New Post

Monday, 7 November 2016

HAKA SO YAKE 5-6

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_5 - 6_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

Momie ta kalli subeey tace "Yau me za'a girka mana ne"? Subeey tace "mai dadi momie, anma fried rice zan dafa da farfesun naman rago, tunda munyi fad'a da yaya Abdul shi kuma yafison tuwon semonvita, bazan girka abinda yakeso ba"
Momie dariya tayi sosae shiko Abdul duk ya marairaice fuska momie tace "aikam babu mai shiga tsakaninku, nasan zai lalla'baki ko kinyi fried rice ki mishi tuwon daga baya,! Tace "A'ah momie yau fa bazanji rarrashinshi ba, barima inje in fara ta mi'ke zata fita.

Abdul ma yabi bayanta yana cewa "haba 'kanwata kinsanfa bamu haka dake, kinga muje ma in tayaki munayi muna firarmu! Wani irin dad'i sosae ya ziyarci zuciyar subeey, ba 'karamin burgeta yakayi ba, ji take daman a gidansu na aure ne  suke gudanar da irin wannan soyayyar!

A kitchen kusan tare suke aikin, a nutse take gudanar da komi cikin tsafta, gani tayi Abdul ya tsaya yana kallonta, watsa yatsunta tayi tana murmushi tace "yadai? Yace "dai dai, kawai wani tunani ne nayi, gaskiya qanwatah duk mijin daya aureki yaayi dace sosae, kinga yanda kike girkinnan kuwa, kamar ace a gidanki ne"

A lokaci d'aya Wasu hawaye suka tarar mata a ido tayi saurin juyawa tana share 'kwallah, baiyi shiru ba yaci gaba da cewa, "gaskiya na 'kagara inga ranar aurenki qanwatah, don ba qaramin shagali zamu shirya miki ba, kinsan me? Zan shirya miki party kala-kala har saikin gaji ko angon yace ya isa hakanan, kinsan inaji da qanwatah sosai kuma  burinah inga lokacin aurenta"

Ba tare data juyo ba tana 'ko'karin tsaida hawayenta tace "zaka dad'e baka gani ba kam, tunda wanda nakeso ko kad'an hankalinshi baya wurinah," ajiye ladle d'in hannunshi yayi ya matso inda take yace "waneneshi da bansanshi ba qanwatah?

Juyowa tayi bayan ta share hawayen tace "kafi kowa saninshi yayanah, Yanzu sha'kuwar da mukai bata kai ka dinga gane duk halin da nake ciki da zuciyatah ba? Dariya yayi cikin wasa yace "yaren zuciyah ay sai mai ita en matah, nida baki ta'ba bani labarin soyayyarki ba ya za'ai in sani? Laifi ma ya kamata ince kinyi mun tunda baki fad'amun qanen nawa ba na sanshi!

Girgiza kai tayi tace "wani yaren da zuciyah ta kasa bayyanawa, baki ya kasa furtawa, za'a iya fahimtarshi ta cikin ido," yace "tohhpa! Yana riqe baki yace "yanzu tohm rufe edon naka d'aya sai in karanto sunan qanen nawa a d'ayan idon,"

Wani daskararren takaici ta had'iye sannan ta nuna mishi idonta marar lafiya tace "wanna zan rufe ba? Ya 'daga mata kai, wani takaici ne ya 'kara taso mata ta, duk yanda taso riqe kukanta kasawa tayi ta juya ta gudu tabar kitchen d'in

Abdul ya 'kwala mata kira yace "ki dawo na daina, ni naa rasa inda kika samo saurin kukannan! Karfa girkinki yayi 'kauri

Via OHW📚📲

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts