New Post

Saturday, 5 November 2016

A YINI ƊAYA 9-10

[8:02pm, 21/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘:
💀 *A YINI 'DAYA* 💀

   👹💀            💀👹
                 👺

           *®NWA*
     *Na Princess Amrah*
     *Da Rabiatu sk msh*

              Page9⃣


*'Karfe 9:00pm*
*_AJIWA DAM_*

  Iya rud'ewa da kid'ima yau *AREWA STARS* sunyi ta, kuka suke su duka 19 d'in banda Kerry da tabi wayar ta, hankali tashe Feenat ta ringa kiran "Ummah! Ummah!! Ummana kizo ki taimake ni, alhakin ki ne Ummana, kullun k'ok'arin ki ganin kin bani kyakkyawar tarbiyya amma bana d'auka, ina watsi da duk tarbiyyar da kike bani, yau gashi nan muna ganin abunda muke shukawa", sosai take kuka duk ta fita hayyacin ta.

       A hankali guguwar nan ta fara isowa inda suke, k'ura ce mai had'e da wasu irin k'ananan halittu wanda bazasu iya misaltuwa ba, da yawan gaske suke ta zuwa wurin su, ga wannan kukan mai muryoyi da yawa shima yana ta k'ara yawaita, ga kuma duhu shima babu wanda ke iya ganin ko tafin hannun sa.

       Wurin Eseeee k'warin suka nufa da mamaki naga sun k'adaddabe ta baki d'aya kamar yanda zuma kema mutun idan ta kama shi. Sosai take kuwwa tana ta k'ok'arin murje su daga jikin ta amma sai k'aruwa suke, da mamaki wannan halittun suka ringa shigewa a cikin fatar Esee suna yawo ciki kamar wani bororo, har cikin kanta suka shiga suna mata yawo akai, banda soshe soshe babu abunda take,  take gashin kanta ya fara kakkaryewa yana fita har sai da baki d'ayan shi ya fita kanta ya koma swal, in banda yawon wannan halittun dake cikin kan.
     Fatar jikin ta ta fara zagwanyewa tana barin tsokar ta baki d'aya kamar wadda ta k'one, kamar gari haka fatar ta ringa murmusa a k'asa, take Esee ta fad'i wurin bata a hayyacin ta.

      Reesha da Sally kam har yanzu basu saki junan su ba, cike suke da tsoro da fargabar wannan al'amarin,
    Can suka ji wannan halittun sun dawo kan su, yanda suka ma Esee suma haka suka masu kuma har a lokacin suna manne da juna basu rabu ba hannun Reesha a cikn rigar Sally kan k'irjin ta.
    Fad'i sukayi a tare suma basa a hayyacin su.

      Da wata irin dariya da k'arfi naji wata muryar da tunda babata ta haifeni ban tab'a jin ko makamanciyar ta ba,
   Wannan k'warin ne suka hau dunk'ulewa guri d'aya, d'aya na cin d'aya har suka zama guda d'aya babbar halittar da babu halitta mai girman ta a duk doron k'asar mu ta Nigeria.
     Nan ta hau jijjigar jikin ta saboda duk inda bai gama had'ewa ba ya had'e.
    
    Idon ta ma jaa ne tamkar garwashi wanda hasken idon kawai ake iya gani a duk fad'in filin.
    
     Afnan ce b'oye a bayan wani katako wanda jikin shi duk k'usoshi ne ta lafe jikin ta sai rawa yake, da k'arfi taji an buga ta jikin k'usoshin duk suka caccake ta, take jini ya fara ambaliya daga jikin ta, tun daga nan itama ta fita hankalin ta da alama suma tayi, bata kuma sanin abunda yake wakana ba.

      Nan ma wata dariyar ta kuma yi da k'arfi wadda tafi waccan ma tsanani.

    Ruky wadda tuni ta sume tsananin tsoro da tashin hankali da k'arfi halittar nan ta d'auki Ruky ta d'aga ta sama ta nanata k'asa, take kuwa Ruky ta farfad'o, sake d'aga ta sama tayi ta jefar sai kan wani dutse, take jini ya fara ambaliya daga kanta itama ta sake sumewa.

       Dj da Mc kuwa had'a su tayi da karfi ta matse su sai ga hannun Dj ya b'ullo ta bayan Mc, hannun Mc kuma ya b'ullo ta cikin Dj, wulwula su taci gaba dayi sannan ta jefar dasu daidai kan dutsen da ta jefar da Ruky, take suma suka sume.

       Dariya mai had'e da sautin kuka ta fasa lokaci d'aya, wanda yasa sauran da bata kashe ba suka k'ara tsorata da ita, dan cikin su har da wanda ya saki zawayi daga zaune akwai, a ransu kuwa banda dana sani babu abunda sukeyi, ni kuma Amrah nace maganin irin ku kenan, wata k'ila wasu idan suka ji labarin ku koda halin su ne zasu daina, basu san aron lokaci bane Allah ya basu amma sun kasa ganewa, yau gashi sun had'u da daidai dasu, muje zuwa dai inji ni Amrah.

Amrah and Rerbee'art sk novels,
Admins
ONLINE HAUSA READERS📚
[8:14pm, 21/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘:
💀 *A YINI 'DAYA* 💀

   👹💀            💀👹
                 👺

           *®NWA*
     *Na Princess Amrah*
     *Da Rabiatu sk msh*

          Page1⃣0⃣

Bari mu koma b'angaren gidajen su.

*Karfe 10:30pm*
*~Gidan su Feenat.~*

        Ummah ce zaune tayi tagumi baki d'ayan hankalin ta a tashe yake, ita dai tasan a duk inda Feenat take ya kamata by now ta dawo gida, "to ko dai jikin maman Afnan d'in ne ya rikice?" Ta fad'a a ranta,
"To inko hakane ai ya kamata Safeena ta kira ni a waya ta sanar dani in ma acan zata kwana, amma gashi har dare yayi babu ita babu kiranta kuma",
  Wayar ta ciro nan ta hau neman lambar Feenat tana ta ringing amma bata d'aga ba, a hankali ta soma jiyo k'arar ta daga d'akin Feenat alamar can ta barta, "to kenan anan ta bar ta kome?",
  D'an guntun tsaki tayi tare da komawa ta kishingid'a ko zataji zuwan Feenat dan har a lokacim bata rufe gida ba.

     Jin shiru har sha d'aya ta kusa yasa tace "bari dai in tashi in tafi gidan su Afnan d'in sai a fad'a min asibitin da maman take, wata k'ila dai babu lafiya",
  Hijabin ta ta zira a hargitse ta rufe gidan da makulli ta fita. Da sa'a kuwa tana zuwa bakin titi ta samu napep babu kowa, bata koyi ciniki ba ta hau ta kwatanta inda zai kaita.

*Karfe 10:49pm*
*~Gidan su Afnan.~*

     Momy ce zaune ta rungume Affan dake ta bacci abin sa hankali kwance, ita kuwa tv kawai ta tsura ma ido tana kallon NTA wai a nufin ta ko za'a fad'i cewa wani jirgi yayi had'ari amma har yanzu babu, canjawa tayi ta kai AIT amma nan ma babu, tab'e bakin ta tayi tace "wata k'ila har an gwada ban gani ba, Allah dai yayi ma duk musulman cikin jirgin rasuwa, wanda suke raye kuma Allah ya basu lafiya, nayi zaune har Alhaji ya kwanta ya barni da wannan rigimammen",
    D'aukar Affan tayi ta d'ora a kafad'ar ta sannan ta kashe kallon,
   Daidai zata kashe wutar parlor'n ne yayi daidai da shigowar Umman Feenat.

     Cikn mamaki Ummah ta gaishe da momy, momy ma amsawa tayi da mamaki dan sam bata wayi Ummah ba,
   "Ina zuwa dan Allah" momy ta fad'a tare da nufar d'akin Affan ta kwantar dashi sannan ta dawo.

     Zama tayi tace "baiwar Allah lafiya dai a cikin wannan daren?",

   Ajiyar zuciya ummah ta sauke sannan tace "to ko dai ba inda nake son zuwan bane nazo? Ni inda zanje fa mai gidan bata da lafiya tana asibiti, kuma tun a waje mai gadi yace min wai me nan gidan lafiyar ta lau",

       Momy tace "Allah sarki! Gaskiya ba nan bane sai dai ko makwaftan mu, ya sunan mai gidan da kike neman?",

     "Ban san sunan su ba gaskiya, sai dai nasan sunan  'yar Afnan Abbas tana da k'ane kuma Affan, maman ta bata da lafiya ne 'yata ta tafi ganin ta, amma gashi har yanxu bata koma gida ba shine nake son jin ko lafiya?, amma babu komai nagode barin ci gaba da bincike ko Allah zaisa in dace", ta fad'i hakan ne tare da mik'ewa tsaye tana neman fita.

    Cikin mamaki Momy ke kallon Ummah, baki a sake da 'kyar ta iya furta "b..b..b..baiwar Allah ai nan ne gidan su Afnan Abbas, kuma nice mahaifiyar Afnan, sai dai kuma ni lafiya ta k'alau babu abunda ya same ni",

     Da sauri Ummah ta dawo ta zauna tana kallon momy, "kina nufin 'Yata Safeenah Al-hassan  ba nan tazo ba kenan?",
   "Gaskiya ba nan tazo ba, k'ila dai wani wurin zataje shine ta miki k'aryan zatazo gani na",
   "Hajiya dan Allah ki kira min Afnan in tambaye ta ko tana da masaniyar inda Safeenah ta tafi" ummah ta fad'a tashin hankali k'arara a fuskar ta,
     momy cike da tausayin Ummah tace "sai yanzu na gane ki ashe kece maman Feenat, kin san kolacin da muka had'u last speech and prizes given d'in su ban kalle ki sosai bane, wallahi Afnan bata nan taje gidan rasuwa ne",

     Ummah tayi salati ta rufe idon ta tana matsar hawaye, "to ina Safeenah taje? yaushe Safeenah ta koyi wannan halin? Kenan k'arya tamin? Allah yasa dai ba maza tabi ba suka sace min ita" wasu zafafan hawaye sukaci gaba da bin ta.

      Momy kuwa a ranta cewa take "kai! Allah ya shiryi yaran yanzu, k'ila ma yawon iskancin ta xata tafi shine ta ma uwarta k'aryar banda lafiya, kuma ta rasa wanda zata ce baida lafiya sai ni",

     Dady'n Afnan ne ya fito yana fad'in "maman Afnan lafiya kuwa?", yana fad'in haka yana kallon Ummah cike da mamakin yanda tazo gidan su cikin wannan daren dan shi tsoro ma ta bashi.

      Momy bata bashi amsa ba sakamakon sallamar da sukaji, maigadi ne ya shigo yana fad'in "yallab'ai wani bawan Allah ne yaxo, da ganin shi dai babban mutum ne yace wai sunan shi Alhaji Abdallah, wai baban Ihsan ne k'awar Afnan,  wai yana son ganin ka",
    Dady yace "Alhaji Abdallan da akace yayi hatsarin jirgi ya rasu!? Kace masa ya shigo".

Tir k'ashi! Kallon sis R. Nayi cike da k'aguwa da shigowar Alhaji Abdallah, muje zuwa dai sis R. Ta fad'a, sai kuma gobe zakuji posting d'in mu insha Allah.

Amrah and Rerbee'art sk novels,
Admins
ONLINE HAUSA READERS📚

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts