New Post

Wednesday, 16 November 2016

HAKA SO YAKE 29-30

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_29 -30_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

www.babymsh.blogspot.com

Kamar zaki haka yake kallonta yana huci, subeey ta lurada yanayin dayake ciki, ta d'aga mashi edo "yaya yadai, lafiya naganka haka" takarasa maganar da fara'a

Kamar gunki haka ya mata tsaye yakasaka magana,
Subeey tad'an daure fuska tana kallonsa "yaya wai lafiya ne, ko wani abu akayi maka ne"
Hakan ma shiru yamata yana kallonta, sai cen yad'aga hannunsa yanunata kamar zaiyi magana sai kuma yafasa, a hankali yake sauke hannu sannan yajuya yafita yabar d'akin, ransa a bace,

Subeey tayi kuru tana kallon kofar d'akin, a zuci take tambayar kanta "shikuwa wannan me kayi masane haka " tad'an makale kanta akafad'arta sannan tace "komema akayi masa bari dai naje naji" tana gama maganar tajanyo mayafinta tasaka sannan tafita tanufi d'akinsa,

Yana labe a bakin kofar dakinta ashe bayan yafita baije ko inaba, yana tsaye a bakin kofar d'akin yana share hawayen da suka sauko daga cikin edonsa, yana tsoron karya fita suyi kicibus da momy,

Saida yaji motsin tafiyarta tana kokarin fitowa sannan yayi saurin share hawayensa yabar kofar d'akin, gudu-gudu sauri-sauri haka yakarasa d'akin yana shiga yamayar da dakofar d'akin yarufe, dafe kansa yayi saboda wata irin juyi dayake ganin d'akin yana masa, jirine ke dibarsa sosai, da sauri yazauna gefen gado yana maida nunfashi, 5 sec sannan yadawo normal, a daidai lokacin subeey taturo kofar d'akin tashigo,

Ganinshi zaune a gafen gado yadafe kai yasa tayi saurin karasa wurinsa tana fad'an "yaya lafiya...!"  Jin muryarta a kusa dashi yasa yayi saurin d'ago kansa sukayi edo hudu, sai a lokacin Ta lura da irin yadda launin edonsa yachanza zuwa ja, sunfi kusan min biyu suna kallon juna, saicen subeey takauda edonta gefe, daga bisani kuma takara juyo ta dubesa sannan tace "yaya abdul wai meke damun kane, hankalina duk atashe yake kasa nakasa samun natsuwwa dan Allah Yaya abdul kafadamim, menene" koda takara maganar duk hawaye sun cicciko mata edo,
   Bakinsa yasoma rawa yana kokarin furta wata magana, sukaji an turo kofar d'akin anshigo,
Suduka suka mayar da dubansu wurin kofar,
Momyce tashigo tana murmushi ganin su zaune a tunaninta fira suke, amma ganin yanayin fuskar abdul yasa tayi  jugum tana kallonsu..

Via OHW📚📲

Related Posts:

  • MAKASHINKA 25-26```MAKASHINKA...```          25-26 ©Rabiatu sk msh Shamsuddeen zaune ya haɗe fuska wuri ɗaya, ranshi a ɓace yake kallon hafeez dake ta dariyarshi hankalinshi kwance … Read More
  • MAKASHINKA 27-28```MAKASHINKA...```           27-28 ©Rabiatu sk msh Zuwan yayanta ya hana shamsuddeen ya fara koya mata, duk inda zataje da yayanta take zuwa kullum suna tare, har ya gama wee… Read More
  • MAKASHINKA 19-20```MAKASHINKA...```           19-20 ©Rabiatu sk msh WANENE SHAMSUDDEEN? wani lokaci kafinnan.... Yarinyace mai kamar shekaru 18 take shigowa ɗakin, da unifoam a jikinta t… Read More
  • MAKASHINKA 23-24```MAKASHINKA...```            23-24 ©Rabiatu sk msh Ana tashi ckul, ta hangoshi yana jiranta, anma ta shareshi sai data ɓata mishi lokaci sosae, duk en makarantar a… Read More
  • MAKASHINKA 21-22```MAKASHINKA...```            21-22 ©Rabiatu sk msh _Washe gari_ Da wuri sadeey tayi shirinta natafiya makaranta domin ta san yau babu driver, Daddy ma haka tundda wuri… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts