💕💕 *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
💗💗💗💗💗
💕 *_31 - 32_* 💕
💗💗💗💗
*Na*
*_Rabee'at sk mash_*♥
```_And_```
*_Mr, smiles_*😃
Cikin takun girma da kasaita takaraso wurinsu, tayi tsaye a kansu, Sukayi shiru suna kallonta
Momy tayi murmshi tace "yanzu kuma me ake shiryawane,"
Subeey ta kirkiri murmushi sannan tace "a a momy bakomai kawaidai muna firane,"
Momy tace "wato shine ko kufito falo kuyi firar nan dani amma shine kukaki, naganeku 'yan kwanna kinnan kunfara gujemin koh, shi wannan mekayi masa ne naga fuskar tashi a d'aure" takarasa maganar tana nuna abdul da yatsa,
Subeey tajuya tadubesa daga bisani kuma tamaida dubanta wurin momy sannan tace "a a momy ba komaifa, inajin bayajin dadine, nima tambayar danake masa kenan"
Momy tace "toh shikenan nizan koma falo, sai kunfito,"
Subeey tace toh mommy"
Nan tafita tabarsu,
Bayan momy tafita subeey tasauke nunfashi sannan takara juyowa ta kalli abdul tace "yaya Abdul tunda bazaka gayamun matsalar kaba nizan koma d'akina " tana karasa maganar ta mike tsaye tana kokarin tafiya, Abdul yayi saurin riko hannunta da karfi saida ta razana, ya janyota tadawo saman gado tazauna,
A hankali abdul Ya d'ora goshinsa akan nata suna sakar nunfashin juna, cikin sanyin murya yace "meyasa kika kulashi, " cike da rashin fahimta subeey tace "waye kuma yaya Abdul"
Abdul ya lumshi edo sannan ya bud'e yasaka edonsa acikin nata sannan yace "Ahmed!!!, "
Sannu a hankali subeey ta janye goshinta akan nashi,
Tamike tsaye tana kallonsa,
Abdul ya d'ago edonsa dasukayi ja sosai ya kalleta,
Saida tagama karantar yanayinsa sanan tace "kishine koh, kishi kake akaina, hmm toh kishin meye, bayan babu sona a cikin zuciyarka, tohm meye nakishi dan na kula wani" tadan dakatar da maganarta tana jan nunfashi,
Sannan taci gaba dacewa "Meyasa na kula ahmed koh, shine tambayar dakayimun, tohm nakula ahmad ne saboda ina sonsa a yaune muka tabbatarwa da juna sona hakika, kuma ni a ganina mundace da juna, domin shi misakine nima haka, yaya Abdul katsaya iya matsayinka na yayana karka nemi katakura rayuwata niba yarinya bace masan komai daya dace dani" tana kai karshen maganar ta juya tana hawaye tafita yabar d'akin,
Abdul ya kanne edonsa sosai yakasa bud"ewa, tunda subeey tafara magana yakejin zafi da radadi a cikin zuciyarsa,
Sai bayan tafita dakusan minta biyu sannan ya bud'e edonsa, yana akallon d'akin kansa yakejin yana masa ciwo sosai, nan take jikinsa yadau zafi...
Via OHW📚📲
0 comments:
Post a Comment