💕💕 *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
💗💗💗💗💗
💕 *_19- 20_*💕
💗💗💗💗
*Na*
*_Rabee'at sk mash_*♥
```_And_```
*_Mr, smiles_*😃
www.babymsh.blogspot.com
Dasauri ta biyoshi har suka shiga falo, tana cewa "haba yaya ka tsaya mana, ka tsaya don Allah".
Ya juyo a harzuK'e, "mezan miki idanna tsaya? Shi kenan ko wani jaki da doki kuma sai Yace yana sonki?"
Subeey Tace "nifa ba cewa yayi yana sona ba"
Abdul yakara d'aure fuska Yace "eeh yanzu kuma saiki maidani sakarai, toh idan ba yana sonki ba mezai saka ya anshi numberki?
Momie ta fito daga ɗaki jin hayaniyarsu "me nake shirin ji kuma daga shiryawa?" ya k'arasa inda momie take yana k'ara ɗaga murya "komi ma sai kiji momie, donta maidani sakarai a gabana zata baima wani saurayi numberta? Shikenan ni kullum cikin gadinta nake amma a hakanma ban iya ba?"
Momie daɗi ya kamata cikin fara'a tace "da alama dai yau suby taa samo mana suriki ko?"
kamar yayi hauka jin kalaman momy yakara bata rai yace "ko tayi saurayi dai ko batayi ba abnda tayi bai dace ba"
Akafaice subeey ta tayiwa momy alama datayi shiru,
momie tayi murmushi tace "tohh ci gaba da faɗa mata ni kunga tafiya ta" momie tabar falon tana dariya
Yana tsaye shikansa yasara dalilin yin fad'ansa, sai masifa yake shikadai, dasauri Suby taje tad'auko mishi cup da ruwa mai sanyi, takarasa wurinsa, ta tsaya a gabasa suna had'a edo yayi shiru, tayi murmushi tana mika masa cup d'in, baisan lokacin dayakai hannu ya karb'a ba, sannan tace "ni bansan faɗan da kakeba Ya Abdul, saboda nayi saurayine kodan na bashi numba?.
Abdul Yace "Duka"
Subeey tayi ƴy'ar daria tace "ina ganin zuciyarka ke tafarfasa yaya kasha ruwannan zatayi sanyi" ta juya da gudu kawai ta shige kar ya k'ara mata wata masifar" tana dariya..
Via OHW📚
0 comments:
Post a Comment