💕💕 *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
💗💗💗💗💗
💕 *_33 - 34_* 💕
💗💗💗💗
*Na*
*_Rabee'at sk mash_*♥
```_And_```
*_Mr, smiles_*😃
Abdul dafe kansa yayi, ya koma ya jinginar da kanshi jikin gado, ko ina cikinshi kyarma yake ya ɗauki zafi kanshi kamar zai rabe biyu yakeji.
Daƙk'yar ya iya rarrafawa ya bud'e bedside drower ɗinshi ya ɗauko magani, ya zuba ruwa a cup dake kusa dashi ya ɗaga kai ya haɗiye daƙk'yar sannan ya koma ya kwanta.
Wani irin zafi yakeji a zuciyarshi, nan yafara zancen zuci "to mezaisa ya damu kanshi? Haka kawai zai sanyama kanshi ciwo ba wani dalili, "bazan taɓa sonta ba, bazan taɓa aurenta ba" ya faɗa a bayyane, wata zuciyar tace "ka fita hanyarta mana, idan kana kulata ne zaka shiga damuwa" ya gyara kwanciyarshi, tabbas zan fita harkar subeey.hakan ya ajiye aransa har bacci yazo masa,
*Bayan kwana biyu*
Soyayya sosae suke tsakaninsu subeey da Ahmad, kullum tana mak'ale da waya a kunne suna fira.
Abdul kuwa ko kaɗan ya daina nuna damuwarshi a kanta, magana ma saita kama dole take haɗasu, ita hakanma daɗi yayi mata, don yanzu duk lokacinta na Ahmad ne.
Yau tatashi cikin farin ciki, saboda murnar ziyarar da Ahmad zai kawo mata a karon farko, tunda wuri ta fara shirye shiryen zuwanshi, kafin la'asar ta gama da haɗa mishi ƙk'ayatattun girke-girke kala-kala, sannan ta shiga wanka bayan yace mata yana hanya.
Bayan tafito wanka Ta daɗe tsaye gaban kayanta tana tunanin kayan da zata saka, can ta hango wani jan material ɗinta ta tuna yanda yayi mata kyau sosae ranar data saka shi saida Abdul ya yaba ya dinga ɗaukanta hotuna.
Daukowa kawai tayi tasaka Bata tsaya wani makeup ba, powder kawai ta shafa da lipstick, tana gamawa yayi mata waya ya iso yana cikin gidan, tace tana zuwa sannan ta shiga ɗakin momie ta faɗa mata cewa ya iso, momy tace "adawo lfiya"
Nan tafisa a harabar gidan tadda shi a tsaye, bayan takarasa wurinsa tamasa iso yazo yazauna, Saida suka zauna saman fararen kujeru, sai kallonta yake ya kasa ɗauke idonshi daga kanta,
Subeey Tace "Sannu da zuwa"
Ahmed yayi murmushi Yace "Yauwah mai kyau na sameki lafiya?
A kunyace ta janyo mayafinta ta rufe fuskarta,
Ahmed yay 'yar dariya Yace "Ya kuma zaki rufemin kyakkyawan fuskar taki? Hmm Gaskiya ne subeeyta, duk yanda na daɗe ina ganin kyawunki a cikin idanuwanki kin wuce nan"
Subeey ta bud'e fuskarta tana murmushi Tace "Hhm indai kyau kakeson gani sai in samo maka mirror kazauna kana kallon kanka, nidai banson kallo"
Amhed Yace "ni kuma farin cikina kenan inrika kallon fuskarki, kuma nasan kinason farin cikinah ba?.
Ta ɗaga mishi kai tana murmushi takara sauke murya tace "bansan ta yanda zan bayyana maka irin farin cikin da nakeji ba ganina a tare dakai"
Ahmed Yace "nima da nasan ta hanyar dazan bayyana miki sonda nake miki toh da tabbas nawa sai yafi naki"
Tana murmushi tace "hhm naka dai ka sani.
Firarsu suke gwanin ban sha'awah irinna masoyan da suke matuƙkaunar junansu, suna ƙyalƙyalar dariya abunsu.
Kamar daga sama sukaji shigiwar motar Abdul, yana hangosu duk ya haɗa Rai ya juyar da fuskarshi gefe ta yadda bazasu gane ya gansuba,
Da sauri Ahmad Ya mi'ke ya tafi inda yake yana miƙa mishi hannu Yace "babban Yaya sannu da zuwa" bayan yafito daga ciki motar kallon inda yake baiyi ba ya juyar da kanshi ya shige gida.
Ahmad bai wani nuna damuwarshi ba ya dawo inda sabeey take ya zauna sukaci gaba da firarsu hankalinta duk yana kan Abdul ganin yanda ya ɓata rai da ganinta da Ahmad..
Via OHW📚
0 comments:
Post a Comment