💀 *A YINI 'DAYA* 💀
👹💀 💀👹
👺
*®NWA*
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page 36
*```KARSHE```*
💓💓💓
haka dai rayuwar taci gaba da tab'arb'are masu, raunukan su sai k'ara rub'ewa suke abun k'yama da tausayi, Ummy banda wari babu abunda takeyi, ko Mamin ta ta daina shiga d'akin da take, in ma abinci zata kai mata sai dai ta ajiye daga bakin k'ofa ta rarraho ta d'auka.
Afnan kuwa Momy ta aika da hoton ta masallatai ayi tallar ta, nan da nan kuwa aka fara rububin ta, amma da mamaki duk wanda yazo yaga fuskar ta da yanda take sai ya tafiyar sa.
Kamar kullum Momy ce zaune ta buga tagumi ta tsurawa Afnan ido tana kallon ta cike da tausayi, sallamah akayi Momy tayi saurin amsawa tana kallon mai shigowa, Dady ne ta gani hannun shi rik'e da Affan sanye da Uniforms alamar daga makaranta ya d'auko shi,
"Oyoyo momy na" ya fad'a tare da isowa wurin Momy.
"Sannu da dawowa Alhaji" ta fad'a bayan ta rungume Affan a cinyar ta tana cire masa safar k'afa.
"Momy wai yaushe Yaya Afnan zata warke ne?",
D'an murmushin yak'e ta mashi kafin tace "insha Allahu zata samu lafiya yaro na, ka ringa saka ta a addu'ah kaji?",
Kai ya d'aga cike da tausayin 'yar uwar sa.
"Assalamu alaikum" akayi sallamah,
Dady ya amsa da "wa alaikumussalam, Mati ya akayi ne?",
"Yallab'ai kayi bak'o",
"Bak'o? Waye ne?",
"Wani gurgu ne yallab'ai, yace ayi masa sallamah da kai",
"Gurgu? To kace ina zuwa".
Kallon shi ya miyar ga Momy yace "Maman Afnan barin fita inga mai nema na".
Bayan ya fita ya samu wani gurgu ne ya mik'a masa hannu suka gaisa,
"Bawan Allah meke tafe da kai?" Dady ya fad'a yana kallon gurgun mai ido d'aya.
"Sunana Sani, dama yallab'ai naga wani hoto ne a masallacin da nake aiki, so ina da ra'ayin auren yarinyar indai babu damuwa"
Shiru Dady yayi ya k'are masa kallo sosai sannan yace "ehh to! Nidai a wuri na babu damuwa, amma ka shigo mu shiga ciki idan yarinyar taji tana son ka sai ayi binciken komai sannan a d'aura aure".
Murmushi yayi sannan yabi bayan Dady daya fara shigewa cikin gida.
Bayan sun shiga ciki ya gaishe da Momy cikin girmamawa itama ta amsa masa da sakin fuska.
Dady yayi ma Momy bayanin abunda yake tafe dashi kai tsaye momy ta goyi bayan abun,
Afnan ma dake kwance take ta amince dashi duk da yanda yake d'in.
*****
Shirye shirye sosai suka kankama na bikin Sani gurgu da Afnan, duk da ba wani abu za'ayi ba walima ce kawai za'ayi.
Ranar jumu'ah aka d'aura auren su amarya ta tare a babban gidan ta da Dady'n ta ya mallaka mata ita da mijin ta.
Feenat kuwa taci gaba da zuwa makarantar ta har sun fara zana jarabawar k'arshe ta sakandire.
Kerry kuma har yanzu abun shiru babu sauk'i, gashi kuma sun k'i zuwa wurin malamai duk da shawarar hakan da ake basu.
*AREWA STARS* dai a haka suka k'are da tab'arb'ararriyar rayuwa, wannan ishara ce ga masu hali irin nasu, masu yawan zuwa party ba tare da iyayen su sun sani ba, ina fatan wannan gajeren labarin zai zama fad'akarwa ga al'ummah musulmai har ma da wanda ba musulman ba.
ALHAMDULILLAH!!!
Duk abunda yayi farko zayyi k'arshe, muna godiya ga Allah mai kowa mai komai da ya bamu ikon kammala wannan labarin namu, kurakuran dake cikin labarin Allah ya yafe mana,inda muka yi daidai kuma Allah ya bamu ladar.
Muna godiya ga masoyan mu da suka bibiyi labarin har ya kaiga k'arshe irin su:-
```Rukayya Auwal,```
```Faty KK```
```Husnah Ibrahim,```
```Aysha Khalil,```
```Amman Suraj```
Da da da da, lissafo ku ba abune mai sauk'i ba, sai dai muce muna k'aunar ku akoda yaushe, kuci gaba da kasancewa damu a littattafan mu na gaba.
Jinjina, fatan alkhairi, godiya su tabbata ga K'ungiya mai albarka *```NAGARTA WRITERS ASSOCIATION```* Allah ya bar zumunci ya k'ara had'a kawunan mu amin.
```ZARAH~B~B``` *godiya da jinjina mai tarin yawa a gare ki, kin nuna mana soyayya kuma kina kan nuna mana ita, Allah yabar mu tare ya k'ara miki baseerah.*
All groups members and admins na group d'in da muke muna gaishe ku, tsayawa lissafo ku ba abune mai sauk'i ba, sai dai mu maku godiya da bibiyar labarinmu da kukayi.
'Yan uwan mu writers muna godiya a gare ku, Allah ya raba mu da sharrin mahassada da mak'iya.
Amrah and Rabi'atu sk novels group mun gaishe ku da babbar murya, Allah ya barmu tare ameen.
Kuci gaba da kasnacewa dani Amrah a cikin novel d'ina mai suna *UMMU HAYDAR* idan na kammala exam insha Allahu.
Amratu A Mashi and Rabiatu Sk msh
AKA
Amrah da Rerbee'art
ke cewa mu huta lafiya.
0 comments:
Post a Comment