💕💕 *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
💗💗💗💗💗
💕 *_17 - 18_*💕
💗💗💗💗
*Na*
*_Rabee'at sk mash_*♥
```_And_```
*_Mr, smiles_*😃
Abdul cikin sauri ya k'arasa wurin wannan kyakkawan saurayi yana bashi hak'uri, Anma hankalinshi sam baya jikinshi yanacen ya k'ura ma suby ido, itama kallonshi take tana ayyano haɗuwarshi a cikin zuciyarta.
Baima kalli inda Abdul yake ba ya fara tafiya zuwa inda suby take, sai lokacin suka lura da k'afarshi d'aya tana da matsala, wata irin tafiya yake yanad'an jefa kafar, harda sanda irin mai kyaunnan A hannunshi, A zuciyar sadeey tace "Allah mun gode maka da baiwar dakai mana"
Abdul ya tareshi da cewa "Yadai malam? sai baka hak'uri nake amma kayi shiru sai tafiya kake, idan baka hak'ura ba kaimin magana in biyaka mana" Saurayinnan Yayi murmushin daya k'ara bayyana kyaunshi Yace "Ayna daɗe da hak'ura, tun lokacin sa idona suka hangomin kyakkyawar k'anwarnan taka" yakarasa maganar yana nuna subeey
Damm!! Abdul yaji gabansa yafad'i, kalaman saurayin sun sosa masa zuciya sosai, Ransa ya ɓace yace "ina ruwanka da k'anwata da zaka k'ura Mata ido? Da Allah malama shige muje" Yaja tsoki yana kokarin komawa cikin mota.
Suby zata buɗe mota Ta shiga sai dai taji maganarshi kusa da ita "Sunana Ahmad ne, da alama yayannan namu zafi ne dashi, amm basai na tsaya miki dogon bayani ba kinsan menene manufata, ki duba idan har kinga cancantata ki taimakeni da numbarki,"
Daga can waje Abdul Yace "zaki shigo mu tafi ko saina barki a wurinnan?" murmushi kawai tayi ta mikawa Ahmad wayarta ba tare da tace komi ba.
Yana murmushi ya karbi wayar ya saka Mata number ɗinshi sannan ya kira, wayarsa nacikin aljihunsa tad'au ring sannan yakara yin murmushi Yace "yawwa gatanan tashigo, ngde sosae, sai kin jini" ta ɗaga kai kawai ta buɗa motan zata shiga" har ya fara tafiya ya juyo, Yace "Har yanzu fa bakimin magana ba, ko kina rowar zazzaƙk'ar muryarkine"
Girgiza kai tayi tana murmushi tare da cewa "Sunana subeey" dariya Ahmad yayi mai sauti "Suna mai daɗi, kuma murya mai daɗi"
Subeey tana kokarin shiga mota tace "ngde mai daɗin baki" takarasa maganar da zolaya,
Ahmad yana dariya Yace "tun yanzu shaidar da zakimin kenan? " Bata bashi amsa ba sai dai dariyar da tayi ta shige mota, lokacin Abdul ya gama cika sosai, zuciyarshi sai tafasa yake baice mata komi ba ya hizgi motan yayi gaba.
Daria ta fara yi ciki-ciki tana kallon yanda Abdul ya ɓata rai, a zuci yace "tohh miye nawa aciki? Saboda kawai ta bama saurayinnan numbarta, meyasa nake kishi, mtsw" Tsoki yaja,
Subbey tayi ƙk'ok'arin shanye dariyarta sannan tajuyo ta dubesa tace "yadai Yayana?" banza yayi ya ƙk'yaleta yana ci gaba dajin wani irin zafi a cikin zuciyarshi ganin da yayi sadeey sai murna take hankalinta kwance. Yasa yakara jan tsoki, jiyake kamar yakai mata duka,
Subeey kuwa farin ciki fal a zuciyarta, sunan saurayin tasoma tunawa domin sunan ya kwanta mata, Cikin Zuciyarta tace "ni yama sunanshi?" batasan maganar ta fito fili ba, cikin ƙk'uluwa Abdul Yace "saimu koma a tambayoshi" yaja uban burki ƙk'uu ya tsayar da motar.
Hannu ta saka tana rufe bakinta tace "Allah ya baka hak'uri yaya Abdul, ay yanzu komun koma ma yaa tafi"
"da bai tafi ba komawar zakiyi kenan? Wato Ke harkin samu damar da zaki kulaƙwani saurayi a gabana koh? Yanzu zai samu damar dazai rainani ina yayanki, sai wani iyayi kike da kilbibi ke kinga saurayi, shi kuma ya jawo wasu miskinan k'afafu yazo inda kike harda tambayarki number, ke kuma da Allah yasa kunya ta miki karanci shine kika kwasa kika bashi" duk cikin zafin rai yake maganar, nanfa yaci gaba da masifa saikace wanda akayiwa wani laifi,
Jin faɗan bamai k'arewa bane, ya saka suby taja bakinta tayi gum tana saurarenshi, dariya na cinta har suka iso gida, ya riga ta fita daga motar ya shige ciki duk ranshi a ɓace..
Via OHW📚
0 comments:
Post a Comment