New Post

Saturday, 5 November 2016

A YINI ƊAYA 1-2

[11:20pm, 19/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀

    💀💀           💀💀
                 👺

              *NWA*
    NA *Princess Amrah*
    Da *Rabiatu sk msh*

  *~hannu biyu writers~*

           
Duk kan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mad`aukakin sarki, tsira da aminci su k`ara tabbata ga shugaban mu annabi Muhammad (SAW) tare da alayen sa. Kamar yanda muka fara rubata wannan littafin, muna fatan mu k`arisa shi cikin aminci da yardar Allah mad`aukakin sarki, muna fatan abun da muke son isarwa ya isa ga d`aukacin al'ummah musulmai har ma da wanda ba musulmai ba.

Wannan labarin k`irkirarre ne k`agagge ne munyi shi ne akan illar zuwa party, da duk wurin da addinin musulunci yayi hani dashi, ba munyi shi don cin zarafin wani ko wata bane, munyi ne domin nuna illar abun.

Abstract (shimfid`a).
Labari ne mai ku`nshe da wasu bayin Allah da suka mayar da zuwa party tamkar ruwan shan su, sukan fita a kowane lokaci ba tare da sanin iyayen su ba, sai dai kuma daga baya zasu had`u da rikicin rayuwa suyi dana sani a lokacin da bashi da amfani. Allah ya shiryar damu bisa hanya madaidaiciya, Allah kuma ya bamu ikon d`aukar abunda zamu karanta a ciki.
    But idan kin San kina da tsoro kar ki karanta shi. (Lol..😊)

              Page 1⃣

K`arfe 8:00AM.
      Kwance take kan lallausan gadon ta na royal bed, wayar ta na jikin chaji amma still tana latsar ta, zumbur ta mik`e cike da murna tana fad`in "yesss! Am glad to hear that woooo" komawa tayi ta kwanta taci gaba da charting d`in ta.
      Wani kyakkyawan yaro ne ya shigo d`akin cikin shagwab`a yace "yaya Afnan momy is calling youh",
     Cikin haushi tace "am coming",
       "Buh yaya Afnan the momy said...", katse yaron tayi "Affan tell her that am coming now", tafiya yayi yana waigen ko ta taho har yabar d`akin bata tafi ba, aikin charting kawai take.
      Jin shiru Afnan batazo ba yasa momy sake tura Affan, a bakin k`ofa suka had`u tace "sai ka tafi ai uban gulma gani a hanya".
      Bakin shi tunzure ya tafi tana biye dashi a baya.

      "Afnan wai bazakije islamiya bane tun d`azu Affan ya shirya yana jiran ki amma kin k`i fitowa?", "momy banda lafiya fa" Afnan ta fad`a cikin shagwab`a.
    "Me ya same ki?"
     "Momy mp ne fa",
    "Eyyah sorie, kije ki kwanta ki huta, hope kin sha magani"
     "Yeah momy nasha"
      "Ok Allah baki lafiya, Affan kaje kacewa driver ya kai ka kawai, kace wa malamin su Afnan wai bazata samu zuwa ba may be da yamma idan ta samu sauk`i taxo".
      Kitchen ya nufa ya d`auki launch box nashi ya nufi mota.

     Dakin ta ta koma taci gaba da charting d`in ta. A fili tace "kawai abi a damu mutun da wata islamiya, da yamman ma barin je ba birthday party'n Kerry zanje".
 
      "Arewa Stars kun jini shiru wlh momy ne ta kira ni wai sai na tafi islamiya".
    D`aya daga cikin members na group d`in Arewa Stars tace "hhhh tou ya kika ce da ita?"
      Afnan ta mayar mata da "nace mata mp pain ke damu na".
       Wani namiji ya turo da "lol...Afnan bakya ji fa, yanzu dai ku fidda mana colour`n da zamu saka anjima",

       Sally tace "ai an riga da an fitar, ash, pink and black ne zaa saka, har na kira wanda zai mana decoration na sanar dashi colour d`in",

      Haka dai sukaci gaba da hirarrakin su cike da nishad`i da munanan k`udurin abubuwan da zasu aikata a wurin birthday party`n Kerry.

        A rikice ta fito daga d`akin ta dan duk a kayan ta bata da colour d`in da zasu saka, "Afnan lafiya?" Momy ta fad`a tana kallon ta.
       "Lafiya lau momy, maganar practical materials d`in  mu ne, malamin yace daga ranar monday za`a rufe sayar wa",
    "Tou Afnan yau fa Saturday, kina tunanin idan kinje yau zaki samu ne? Kuma ma ai naga duka fa jiya kikace ya fad`a maku ku siya",
     "Momy tun fa last week ya fad`a nice dai ban sani ba sai jiya".
     "Ok akwai kud`i hannun ki ko sai na baki?",
       "Momy sai kin k`aro min dan ban san ko nawa zan kashe ba kar suyi min short",
     "Ok ki bud`e side drawer na ki d`auki yanda zai ishe ki".

   Cikin murna ta nufi d`akin, kud`i sosai ta d`auka sannan ta fito. "Zaki iya driving ko sai Abu ya dawo ya kaiki?",
     "Zan iya momy" ta fad`a tare da d`aukan key ta fita waje, a daidai parking space d`in babban gidan su taje, wata benz cement colour ta bud`e ta shiga.
     Bata zarce ko ina ba sai gidan su Feenah.
    Bayan ta gaishe da maman Feenah suka shiga d`an k`aramin d`akin ta.
    "Ina fatan kina sane da birthday party`n kerry yau ne, kuma nasan baki da colour`n kayan da za`a saka, shine nazo d`aukan ki muje na siya miki",
    "Eyyah Afnan nikam yau barin je wannan party`n ba, wanda naje a baya ma ina rok`on Allah ya yafe min dan zunubi ne babba muke kwasar wa kan mu, kuma ga k`arya da muke yiwa iyayen mu kawai dan muje wurin sab`on Allah, gaskiya ki tafi kawai bana so".
      Cikin takaici Afnan ta mik`e tsaye "haka kika fad`a ko? Aikuwa yanzun nan zanje na sanar da umma`n ki abubuwan da kikayi a baya, kuma wallahi harda k`ari zan miki nasan dole zata yarda",
     Marairaicewa Feenah tayi dan tasan halin umman ta, k`aramin aikin tane ma ta hana ta zuwa har skul d`in ta da ko ina ma, sosai ummanta ke tsaron ta.
    Ganin Feenah tayi zurfi a tunani yasa Afnan ta fara cewa "sai kisan abunda zaki fad`awa umman ki dan ki kare kanki".
     Cikin takaici Feenah tace "kiyi hak`uri Afnan kar ki fad`a mata, na yarda zanje".
    Murmushin mugunta Afnan tayi tace "oya lets go".
      Hijabin ta har k`asa ta sako, a d`an madaidaicin parlor`n su suka tayar da umma`n ta, "ummah zan raka Afnan gidan su Maryam khalil  amma bazamu dad`e ba".
    "Ok a dawo lafiya, ki gaishe min da hajiya Zainab, kiyi saurin dawowa ki tafi tahfiz k`arfe sha biyu".
    "Insha Allahu momy barin dad`e ba".

     Daga nan kuma suka kama hanyar AA BOUTIQUE don sayen k`ananan kayan da zasu saka.

©Amrah and Rerbee'art novels
Admins
ONLINE HAUSA READERS📚
[11:29pm, 19/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀

   👹💀            💀👹
                 👺

           *®NWA*
     *Na Princess Amrah*
     *Da Rabiatu sk msh*

                  Page2⃣

Nan suka hau dudduba kalar kayan da zasu saka, Afnan ce taci karo da wata had`ad`d`iyar top gown hot pink sai torches d`in black kad`an kad`an, baki d`aya k`irjin rigar a bud`e yake da wasu hudojin da aka k`awata su da zanen manyan flowers, bayan rigar yafi gaban ta tsawo da kad`an, hannun ta ma d`aya dogo d`aya gajere ne, gata da shape sosai irin wadda take fidda zahirin coca cola shape na mace, (niko Amrah nace wannan kyan ta masu aure su same ta, ai ranar babu oga ba zuwa office..lol).
      Bayan ta tabbatar da rigar ta burge ta ne suka hau dubama Feenat nata, "nidai Afnan pls bana son mai tallan jikin nan, asamar min mai rufe tsiraici",
     Cikin fushi Afnan tace "wallahi duk wadda aka samu ita zaki d`auka kuma dole ki saka ta",
      Shiru Feenat tayi taci gaba da bin bayan Afnan suna kewaye boutique d`in, da k`yar suka samu wata gown ash da torches  d`in pink, gown ce ta mutunci mai A shape, zata iya sauka har k`asa, tana da turtle neck da dogon hannu. Sosai Feenat taji dad`in wannan rigar, dan tasan zata iya sakata ba tare da taji komai ba.
   Side d`in jewelries suka koma, nan naga k`aryar fashion sark`a da `yan kunne da abun hannu, komai na AA BOUTIQUE kyau gare shi, nan Afnan ta zab`i wata siririyar chain mai kyau, Feenat ma irin shi ta zab`a, kud`in suka biya sannan suka koma mota dan nufar gida.
  
        Cike da damuwa Feenat ta kalli Afnan tace "yanzu Afnan wace k`arya zan ma Ummah anjima idan zan fito?"
"Oho miki, sai kisan abunda zaki fad`a mata, nidai k`arfe biyar na yamma zanzo d`aukar ki, ki tabbatar kin shirya by then",
   Tun daga nan kuma sukayi shiru su duka har akazo k`ofar gidan su Feenat.
    Afnan da kanta ta fitar ma Feenat da kayan ta daga leda, cikin in ina Feenat tace "Afnan ki tafi da kayan nan idan mun tafi can zan saka, dan yanzu Ummah zata iya cewa in bata ta gani kuma nasan halin ta zata iya fahimtar wani abu",
Bata ce mata komai ba sai jinjina kanta da tayi, daga nan taja motar ta sai gida.

*K`arfe 1:00pm*
*~Gidan su Ruky.~*
      "Momy ta samu fa, yau ma akwai wani casun",
     Wadda ta kira da momy tayi mirmushi tace "kedai Ruky bakya gajiya da casu, kullun baki nan baki can, duk inda ake wani biki ko party kina can ko? Yau kuma wane casu ne akeyi?"
    "Momy birthday party`n Kerry ne fa za`ayi kuma mune best friends nata, idan bamuje ba waye zaije?"
     Momy tace "ehh kuma fa gaskiyan ki, to amma ki k`ure kwalliya dan nasan yau akwai wankan gayu, so nake auta ta tafi kowa yin kyau a wurin, kiyi chajin iphone d`in ki sosai yanda zaki d`auko pictures da yawa",
     Can naji wata murya zazzak`a daga bakin k`ofa tana fad`in "haba momy, wai yaushe zaku tuba ga Allah ne ki daina d`ora Ruk`ayya akan wannan munanan halayen? Ku baku ma tsoron mutuwar ku? Koda yaushe fa mutuwa zata iya riskar ku dan ita bata alerting mutun kafin tazo",
    Cikin takaici momy tace "ke Rumaysa wai ina ruwan ki ne? Ni tunda na gane ke ba wayayyiya bace kinga ina saka ki a irin wannan harkokin ne? tou wallahi kul dinki, kar ki kuma jefo mana wannan shegen bakin naki idan muna maganar mu".

     Rumaysah tayi shiru daga nan bata kuma fad`in komai ba, sai dai kuma har a ranta tana tir da Allawadan halin mahaifiyar ta da k`anwar ta Rukayya, mahaifin su yana kabari amma su suna nan basu ta yi mashi addu`ah sai munanan d`abiu, da wannan tunanin ta shiga d`akin ta cike da tsanar halayyar su.

     Da tafiyar ta kuwa suka hau shewa da k`arfi, momy tace "k`arfe nawa ne party`n?"
"K`arfe biyar na yamma ne momy, amma kuma nasan ba lallai ne a fara shi a lokacin ba ana iya akai dare",
"A ina zakuyi"
"Momy nima ban sani ba, suna so suyi suprising namu ne, Sally ce kawai tasan inda za`ayi dan har ma ta tura wanda zayyi mana decoration ina tunanin ma har an gama",
"Tou yayi daidai `yata, ya maganar dressing fa?",
"Pink, black and ash ne za`ayi kuma ina dasu ai da banda shi momy da tun d`azu na mimi magana",
"Ok yayi daidai autah nah, Allah kaimu anjimar, sai ki tafi da mota ta dan bana so kowa ya kara ki a tashi dan kar a miki wulak`anci",
   Tafi sukayi da junan su, Ruky tace "das my momy, saisa nake sonki always".
©Amrah and Rerbeeart novels,
Admins
ONLINE HAUSA READERS📚

Related Posts:

  • MAKASHINKA 29-30```MAKASHINKA...```           29-30 ©Rabiatu sk msh     A hanyarsu ta komawa gida, sadeey tayi shiru tana sauraren Shamsuddeen yana ƙara mata nasiha, ba … Read More
  • MAKASHINKA 27-28```MAKASHINKA...```           27-28 ©Rabiatu sk msh Zuwan yayanta ya hana shamsuddeen ya fara koya mata, duk inda zataje da yayanta take zuwa kullum suna tare, har ya gama wee… Read More
  • MAKASHINKA 33-34```MAKASHINKA...```           33-34 ©Rabiatu sk msh Wani Yammaci shamsuddeen da sadeey na zaune a gefen wurin wasa a harabar gidan. Wasa take da yatsun hannunta tana yawan sat… Read More
  • MAKASHINKA 25-26```MAKASHINKA...```          25-26 ©Rabiatu sk msh Shamsuddeen zaune ya haɗe fuska wuri ɗaya, ranshi a ɓace yake kallon hafeez dake ta dariyarshi hankalinshi kwance … Read More
  • MAKASHINKA 31-32```MAKASHINKA...```            31-32 ©Rabiatu Sk Msh Shamsuddeen ganin yayi gudu mai nisa basu biyoshi ba ya sakashi tsayawa yana wasi-wasi, ihunta ya jiyo daga can nesa,… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts