New Post

Sunday, 27 November 2016

HAKA SO YAKE 41-42

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_41 - 42_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

Bayan sun fita malam habu yad'aga edosa yadube hauwa,
Hauwa ta bushe dadariya "wayaga namijin gaske a gaban mazaje, basai jikinsa yad'au rawa ba" takara maganar tana dariya,

Malam habu yace "ke meye abin dariya farin ciki yana gaf da samuwa acikin gidan nan, yanzu indan Alhaji ya aure suwaiba aini da talauci munyi hannun riga", Malam habu yad'aga hannunsa sama yana rokon Allah yasa suwaiba takasance zabin Alhaji, domin ta wannan hanyar ce kad'ai zai iya biyansa kud'insa,

*BIRNI*

Subeey gabaki d'aya yanzu tasaki jikinta kamar babu abinda ke damunta, duk da kuwa a cikin zuciyarta akwai wani bangane wanda ta ajiye soyayyar Abdul aciki, amma takasa mantawa dashi, koda yaushe taje kwanciya saita tuna cewa yanzu shikenan ta rasa abdul, yanzu watace zata aure Abdul ba itaba, duk ta tuna wannan sai tayi kuka,

Soyayyarta da ahmed kuwa sai abinda yakaro domin yanzu kullum yana hanyar gidansu,
  Tun Abdul yana nuna damuwarsa akan haka har yazo yadaina nunawa amma a koda yaushe yaga ahmed yana fira da subeey, to sai yaji kamar ana masa zugar wuta a zuciya, amma saidai baya ganin laifin kowa ta wannan hanyar shikansa yasan laifin sane,

*BAYAN KWANA UKKU*

Misalin karfe 8:30pm Nadare subeey ce kwance a cikin d'akinta kan gadonta tana juyi, waya makalle a kunnenta ga dukkan alamu waya take kuma wayar tayi matukar mata dad'i, kuma bada kowa take wayarba face Ahmed,
Ahmed yace "kinsan me, Allah jiya nayi mafarkin wai angyara miki edon nan, kinyi bala'in kara kyau"
  Dariya tafashe da ita sannan tace " ai wannan edon nawa bazai taba warkewaba nima hakan natashi naga kaina, kama daina wannan mafarkin,"
Ahmed shima dariyar yake yace "ninasan wata rana insha Allah zan gyara miki shi matukar zai gyaru, amma dai sai bayan munyi aure, domin bazan gyarashi a yanzuba wani yaganki yamun kwace"
Subeey tace "lah ashema ragone akan soyayya har kana tunanin wani zaizo ya kwaceni a wurinka"
Ahmed yace "tap waya isa ai ko mutuwa bazatayi wannan gaggancinba, ke nida kefa mutu ka raba takalmin kaza"
Subeey tayi murmushi tana shirin yin magana,
Momy ta turo kofar d'akinta tashigo, dasauri tacewa Ahmed "ina zuwa momy tashigo" bata jira yayi maganaba takashe wayar tana kallon momy tana murmushi,
Momy takaraso kusa da ita tazauna tana murmushi tace "subeey sarkin waya ke kam ko gajiya bakyayi"
Subeey ta noke kai saboda kunyar dataji ta risketa a lokaci d'aya, takasa yin magana sai murmushi take,
Momy tayi ajiyar zuciya sannan tace "daman bakomaine yakawoniba face akan maganar ahmed, munyi waya da abban ku  yace jibi zai dawo, nayi masa magana akan ahmed, yace kice yaturo iyayensa zuwa jibin sai suyi magana akan aurenku"
Subeey ta rufe fuskarta tana dariya, ciki - ciki tace "toh momy zan fad'a masa" takarasa maganar kamar wata marar lafiya,
Momy tamike tsaye "toh shikenan, sai kin fito ina jiranki a falo" tace to momy,

Nan Momy tafita, 

ko karasa rufe kofar d'akin momy bata yiba subeey tayi saurin ciro wayarta takira ahmed ringing biyu yad'auka tana fara tace "abishirinka "
Ahmed yace "fari kal, kamar farin wata"
Subeey tace "abbana zai dawo jibi, kuma yace agayama katuro iyayenka akan maganar aurenmu"
Ahmed kasa cewa komai yayi dan farin ciki, saidai subeey takara cewa "yadai  naji kayi shiru"
Ahmed yasauke nunfashi yace "masha Allah,  nama rasa mema zance, akan farin ciki, ina zuwa bari naje nayiwa ummata wannan farin albishir" subeey tace "toh agaida umma" nan suka kashe wayar subeey tatashitafita falo sukayi kallo ita da momy,

Ahmed kuwa yayiwa ummansa albisir, saida tayi hawaye dandad'i yanzu dai yaronta zaiyi aure, daman abinda take muradine tuntuni.

Abdul kuwa yasamu labarin a wurin momy domin koda tabar d'akin subeey ta fito falo tatarar dashi azaune yana kalllo anantasar dashi, saboda tsabar bakin ciki, tashi kawai yayi yabar falon tare dacewa momy kansa keciwo, ai kuwa yana shiga dakin yashare hawayensa ,yarasa meyasa yake damuwa da subbey a yanzu, shin kodai hasashen da zuciyarsa ke masa gaskiyane sonta yake,    
    dakarfi yace "no baso a raina, kuma zanfita harkar subeey har abada" da wannan zulumin yakwanta saman gado yana hawaye wad'anda yakasa sanin dalilin zuwansu..

Via OHW 📚📲

Related Posts:

  • MATATAH CE 55♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              55 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More
  • MATATAH CE 52♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              52 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More
  • MATATAH CE 51♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              51 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More
  • MATATAH CE 54♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡             54 ©Rabiatu sk msh       ®NWA   … Read More
  • MATATAH CE 53♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              53 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts