyya tsakani na da ita saboda ita tana da son huld'a da mazan class d'in mu, tana yawan yi min fad'a wai na kasa in waye har yanzu gashi ina da kyau maza na son yi min magana amma bana basu fuska, sai dai kawai na mata murmushi idan ta fad'i haka.

    Kwatsam wata ranar da zamu kammala zana jarabawar jss muna zaune da Afnan akan window sai ga wani yaro yaxo kusa damu, hannu ya bata suka tafa kamar yanda suka saba ni kuwa na b'ata fuska tamkar ban tab'a dariya ba.
      "Wai Afnan wannan k'awar taki bata dariya ne ita?",
     Kallon ta ta juyo gare ni tace "Feenat wai? Tana yi mana me ka gani?",
     "Kawai dai yanayin ta na gani haka, amma ya kamata ta saki jiki damu tunda dai duk ana tare" ya k'arisa maganar da kanne mata ido d'aya.

     Shareef da Shareefat ne tafe hannun ta rik'e a nashi suka gitta ta inda muke, da sauri Afnan tace ma yaron "nikam Shamow dama ina son tambayar ka akan wancan yaran da suka wuce?",

     "Wai Shareef da Shareefat kike nufi?",
    "Ban san sunan su ba, amma pls ina so ka bani labarin daka sani game dasu, haka kawai yaran suna burge ni da alamar saurayi da budurwa ne"

    Saurin dafe bakin shi yayi yana k'ok'arin yin dariya "inji wa ya fad'a miki haka? Twince ne fa, ke baki ga komai nasu iri d'aya bane? Yaran gidan former Minister'n petroleum ne Alhaji Ma'aruf Sale, yaran 'yan gata ne da kike ganin su, suna k'aunar junan su sosai, kamar yanda kika gansun can to haka suke ko a class, koda yake ba class d'in mu d'aya dake ba saisa baki san su sosai ba har kike fad'in haka, babu malamin daya isa ko fad'a yayi ma d'ayan su, idan kuwa wani malami yayi kuskuren haka tou ranar baxai kwana a makarantar ba sai an kore shi, kowa yana tsoron tinkarar su da sunan magana saboda ko murmushi basu yi sai ga junan su, nima tun farkon zuwan su makarantar nan nake son masu magana amma hakan bata yiwuwa saboda sun fi k'arfi na, akwai wani yaro d'an ss2 daya ma macen magana wai yana son ta wallhi baki ga yanda yaron ya wulak'anta ba sai da ya bani tausayi, saisa kawai na hak'ura na k'yale su, ni wallahi tsoron su ma nake".

     Dariya Afnan ta k'yalk'yale da ita tana tafa hannu "amma dai ka bani kunya guy, kai yanxu duk tak'amar da k'wambon amma ka kasa tinkarar wasu, ni kuwa wallahi sai na masu magana sai dai duk abun da zai faru ya faru, kowa yana ji da nashi ai, su idan uban su former minister ne ni nawa  Commissioner of police ne, bari ma ka gani" mik'ewa tayi da sauri ta bi bayan su tana k'ok'arin shiga gaban su, nima nabi bayan su jiki na sai rawa yake dan bana so wani abu ya samu Afnan.

    "Hi" Afnan ta fad'a bayan ta shiga gaban su.
   "Hello" Reesha ya miyar mata da amsa,
   "Am Afnan by name", tare da sakin d'an murmushi.
    Kallon banza suka watsa mata kafin macen tace "and so?",
     "I just want you 2 to be my friends, ina yawan ganin ku a School d'in nan kuma kuna burge ni, and I  decided kawai na maku magana yau, babana shine commissioner of police a halin yanxu",

      Da sauri Shareef ya sakar mata fuska jin ko waye mahaifin ta yace "am Shareef and Shix Shareefat, nyc to meet you",

      "Nyc to meet you too dear, pls ko zan iya zama frnd d'in ku in ba damuwa?",

     Shareefat tace "why not? You can dear"

    Murmushi Afnan ta masu tare da mik'awa Shareef hannu suka gaisa sannan ta mik'a ma Shareefat, nan ta masu introducing d'ina da Shamow take suka hau hira kamar dama sun saba.

   Haka muka kasance mu biyar har lokacin da mukayi hutun jss, Afnan na zuwa gidan mu nima ina zuwa nasu, duk da talaucin mu bai sa ta raina mu ba, tana yawan bani labarin Reesha da Reeshat kamar yanda ta miyar masu da suna.

     Haka ta k'agara hutun mu ya k'are saboda sabuwar rayuwa da take burin yi idan mun koma, Shamow kuwa shi yayi naming namu da *5 STARS* saboda yanzu mun had'e kan mu sosai kamar mun dad'e da sanin junan mu.




*Amrah nd Rerbee'art sk novels📚*
[5:25pm, 16/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀

   👹💀            💀👹
                 👺

          
     *Na Princess Amrah*
     *Da Rabiatu sk msh*


          Page 31-33

Ranar da muka koma hutu kuwa munyi farin ciki saboda a class d'aya aka had'e mu, Shamow ya kawo wata Friend d'in shi Nuratu yace "shix my frnd wai tana da sha'awar kasnacewa a cikin mu ne, shine nace zan kawo ta ku gani",

    Reesha yace "tou muna da dokoki sai idan ta aminta dasu sannan zata shiga cikin mu"

   Da sauri ta d'aga kanta tana kallon shi,

   "K'ungiyar mu duk wanda ya shiga cikin ta zai mana alk'awarin bazai tab'a fita ba har sai lokacin da mutun zayyi aure, sannan kuma duk lokacin da muka yanke hukunci a abu babu wanda ya isa yace a'a, zamu ringa tallafawa junan mu idan wani yana buk'atar taimako, idan wani zayyi *BIRTHDAY* dole mu had'a kai mu faranta masa rai, kin yarda?",

    "Ehh na yarda wallahi na amince"

    "Good, miye Sunanki?",

     "Sunana Nuratu Abdullahi",

    "Kinyi register daga yanxu kin shiga cikin mu".

   Nidai haka nan nake cikin k'ungiyar ba wai dan ina so ba sai dan bana so na b'atawa Afnan rai dan naga itace silar k'ungiyar.

     Shamow yaji dad'i sosai yace "tou amma ya kama ta mu canja suna ko?"

    "Ehh ya kamata gaskiya" Reeshat ta fad'a.

    "Why not mu saka *AREWA STARS?* wato taurarin arewa",  Reesha ya bayar da shawara.

    Tafa hannu duka mukayi saboda sunan yayi dad'i sosai.

*******

Haka mukaita k'ara yawa har lokacin da muka kai mutun 15, daga nan Reesha yace a rufe shigar da mutane haka nan saboda idan mukayi yawa sosai abun bazayyi dad'i ba za'ayi ta samun sab'ani. Hakan kuwa mukayi bamu k'ara d'aukar kowa ba duk da akwai mutun uku da sukayi requesting amma akayi rejected nasu.

      Wata rana English teacher'n mu ya shigo shine first period ya fara lesson mu kuwa muna baya muna meeting akan *Birthday* d'in Iby dake gabatowa, wani taku muka fara jiyowa na takalmi  tun daga farkon class, a tare muka d'aga kai mukayi duba ga wata kyakkyawar budurwa sanye da sabbin uniforms d'in ta, skirt d'in ta ko guiwar ta bai rufe ba sai d'an hijabi akan wuyan ta, hannun ta na jan wani d'an trolley bag k'arami irin wanda ake saka littattafan makaranta. Duka hankalin 'yan class d'in ya koma gare ta saboda wani kallon raini da take watsa ma kowa,
    Baki ta tab'e tare da zare dark glasses d'in dake idon ta tace "excuse"
    Shi kanshi malamin sai da ya tsorata da ita, dan daga ganin wannan ba xatayi kunya ba, nan ta hau yi masa bayani cikin British English nata cewa Principal ya gwada nata nan class d'in yace taxo, sosai turancin yarinyar ya burge shi, take ya gwada mata baya yace ta zauna acan saboda duk gaban a cike yake, bayan kuwa mune kad'ai saboda kowa yana tsoron mu a class d'in yasa babu mai iya tinkarar wurin mu ya zauna.


*Amrah nd Rerbee'art sk novels📚*

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts